← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 211

Sashe 135

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

              Tabbas yau Gebrail ya sako Aymah cikin mummunan matsala. Musamman daya kasance a irin wannan lokacin ana lallaɓa lafiyar tata ne, domin aikin da Yoohan keta kaikawo wajen ganin da shine za'ai mata shi saboda haɗarinsa. Sai dai Alhmdllh, isowar Yoohan ɗin akan lokaci ya zama rahama a gareta. Duk da shima kuwa dawowar tasa bata lafiya bace ba. Ciwonsa ne na rashin barci ya dawo, yau kwanakinsa uku kenan baya iya barci, koya ɗaukesa saboda addu'a da yake yi baya gaza mintuna ashirin yake farkawa. Ganin al'amarin nasa na ƙara faɗine ya sakashi tattarowa ya taho gida. Sai gashi kuma ya iske wani tashin hankalin da shima ya nema birkita tashi ƙwalwar kan.
     Duk yanda yake tunanin bama Nu'aymah taimako da kansa anan kafin wa'adin da za'ai mata aikin ya fahimci babu mafita. Dole ya yabar ƙasar nan da ita a gobe idan ALLAH ya kaimu, dan inhar ta wuce awa saba'in da wani abu komai zai iya faruwa da ita. Shi a yanzu hakama ya rasa wane taimako zai bata. Duk wata basirarsa ta likitanci ta kufce, man kansa ya tsiyaye tas. Waya ya ɗauka ya shiga nema wata abokiyar aikinsa Dr Shukurah dake anan General hospital na Abuja. Dan itama likitace mai ƙwazo da sanin makamar aiki. Gata babbar mace kuma dan momy ma Yoohan ke kiranta ita kuma tana cemasa Son. Tun ganinta da shi na farko lokacin an turasa bautar ƙasa a asibitinsu kamanninsa da yaron ƙanwarta yaja hankalinta. Ta kuma kasa haƙuri sai da tai maganar kamannin nasu. Sai dai shi Yoohan har yanzu bai ɗauki abin da muhimmanci ba, saboda bai taɓa ganin wancan datake faɗin suna kamar ba. Amma tayi alƙawarin wataran sai ta haɗasu dan wancan duk da ba'a Najeriya yake ba.
       Duk da Dr Shikurah ta tashi da ga aiki yanda taji muryar Yoohan ɗin sai yay matuƙar tada mata da hankali. Dan haka ta nema alfarmar mijinta akan zataje. Da yake mutumne shi mai sauƙin kai sai ma yace bara ya kaita da kansa tunda darene duk da bawai can sosai ba.
        Kasancewar tasan gidan su Yoohan ɗin dama basusha wani wahalar neman address ba. Cikin mintuna ƙalilan sai gasu sun iso. Solomon ne yay mata iso cikin gidan. Har lokacin su momy na tsaye a ƙofar sashen cirko-cirko kowa da abinda ya damesa. Dan da farko basu ɗauki al'amarin da zafi ba. sai da sukaga yanda Yoohan ɗin ke a birkice ne yanata shige da fice suka sanfa aiki ne babba kenan.
       Sama-sama ya iyayma Dr Shikurah bayani akan matsalar Nu'aymah. Itama sosai hankalin nata ya tashi ta shiga faɗa akan dan miyasa za'ai gangancin sakata a duhun? Bayan kuma yana cikin abunda zai iya burkita ƙwaƙwalwar ta a lokaci ɗaya babu jinkiri. A yanzu hakanma basu da tabbacin ba'a samu matsalar da suke tsoronba. Shi dai Yoohan ma ya gaza cewa komai. Sai dai idanunsa sun sake kaɗawa jazur. Yana tsananin tausayin yarinyar nan fiye da tunani. Shiyyasa yake ta lallaɓa yanayin nata har kwanakin da zasu wuce ai mata aikin su cika. Amma dan tsabar zalunci an samu wani yazo yana neman ƙwaɓe masa aiki. Dolene wanda ya aikata wannan ya fuskanci mummunan hukunci daga garesa a gidan nan koda kuwa wanene. Amma a yanzu bashi da lokacinsu sai matarsa ta dawo hankalinta insha ALLAHU.
         Dukkan wani taimako daya dace Dr Shikurah ta bama Aymah, dan yau ko allurar nan da yake mata biyu akai mata, dama uku ce ta rage. Ta kuma tunatar dashi akan dolene kafin nan da awanni saba'in aimata aikin da ya sanar mata sun gama booking.
     Kansa kawai ya iya jinjina mata, tare da godiya akan ƙoƙarinta. Daga haka yayo mata rakkiya ta wuce.
      Sai a lokacinne yacema su Momy ya kamata suje su kwanta abinsu tunda da sauƙi. Dama a ƙage Momy take da kowa ya shige ɗin. Dan har yanzu Gebrail na ɗakinta neman hanyar da zai gudu take bukata.

           Dole ranar a ɗakin ya kwana. Dama gashi ba barci yake iya yi ba. Sai dai saɓanin baya da yake kwana cikin ƙunci da baƙin ciki yanzu ba haka baneba. Zuciyar tasa kam a ƙuntacen take, ga ciwon kai mai tsanani. sai dai kuma ya raya kaso biyu bisa uku na daren ne da nafilfili yana miƙama UBANGIJI kukansa. Sauran kaso ɗayan kam duk akan duba na'urorin da aka sakama Aymah ne lokaci-lokacin domin duba yanayin tafiyarsu, sai kuma neman hanyar da zai matso da maganar aikin da za'ai mata kafin waɗanan awannin su cika. Alhmdllh babu wata damuwa har suka wayi gari. Bayan yayi sallar asuba toilet ɗinta ya shiga yay wanka. Sannan yaje ɗakinsa yay shiri ya sake dawowa. Wayarsa ya ɗauka kamar zai kira baba malam sai kuma ya fasa bisa wani tunani da yayi.
            Dubata yayi, ya tabbatar kozata iya farkawa sai nan da wasu awa kamar huɗu. Insha ALLAH kuma zuwa sannan zai kammala usirinsa ya dawo. Hannunta ya kama a hankali ya sumbata, kafin ya shafi kumatunta yana mai mata addu'ar samun lafiya mai ɗorewa. Daga haka ya fito. A falo ya iske Uwaliya na gyarawa. Ta gaidashi da girmamawa tana tambayarsa mai jiki. A takaice ya amsa mata. Tare faɗa mata ta ajiye aikin taje ta zauna a ɗakin Nu'aymah. Ta amsa masa da to, ta ajiye kayan sharar ta nufi ɗakin shi kuma ya fita.
       Masu gidan duk suna ɗaki, ma'aikatanne kawai ke aikin gyara gidan. Papa baya nan yayi tafiya shima.
         Har Yoohan ya nufi downstairs yana amsa gaisuwar da ma'aikatan gidan ke masa sai kuma ya dawo. Ɗakin Momy ya nufa kai tsaye. Ya tsaya a bakin ƙofa yay knocking. Sai da ta bashi izinin shiga sannan ya shigo. Rikicewa tai, dan a bazata ta gansa. Duk zatonta su Victoria ne sukazo mata sallama zasu wuce school. Ta tura wayar da take amsawa ƙarƙashin filo cike da rashin gaskiya. Shi dai da yake hankalinsa ba a jikinsa yake ba yanda ya kamata baima fahimci halin da take ciki ba. Ya gaidata da girmamawa kamar yanda ya saba. Sai dai yanda ta amsa masa murya na rawa da kuma kamar a daburce ne ya bashi mamaki.
       “Mom are you ok? Hope you are well?”.
       “Y..yes yes Son. It is Okay. Mika gani?”.
        “No, dama banga Gebrail bane tunda na dawo. Where is he?”.
           Ba ƙaramin bugawa ƙirjin momy yayi ba, harda taune harshenta saboda a bazata tambayar tazo mata. Ta shiga girgiza kanta tana faɗin, “Uh...Uhm ai yayi tafiya ne?”. Tai maganar da sosa ƙeya tana wani washe haƙwara.
        “Tafiya? Where did he go?”. Yay maganar yana tsuke fuska da ƙyau.
     Sosai Madam Chioma ta ƙara rikicewa. dan gani take kamar Yoohan ɗin ya shinshino wani abune. da ƙyar ta iya control ɗin kanta tace, “Ban sani ba Yoohan. Dama inason ka dawo na zauna da kai akan lamarin Gebrail. Rashin jinsa ya fara yawa. Tunda suka shiga University ɗin nan ƙara kangarewa yakeyi”. Yanda ta ƙare maganar ne tamkar zatayi kuka ya saka Yoohan sassauta muryarsa yana sauke nannauyan numfashin ɓacin rai. Ya cije lip ɗinsa yana miƙewa daga zaman da yayi. “Babu damuwa ki barni da shi. amma Mom kema harda laifinki. Kece ke zama da yaran nan fiye da kowa. Amma miyasa idan kinga irin haka ta fara faruwa bazaki sanar min ba. Yanzu daban tambayaba maybe harna sake barin ƙasar bazaki sanar minba. Zanci ubansane. Tunta bayaji zaiko cigaba da karatu a Nageria”.
         Daga haka ya fice batare da ya sake bata damar cewa wani abuba. Itama daɗin hakan taji, dan inhar suka cigaba da zama a haka zata tonama kanta a siri, zata kuma iya aikata abinda ke ranta game da yaron nata. Dan a yanayin da yake na sanyi-sanyi yau sai ya wani tada mata tsuminta. Ji take kamar tai.....
       Ta matse idanu da ƙarfi tana faɗawa saman gadon batare data iya ƙarasa ruɗaɗɗen tunanin nata ba. Oho shi Yoohan ma baisan tanayiba. Dan har sun fice daga gidan shi da guards ɗinsa.

__________________

       Tunda Yoohan yabar gidan yaketa faman shigi da fici. Duk da azabar ciwon kai dake damunsa haka ya jure yanata kai kawo ko takan breakfast bai bi ba. Baima tunawa da yunwar duk da kuwa jiya ko buɗa bakin kirki baiyi zaman yiba tunda ya kai azumi.
       Sai wajen sha biyu saura ya kammala duk abinda ya dace. Ta office ɗin Abban Abdallah ya biya. Suka tarbi juna cike da girmamawa da surukuta. Anan ne Abba ya fahimci kamar baida lafiya. Sai dai bai tambayesa kai tsayeba sai a cikin hikima. Yoohan ɗin bai ɓoye masa ba ya sanar masa.
       Kai kawai Abba ya dinga jinjinawa. cike da damuwa yace, “Yahya anya kuwa a lamarinka babu sihiri?”. Yoohan bai fahimci abinda Abba ke nufi ba. Dan haka ya ɗago rinanun idanunsa yana kallonsa. Kai Abban ya sake jinjinawa. Cike da tabbatarwa yace, “Tabbas akwai sihiri a wannan al'amarin. Amma karka damu zanyi magana da Yaya. Insha ALLAH komai zai wuce. bara yanzu nai maka kamu sai na rubuta addu'oin nan idan kaje gida mamana ta zauna tayisu dan duk ta sani. Ka fara shansu su zama kamar ruwa a gareka”.
      Godiya Yoohan yay masa. amma sai ya sanar masa ma ai zasu wuce da Nu'aymah ne a yau da daddare dan jikinta ya motsa. Sai dai bayason baba malam ya sani da wuri har sai sun isa can dan karya tada hankalinsa.
        Cikin tsananin damuwa Abbah ke jera mata addu'oin samun lafiya. Ya ɗora da faɗin, “Duk da nasan Yaya bazai shiga ɗimuwar da kake hasashen ba na goyi bayan a ɓoye masa ɗin har sai kunje. Amma insha ALLAH muma zamu biyo bayanku ko zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu ne. ALLAH ya ƙara muku lafiya damu baki ɗaya”.
      Da amin Yoohan ya amsa masa.
Baibar Office ɗinba sai da Abba yay masa addu'oi sosai, har a cikin ruwa ya bashi ya sha sannan yay masa sallama ya wuce yana maijin ƙaunar waɗanan bayin ALLAH har cikin ƙasan zuciyarsa.

★★
Chapter 135 · 0% Book details