Sashe 105
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
A cikin gida ma bayan su mama Debora sun turza sun turza akan Yoohan ɗin sunga babu mafita sai suka sakko dan kansu akan zasu amince da auren, sai dai da sharaɗin duk sun dawo da zama gidan papa. dolene kuma Nu'aymah ta zauna itama a gidan Yoohan bazai kaita ko ina ba.
Sai dai a mamakinsu sai sukaga Yoohan yayi murmushi tare da lumshe idanunsa ya buɗe a kansu. Sai da yay musu kallon tsaf na wasu mintuna kafin ya miƙe cike da basarwa yace, “Na amince”. A ransa kuwa dariya ya tafi yana musu, dan yasan indai nu'aymah ce sun sami dai-dai dasu.
Kusan duk a tare sukai wata irin zabura. Dan sam sun zata zaice bai yardaba su kuma su sake tada wani billin. Sai gashi sunga saɓanin tunaninsu. Kafin su gama dawowa hayyacinsu ya dawo falon ɗauke da takarda. A tebirin dake tsakkiyar falon ya ajiyeta. Ya bisu da kallo fuska a murtuke yana faɗin, “Wannan takarda ce ta agreement tsakanina da ku. Zaku cigaba da zama a gidan nan, matata ma zata zauna. Sai dai da sharaɗin duk randa na kama wani da laifin mata koda maganar banza a cikinku ko cikin yaranku sai mutum yabar gidan nan koda ace kuwa cikin su Gebrail ne. Itama kuma na muku alƙawarin bazata shiga rayuwarku ba bayan mutuntawa da girmamaku”.
Cike da wani mamakin suke kallonsa. Zasuyi magana papa yay saurin faɗin, “Wannan tsarin na John yayi dai-dai. Dan shine zai kawo mana masalaha da kwanciyar hankali a zuri'ar mu. Mukuma sake tabbatar da kowannenmu nada ƴancin aikata abinda bai saɓamana ba”.
Babu wanda ya iya sake cewa komai. Sai singing ɗin da Yoohan ya fara yi ya basu suma duk sukayi. Ɗaya ya ɗauka ya basu ɗaya. Ɗayan copy ɗin kuma da aka saka cikin frame ya nufi bangon falon daga kusurwar d/table ya kafesa jikin ginshiƙin wajen daya zama kwalliya.
Wannan abu da Yoohan ɗin yayi ya kuma girgiza su matuƙa. Gashi babu damar magana dan ya tsuke fuskar fiye da ɗazun.
Wannan takardar Agreement itace ta zama makullun rufe bakin duk wanda keda ƙarfin faɗa a ji a family ɗin su Yoohan. Sai ma zaman shirya biki sukai dan nuna bajintarsu ga gudan jininsu tamkar yanda akema kowa.
Shi dai Yoohan bai tanka kowa a cikinsu ba akan shirin bikin, ranarma yini yayi a asibiti shi da Richard. Basu dawo ba sai dare. Gajiyar da sukayi ce ta sakasu ko zaman hira basuyi ba Yoohan ya shige sashensa. yau ma tsabar wulaƙanci hana su Rich shiga yayi. da sukai magana yace shi yanzu yayi aure baya buƙatar su a sashensa. Suje can su ƙarata a sashen baƙi suyita loda kwalaben barasarsu.
Aiko sun hayayyaƙo masa tamkar zasu cinyesa. Ya fice yana murmushi bayan ya musu gwalo.
______★★★_______
*_KANO_*
A kano kam tunda garin ALLAH ya waye yau da shirye-shiryen tahowar su Nu'aymah aka tashi. Dan zasu taho abuja gidan su Abdallah. washe gari sai a miƙata ɗakin mijinta daga nan gidan. Saboda ma baba malam baya buƙatar ayi wata gayya jirgi zasu biyo.
Jin abuja zasu wuto yasa Nu'aymah fara tunanin ko dai yah Ab aka ɗaura mata aure da shi? Ko burinsu na mallakar juna ya tabbata ne? To amma idan har hakane mizaisa a ringa ɓoye mata?. Har yanzu babu wanda ya sanar mata wanene mijinta. sai dai kowa na zaunar da ita yay mata nasiha dai-dai gwargwadon saninsa. Haka ne yasa yau taci kuka harta godema UBANGIJI. Mai ƙunshi ma da Addah tasa aka kawo da ƙyar Aymah ta yarda akai mata. Hakama da za'a kaita gyaran jiki sai da baba malan ya saka baki wajen lallashinta sannan ta amince. Ai ko sai gata tayi ɗas tamkar ka saceta ga gudu. ƴar ramar da tayi saita sake ƙara fiddo mata da ƙyawunta da haskenta. Sai dai a kallo ɗaya kaɗai ya isa ka tausaya mata duk tayo laushi kamar ba Nu'aymah tsiwa ba. Duk ta zama shiru-shiru, ta kuma nanema Umm taƙi barinta sukuni.
Lokacin da aka idar da sallar la'asar Ananah tazo har sashensu tajata dan taje a kimtsata tunda jirgin 5:30pm zasu bi saita saka musu sabon rikici. Babu wanda bai lallasheta ba amma taƙi tai shiru. Sai da baba malam ya fito yay mata jan ido da nuna mata ɓacin ransa sannan. Aiko tana kuka tana sharɓar hawaye. Koda ta fito ma sai Aunty Kulu yayar Naser ce tai mata kwalliya ka ɗan dukda kuwa ba wai gidan su Yoohan ɗin zata sauka kai tsaye ba.
Tsaf ta sakata ta shirya cikin atamfa lass ƴar ubansu, ɗinkin zani da riga. Kasancewar atamfar baƙa ce da kwalliyar golden sai tai bala'in zama mata a jiki tamkar ka saceta ka gudu.
Iyayenta sun sake taruwa a kanta sun mata nasiha da gargaɗi mai faɗi akan rayuwar da zata fuskanta ta aure mai cike da ƙalubale. Dan aure ibadane. Ita kuma ibada a koda yaushe tana a cike ne da jarabawa kala-kala. Daga haka aka miƙata wajen Umm tai mata sallama. Ba Umm da Nu'aymah kawaiba, hatta duk wanda ke a wajen sai da ya matse hawayen tausayinsu. Da ƙyar aka ɓanbare Aymah jikin Umm. Hakama Muhammad dake taya yayar tasa kuka abin tausayi. Daga haka aka kaita kowane sashe tai musu sallama sannan aka shiga da ita ɗaya daga cikin motocin da zasu musu takkiya zuwa airport. Abban Abdallah da duka yaransa duk sun fito dansu daga haka zasu koma kenan sai kuma anyi hutun makaranta. Sai matan Abba Musbahu duka biyu da zasu mata rakkiya. Sai Ananah da Aunty Kulu. Aunty Aysha, Sai ƙanen Umm biyu da yayarta ɗaya. Sai Yusrah da Adawiya da taso tirjewa bazataje ba. Sai da Hajjo ta zageta tas sama da ƙasa sannan ta yarda da binsu badan taso ba. Sai Nanah, da Rufaidah autar su Naser.
Tunda motocin suka ɗauki hanyar airport Aymah ta kwantar da kanta jikin Aunty Hibbah ta cigaba da raira kukanta a hankali. Aunty Hibbah dai nata shafa bayanta cike da lallashi amma batace uffanba.
Basu wani ɓata lokaci ba a airport ɗin jirginsu ya ɗaga zuwa Abuja. Tafiyar mintuna ƙalilan kuwa ta kaisu. Anan ɗinma dai tarbarsu akazo akayi, daga gani dai daga company ɗinsu ne masu tarbar. Zuwa yanzun jikin Nu'aymah yayi zafi zau da zazzaɓi, hakan yasa suna isa Momy ta kama hanunta zuwa ɗakinta, sai da ta sakata tai sallar magriba da aketayi lokacin da suke shigowa gida, tana idarwa ta haye gado ta kwanta Momy ta lulluɓa mata bargo saboda rawar sanyin da taketa faman yi.
Ganin yanda rawar sanyin nata ke ƙaruwa Momy taje ta sanarma Abban su Abdallah dake shirin fita massallaci sallar isha'i. Biyota yay suka dawo ɗakin tare. Shima sai hankalinsa ya tashi jin yanda jikin Aymah yay masifar zafi. Ga rawar sanyin na ƙaruwa harma tana roƙon a ƙara mata wani bargon.
“Khadijah inaga bara na dawo masallaci sai a kira Yahya zaifi, dan yayi gargaɗin bata magani kai tsaye. Nasan yanzu kuma a duk inda yake yana ƙoƙarin yin sallar isha'i ne tunda kiji gashi can za'a tayar”.
“Eh gaskiya, hakan zaifi Abbansu. Bara nayi sallar nima kafin ku shigo”.
Bayan an idar da sallar isha'i Abba ya shigo gida. Kai tsaye waya ya ɗauka yay kiran Yoohan. Sai dai harta katse bai ɗaga ba. Ya sake kira nanma bai ɗaga ba. Ajiye wayar yayi yana faɗin, “Maybe baya kusa. Amma idan ya gani nasan zai kira”. Kai Momy ta jinjina masa kawai.