← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 211

Sashe 116

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

         Sosai Solomon yaji zafin abinda Aymah tayi masa, ya kuma ɗauki alwashin sai ya saita ta a layi duk da matar ogansa ce. Da wannan takaicin yaje kitchen ya amshi tatattun kayan itatuwan Yoohan ɗin a wajen Blessing data kammala haɗawa. Ta waccan ƙofar yabi ya shiga Gym ɗin. Inda ya tarar Yoohan ko rabin motsa jikinma baiyi ba. “Good Morning sir”. Ya faɗa ransa har yanzu najin zafin Aymah. “Morning?”. Yoohan ya amsa masa yana dubansa da tunanin ko baida lafiya ne. Yanzun ma cike da ɗacin murya yace, “I'm Good sir”. Komai Yoohan bai kuma ce masa ba. Ya cigaba da harkokin gabansa har ya kai lokacin da yake tsayawa. Towel Solo ya miko masa. Amsa yay yana furzar da huci ya ƙarasa kujerar zamansa ya zauna. Solomon ya karaso ya miƙa masa juice ɗin. Sannan ya ɗauka remote ya kunna television.
       Sai da Yoohan ya sha kusan rabin juice ɗin, hankalinsa nakan program ɗin yace, “Ka bama su SJ kayan dana ce?”. “Sir wane kaya? Bansan ka ajiye kaya na basu ba ai”. Da mamaki Yoohan ya juyo ya ɗan kallesa, sai kuma ya maida ga television ɗin yana faɗin, “Baka gyara min ɗaki ba kenan?”.
        A take abinda Aymah tai masa ya dawo masa a rai. Murya a cinkushe yace, “Sir naje zan gyara Madam ta hanani. ta kuma min gargaɗin ma karna sake shiga sashen gaba ɗaya”.
      “Madam? Wace madam?”.
Yoohan yay maganar da tsatstsare sa da idanu. Kan solo a ƙasa yace, “Madam Nu'aymah”. A take ya zayyane masa duk yanda sukayi da Aymah kafin yazo nan wajensa. Ya zata zaiga ɓacin rai tattare da ogan nashi, dan ya saka aiki aƙi masa ko wani ya hana a masa yana ɗaya daga cikin abinda ya tsana, ko madam Chioma ce sai ya nuna ɓacin ransa koda ba zaiyi magana ba. Amma a mamakin Solo sai yaga Yoohan ɗin yayi wani ɗan munafukin murmushi yana ajiye kofin hannunsa. Batare da yace komaiba ya shiga zare takalman ƙafarsa. Yana kammalawa kuma ya miƙe ya fito solo na binsa da kallon tsoro dan ya wuce na mamaki kam.

          Har yanzu Aymah na a falon, dan tsabar ƙwarewa a ƙwaɗayin da take cema wani yana yi ita kofi ma ta ɗakko ta haɗa madara da zuma da yawa, tasa ruwa ɗan kaɗan. Ta kwaso biscuits kala-kala kusan shida tazo ta zube a dining tana faman ci da lumshe idanu. Dan babu ƙarya biscuits ɗin duk sunyi uwar haɗuwa.
     Cak Yoohan dake ƙoƙarin fitowa ya tsaya kawai yana kallonta da maɗaukakin mamaki da al'ajab. Yayi tsayuwar kusan mintuna uku yana kallonta da ita da falon da ƙamshinsa ke neman saukar masa da kasala kafin ya cigaba da takowa a hankali ya iso inda take. Kamar zaiyi magana sai kuma ya wuce a binsa zuciyarsa fal mamakinta. Ya tabbatar ta gansa amma ta basar.
       Tunda ya tura ƙofar ɗakinsa yaga yanda ya barsa haka yake sai ya juyo bai shiga ba. Wajen Aymah dake cigaba da party ɗinta ya dawo. Yanzun kam a bisa tsautsayi ta ɗago kanta, dan batai tunanin shine ya dawoba duk da taji ƙamshinsa sai suka haɗa ido. Saurin kauda nata tayi tana tura biscuit cikin baki.
       Shikam yana tsaye hanayensa duka cikin aljihun wandonsa, cikin ƙasa da murya sosai, kamar baya son yin maganar yace, “Hy Smally, tuda kin korarmin maimin aiki sai ki je ki min dan bana iya wanka a toilet ba'a wanke ba”.
         Kamar Aymah zata sharesa sai kuma ta kasa, dan yanda yay maganar ƙasa-ƙasa da kiranta sumoli yaja hankalinta wajen son maida masa murtani. Sai dai kuma tana ɗagowa ta sami fuskarsa a tsuke mayun idanunsa kuma ƙyam a kanta kamar zasu haɗiyeta. Kumbura baki tayi da faɗin, “Wlhy niba smally bace, dan ko a yanzu dai shekarata goma sha bakwai da wata tara”.
        A ransa yace, ‘Ai fa sai sha bakwai ɗin’.
      Ta cigaba da faɗin, “Kuma da kake cewa na korar maka mai aiki, ta yaya zanbar wannan ƙaton gardin yana tsayamin a kai kamar wani mala'ikin dake tsaron ƙofar wuta. Baga ƙannenka nan ba wani yazo ya gyara maka”.
         Harga ALLAH maganarta ta bashi dariya, amma sai ya danne. Takawa yay gab da ita. Hakan yasa ta miƙe zumbur tana ajiye ledar biscuit ɗin hannunta, ta tura kujerar baya danta samu hanyar guduwa. Caraf ya riƙo hannunta ta faɗo jikinsa. Duk da yaji ɗan zafin yanda ta faɗo masa bai damuba. Sai ma hannunsa daya ɗora akan ƙugunta ya sake matsota ta manne masa sosai.
        “Ouch!! Wannan muguntar fa?”. Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗago fuskarta dake saman ƙirjinsa gab da haɓarsa, dan har ɗan gashin gemunsa na gogar gashin kanta. Kallon ido cikin ido sukaima juna. Tana ƙoƙarin son kauda nata amma ya hana, da wani irin yanayi yace, “Miyasa ke bakinki baya iya daina magana? Kowacce amsa kinada ita?”.
          “To sai in zauna a ringa cutata, ku mutane ai kunason mutum ya zama banza ku dinga takashi kamar wani tiles kuna wucewa”.
        Shi sam bama ya fahimtar mi take faɗa, hankalinsa gaba ɗaya yana kan bakinta ne da idanunta da suka ciko da ƙwalla. Hakan yasa baice mata komaiba, sai saukar babban ɗan yatsansa taji akan gefen bakinta. Saurin kauda fuskarta tai ƙoƙarin yi tana zaro ido. yayinda shi kuma ya ɗaga mata yatsan yana nuna mata ɓurɓushin biscuit daya goge mata. Haɗiye abinda zata faɗa ɗin tayi da ƙoƙarin san zamewa daga jikin nasa. Babu musu ya saketa kuwa.
     Daɓar ta faɗa saman kujerar da take zaune da. “Wayyo Abbana!”. Ta faɗa saboda zafi da taji.
      Dafe tebirin yayi da hannu biyu ya ranƙwafo kanta har tanajin saukar numfashinsa. Cikin kunnenta yace, “Silly girl, wannan shine maganin masu bakin magana kamar akku”.
         Hawaye na silalo mata akan fuska ta sa hannu kan damtsen hannunsa ta turesa. Fuskarsa ɗauke da murmushin mugunta ya riƙe hannunta, “Tashi muje ki gyaramin ɗaki kona sake ɗagaki sama na dire a kujerarnan har sai........ ” Sai kuma yay shiru bai ƙarasa ba
          Zatai magana ya ɗora yatsansa saman bakinta yace, “Shiiii!!!!”. Sai kuma yaja hannunta dake cikin nasa ya miƙar da ita. Tanaji tana gani ya jata har ɗakinsa. Ganin ya nufi hanyar da take ƙyautata zaton toilet ne ta tirje da faɗin, “Nifa bana shiga toilet babu ɗan kwali”.
       Baice komaiba, sai sakin hannunta da yay ya nufi Wadrobe ɗinsa, sai gashi riƙe da babban handkerchief. Gani tai kawai ya warwaresa yay masa linkin ɗankwali ya ɗora mata bisa kai. Tsaf ya ɗaura mata shi kuwa duk da bawai ya buɗe bane da ƙyau yanda ya kamata, amma dai ya rufe gashin. Sake kama hannun nata yay zuwa cikin toilet ɗin.
      “Ki fara wanke nan, wanka zanyi na fita”. Daga haka ya saketa ya fita.
       Dubansa tayi kamar zatai magana sai kuma tai shiru dan harya gama ficewa. Tsaf ta gama bin toilet ɗin da kallo, dan babu ƙarya ya haɗu, gashi an zuba kayan toilet ɗin irin kalar, garai-garai ɗin nan kamar ƙanƙara, sai dai sunfi ƙanƙara duhu dan sunyi ɗan kalar ash da fari-fari. Komai tsaf a tsare inda ake buƙatar ganinsa babu wani dattin da yake faɗa akansa bazai iya wankan ba. Da yake neman aikin yin take saboda jikinta da yay mata nauyi sai gashi ƙara gyarashi tsaf, kamar taje ta ɗakko turaren toilet ɗin da miss xoxo ta haɗa mata mai shegen ƙamshi na wanke toilet sai kuma ta fasa. A cewarta kada ta cika zaƙewa ya ɗauka ya sameta ne a ɓagas.
      Fitowa tai riƙe da ƙugu alamar ta gaji, Yoohan dake zaune a kujerar dake tebirin karatunsa ya ɗago yana kallonta jin tana nishi. Dan shi a zatosa ko faɗuwa tayi a toilet ɗin ma. “lafiya?”.
         Baki ta kumbura gaba da faɗin, “Na gaji ne, bayana kamar zai ɓalle”.
     “Kaɗanma kenan, tunda kika koramin mai mini ai”. Ya faɗa yana ɗauke kansa daga gareta ya maida ga lap-top ɗin gabansa da yake aiki a ciki. Haushin maganar tasa ya hanata tanka masa, ta ƙarasa ga makeken gadonsa ta faɗa a kai tana faɗin, “Wash Umm na gaji, nima bara na rama hawar min gado da kayi”.
      Miƙewa yay idonsa a kanta. Batare da yace mata komaiba ya nufi bayi yana wani murmushin daya zo masa babu shiri. Harga ALLAH ta burgesa da tai aikin, dan baiyi zaton zatayin ba saboda sanin tsiwarta. Iyawarma baiyi zaton ta iya ba. Amma daya shiga bayin sai yagama gyaran natama yamafi na Solomon ɗin.
        Sai da taja kusan mintuna uku a kwance tana shaƙar ƙamshinsa daya manne bedsheet ɗin, kafin ta miƙe ta fara gyarawa duk da harga ALLAH ta gaji da gaske. Amma batason ya fito ya isketa. Kuma tanama buƙatar zuwa tayi wanka itama dan cikinta dam yake da ciye-ciyen da tayi.
Chapter 116 · 0% Book details