Sashe 53
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yoohan najin sun fita shima ya fito, dan dama a gajiye yake da tsayuwar saboda ƙafarsa wani bala'in zogi take masa. Sai da ya leƙo ya tabbatar babu kowa sannan ya fito. Bai kalli ko inda Mirror ɗinsa yake ba balle ai tunanin shafa mai ya nufi wajen kayansa kawai. Dogon wando ash mai taushi da farar t-shirt data kama jikinsa ya saka. Ya taka zuwa gaban gadon yana cije baki, zama yay yana mai kallon ƙafarsa data ɗan kumbura dai-dai idon sawu. Hannu yasa ya taɓa wajen yana yamutsa fuska, duk da zafin da yaji haka ya daure ya kama ƙafar yaja da ƙarfi. Siririyar ƙarar azaba ya saki tare da sakin ƙafar itama.
Har rige-rigen shigowa ake tsakanin papa da Mom da Richard da yazo gidan yanzu babu jimawa. Sai Solomon da Miracle dake ƙoƙarin shigowa falon suma Joy biye dasu tare da masu aiki dake ɗauke da abincin Yoohan ɗin.
Yanda sukagansa a kan gadon ya saka hankalinsu sake tashi, suka zagayesa da tambayoyin yaya akai?. Duk da surutun nasu haushi yake sake bashi sai ya tashi zaune, ganin Rich tare da su ya sakashi miƙa masa ƙafarsa. Kallon ƙafar Richard yayi da ƙyau, kafin ya jawo stool ɗin mirror ya zauna yana tambayarsa garin yaya yaji ciwon?.
Bai tanka masa ba, dan haka Rich ɗin ya kama ƙafar kawai ya hau ja masa. “Jesus!!!” ya faɗa da muryar nan tasa mai amo data haɗu da damuwa a yanzun. Saurin zama Momy tai a kusa da shi ta amshe filon daya damƙe ta maye gurbin filon. Caraf kuwa ya kama hannunta ya damƙe cikin nasa da masifar ƙarfi, dan har sai da ta saki ƙara itama.
Yanda jikinsa ke rawa zufa na fito masa sai duk tausayinsa ya sake kamasu, Miracle tai saurin zama ɗaya gefensa tare da kwanciya a jikinsa tana hawaye. Sai da Rich ya tabbatar ƙafar tayi yanda ya kamata sannan ya barsa. Sai faman jera masa sorry sukeyi.
Duk da yaji mutum kwance a jikinsa bai motsaba sai da zafin ƙafar ya daina sosai, a lokacin ƙamshin turaren Miracle dana Momy suka tabbatar masa sune nanuƙe da shi. A hankali yasa hannu ya ɗaga Miracle dake lafe a jikin nasa, kafin itama Mom da tunda ta farga da Mira take zuba mata wani kallon ƙasan ido na gargaɗi, shi dai ya zare hannunsa daga cikin nata, jan jikinsa yay baya ya haye gadon sosai batare da yace uffanba duk da sannun da suketa faman yimasa har yanzun.
Cike da kulawa Rich ya basu shawarar ya kamata su fita abar Yoohan ɗin ya huta, dan ya kula da yanda Yoohan ya sake cika tamkar zai fashe, hakan kuma yanada nasaba da zamansu a ɗakin, dan shi ɗin shaidane akan yanda Yoohan yay mugun tsanar jin kowanne kalar motsi a kusa da shi idan har yana cikin wannan yanayin.
Papa da ya gamsu da shawarar Rich ɗin sai ya tarkatasu suka fice duk da uwar gayyar Mom bataso hakanba ita. Bin bayansu Richard yay shima dan yana buƙatar ɗakko wani abun da yake son gwadawa Yoohan ɗin ko zai aminta wannan karon yasha.
Yoohan na zaune yanda suka barshi idanu a lumshe Richard ya dawo ɗauke da ƙaramin tray mai ƙyau. Duk da Yoohan na jinsa bai buɗe idanu ba balle ya motsa, Rich ya jawo ƙaramin table glass dake gaban sofa zuwa gaba gadon. Trayn dake ɗauke da kwalbar barasa da kofuna biyu, sai ƙanƙara a wani bowl ya ɗaura a kai yana kallon Yoohan ɗin. “Mr-x!”. Ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe kwalbar barasan.
Buɗe idanu Yoohan yayi a hankali batare da ya amsama Rich ɗinba. Rich ya ɗan murmusa, dan bai damu da rashin amsawarba, barasan ya zuba rabin kofi, ya ɗiba ƙanƙara ya zuba a ciki yana murmushi. Ɗagowa yay ya miƙama Yoohan dake kallonsa ta ƙasan ido kofin.
Ɗauke kai Yoohan yayi fuskarsa na nuna ƙarin ɓacin rai, dan yasan Rich ɗin yafi kowa sanin shi baya shan giya...........
“X-Man! inhar bazaka yarda na maka allurar da zata taimakeka kayi barci ba to ka daure kasha wannan, na tabbatar ita zata saka ka barcin koda na awa ɗaya ne. Kai fa likitane, kasan illar wannan matsalar da yanda take maida rayuwar mai fuskantarta a ƙarshe. Idan kana tunanin ƙin shan giya ne dan karta shiga maka rayuwar aiki yanzu ai ba'akan aikin kake ba, sannan don neman lafiyarka ne”.
Shiru kamar Yoohan bazai kulasa ba, dan har Rich ɗin ya fidda tsammanin samun kulawarma. Sai ya tsinkayi sautin tsakin Yoohan ɗin a hankali. Kallonsa Yoohan ɗin yake cikin ido da jajayen idanunsa dake a kumbure, murya a daƙile yace, “Rich! a wajenka ya kamata mutane su ƙara sanin halina akan idan nace bazanyi abuba bazan taɓa yinsa ɗinba, dan haka karka sake tunanin zansha barasa koda ba yau ba”.
Yanda yay maganar cikin kaushin murya ya saka Rich saurin cemasa “I'm very sorry”. Batare da Yoohan ɗin ya sake cewa komai ba ya maida idanunsa ya lumshe duk da yasan barcin ba ɗaukarsa zaiyi ba.
Haka suka cigaba da zama a cikin ɗakin shiru, Richard da ya sha barasar da Yoohan yaƙi sha har ya fara barci a gefen sa, shiko idanunsa biyu amma suna a lumshe. Lokaci-lokaci hawaye kan ziraro masa ta gefen ido. Yana sauraren yanda Momy da Papa keta faman zaryar leƙowa ɗakin, sai dai ɗauka suke ko Rich ɗin yaci nasara yasha giyar barci ya ɗaukesa, shiyyasa hankakinsu yaɗan kwanta suketa faman jin daɗin yanda duk shigowar da sukeyi suna samun Yoohan ɗinne a kwance.
Wajen misalin goma na dare Yoohan ya gaji da kwanciyar, tashi yay ya sauka daga gadon yana bin Rich dake barcinsa hankali kwance da kallo, bayi ya shiga ya watso ruwa. Bai jimaba ya fito sanye da bathrobe. a bakin gadon ya zauna tare da jingina da fuskar gadon. Ya kai hannu zai kashe fitilar gefen gadon idanunsa suka sauka akan farar envelope, cak ya tsaya yana kallon rubutun jiki, janyewa yay kamar zai share, sai kuma yasa hannu ya ɗauka tare da buɗewa ya zaro takardar dake a ciki.
Rubutun bashi da wani yawa sosai, amma a tsare yake gwanin sha'awa, sannan yanda aka tsara kalaman cikin rubutun da harshen turanci sunyi matuƙar jan hankalinsa har yana ɗan lumshe ido. Sai da ya maimaita takardar sau biyu sannan ya ninketa ya maida cikin envelope ɗin ya jawo drawer ya ajiyeta yana juya abinda ta ƙunsa a cikin ransa.......
________________________
*_SAUDIA_*
Duk da fushi da zuciyarsa keyi ga duk zuri'ar gidan tasu hakan bai hanashin jin ɗokin zuwan hajjo da Ahmad ba, dan baisan harda Nu'aymah a tafiyarba. shiri yay tsaf ya wuce airport domin tarbosu batare da ya saurari Adawiya da tace zata bishi ba, dan tana wanka ma ya siɗaɗe ya fice daga gidan.
Cikin sa'a kuwa yana isa airport ɗin jirginsu Nu'aymah na taɓa ƙasa. Lumshe idanu tayi tana karanto addu'oi da fatan cika alƙawarin da taima iyayenta akan kama kanta batare da wata fitina ta ɓullo ba. Hajjo na lura da duk motsinta, amma sai batace da ita komaiba har sukabi ayarin masu fita. Sanye take cikin wando blue na jeans da farar rigar fakistan da tsahonta yake har gwiwar ta, an ma rigar ado da blue ɗin duwatsu manya da ƙanana, sai farin veil da ta naɗa a kanta wanda ya sake fidda ƙuruciyarta da ƙyawun da ALLAH ya bata. Farar ƙafarta da kalar wandon ya haska tana sanye cikin blue ɗin takalmi da yay masifar mata ƙyau dan bata da babbar ƙafa sam. Sai ƙaramar jakarta itama dai blue ɗince.
Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta tai lokacin da suke ƙoƙarin sakkowa daga jirgin, ta ɗan yamutse fuska tana sauke hannun a hankali da kai dubanta can ɗan nesa dasu. Wani irin bugawa ƙirjinta yayi saboda hango Abdallah dake tsaye jikin motarsa sanye cikin ƙananun kaya da sukai masa ƙyau, ya ƙara ƙiba da ƙwarjini a idanun mai kallo kamar ba azumi ake ba. A take wata kasala ta saukar mata, tafiyarta ta sake raunana fiye da farko. Dan sai da Hajjo ta kama hannunta ta ida sauka da ita ma.
Abdallah da ya yunƙuro saboda hango Ahmad dake a gabansu da yay yaja ya tsaya cak lokacin da idanunsa suka sauka akan Nu'aymah da bai zato ko tsammaanin gani ba.. Wata irin hajijiya-hajijiya ya faraji tana neman ɗibarsa a wajen, ya kasa motsi balle ɗauke ido daga kallonta har suka ƙaraso inda yake.
Hajjo datai tamkar bataga halin da suka shiga ba ta mangare masa ƙeya tana faɗin, “Kurwata kur dan gidanku”. Firgigit yay da sauke nannauyan ajiyar zuciya, sai dai ya kasa ɗauke idanun nasa daga kan Nu'aymah da ta ɗauke kanta gefe tamkarma batasan da zamansa ba a wajen. Hannu yakai ya shafa inda Hajjo ta tallaresa kafin ya janye idanunsa da ƙyar ya maida kan hajjon data wani ƙyaɓe fusaka tana zuba masa harara.
“Yanzu dan ALLAH daga zuwanki mina miki zaki tallemin kai?”. Ya faɗa yana ɓata fuska da kallon Hajjon. Watsar dashi tai taƙi magana, saima hannun Nu'aymah data kamo suna shirin barin wajen.
Dariya Ahmad yayi, ya matsa ya rungume Abdallah, “Oh Yaya kaifa kai da Hajjo sai a slow, manta da batunta kayi tani da ƙanwarmu kawai”. Murmushi Abdallah yay tare da rungume Ahmad ɗin shima. Kafin su saki juna kowanne fuskarsa da murmushi jin daɗi. Abdallah ya sake kai dubansa ga Nu'aymah sannan ya kalli Ahmad.
Kai Ahmad ya ɗan jinjina yana murmushi, amma baice komaiba sai ƙyafta idanu da yayma Abdallahn. Ab ya kaɗa kansa kawai da nunama Ahmad hanya alamar suje to.