Sashe 100
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tsaf Nu'aymah tai shiri da kayan da Umm ta kawo mata ɗakin baba malam ɗin. Lass ne ɗan ubansu sky blue da akaima ɗinkin riga da zani. Ya zauna mata ɗas a jiki tare da haskaka farar fatarta daketa ƙyalli. Ƴar ramar da tayi sai ta sake fiddo ainahin dogon hancinta da manyan idanunta masu matuƙar haske da cikar gashi. Turaren baba malam dana Umm dake a bedroom ɗin babu wanda bata fesa ba. Hakan yasa take zuba uban ƙamshi tamkar tayi wanka da turare. Gashi cakuɗasun da tayi sai ya bada wani irin shu'umin ƙamshi mai narkar da zuciyar mai shaƙa. Ɗan kwalin ta ɗaura bisa gyararren gashinta da hajjo ta matsa jiya Yah Omar ya kaita wajen wankewa tare da su Amal. Ta saka sarƙa da sauran kayan adon sannan ta ɗauki blue gyalen da aka haɗo mata da shi ta ɗora a kafaɗarta. ta zira flat shoes ɗinta suma blue. Tayi ƙyau sosai tamkar ka saceta ka gudu. Kamar yanda Umm ta gargaɗeta akan idan ta shirya ta fito ta gaisa da baƙi batayi musu ba ta nufi sashen Umm ɗin bayan ta kulle falon baba malam ta taho da key ɗin a hannunta.
Tunda ta fito jama'ar dake zazzaune a falon Umm keta ambatar masha ALLAH. Ita dai cikin ɗan jin nauyin wasu daga cikinsu ta shiga risinawa tana gaishesu. Masu tsokanarta kuwa ta kasa maida murtani. Saɓanin da da kowa yasan Nu'aymah bata barin saita kwana ga abokin wasa. da kace kule take cewa cas. Amma yau sai ga bakin ya mutu murus sai ɗan sassanyan murmushi kawai take musu a taƙaice.
Har bedroom ɗin Umm ta shiga inda ƙanen Umm da yayunta ke cike da shi. Nanma gaidasu ta shigayi. Sukam sunata amsawa cike da ƙaunar ɗiyar ƴar uwar tasu. Aunty Hibba dake cin abinci ta jawo hanunta ta zaunar kusa da ita tana faɗin, “Zauna kici abinci. Ni wannan ramar taki sam banason ganinta dota”. A ɗan shagwaɓe Nu'aymah tace, “ALLAH na ƙoshi Umma, munyi breakfast tare da Abba, kuma naci sosai ki tambayi Umm ma kiji”.
“Eh breakfast ai tun ɗazunne, kusan awa uku kenan, wannan abincin rana ne. Ke dama nasani da masifar son masa”. Duk yanda Nu'aymah taso zamewa sai da Aunty Hibba ta dinga bata masar a baki tare da naman. Sai gashi kuwa taɗanci babu laifi ta kuma shanye ƙaramar roban zoɓo data ɗauka.
★★★★
A ɓangaren su baba malam kuwa duk sun ɗunguma massallacin juma'a inda za'a gudanar da ɗaurin aure bayan sallar juma'a insha ALLAHU.
Massallacin ya cika danƙam da manyan mutane daga kowacce kusurwa ta Najeriya harma da wasu ƙasashen ƙetare. Tun daga kan malamai, ƴan kasuwa, harma da masu mulki. Sai abokan arzuƙa da ƴan uwa na kusa dana nesa. gayyar anguna dana jama'ar gari da girma da kimar su baba malam ɗince ta tarasu a wajen.
Bayan kammala sallar juma'a akai ɗaure-ɗauren aure ciki harda na ƴaƴan su baba mala su Aunty Kubrah. Ana kammalawa manyan baƙi suka ɗunguma babban hall ɗin da aka kama domin gudanar da ƙwarya-ƙwaryar walimar cin abinci.
Walimar ce ta jasu har sai bayan la'asar sannan suka koma gida da wasu tawagar baƙin da ba'a ranar zasu wuce gida ba.
Zuwa yanzun kam gidan su Nu'aymah ya sake cika danƙam da mata, dan yau ne Addah ke nata yinin bikin. Hayaniya akeyi sosai babu maijin wani. Dan tun bayan ɗaurin aure su Omar sukaje gidan da labarin yanda komai ya kama.
Nu'aymah na tsakkiyar dangin Umm har yanzu. Sun sakata a tsakkiya anata hirar zuminci cike da farin ciki. Wata Gwaggon su Umm ce, data kasance kaka ga Nu'aymah ta shigo ɗakin tana guɗa. Da mamaki duk suke kallonta har suna rige-rigen faɗin, “Gwaggo an ɗaura ne?”.
“Ƙwarai da gaske an ɗaura. Yanzun ma haka ƴan ɗaurin aure sun dawo, kuma harda sabon albishir na ƙarin amarya”.
Aunty Fareeda tace, “Ƙarin amarya kuma Gwaggo? A cikin yaran gidan dai?”.
“Ƴarku ma kuwa” ta sake basu amsa tana cillara wata sabuwar guɗar. Kafin su gama fita daga ruɗani su Nanah suka shigo suna ƙwala kiran “Nu'aymah amarya”.
Dakatar dasu Aunty Hibba tayi. “Kai mufa kuna sake ɓatar damu, Gwaggo wai mike faruwa?”.
Da sauri “Raudah tace, “Momy baku san Nu'aymah ma an ɗaura mata aure ba yanzu tare da su Aunty Hajarah. Yanzun ƴan ɗaurin aure da suka dawo suke faɗa ai”.
A take ɗakin ha harmutse da murna da taraddadin wanene angon? Miyasa kuma aka ɓoye musu, dan su dai basusan da auren ɗiyar ƴar uwar tasu za'ayi ba. Duk sunzone yima Addah baici kasancewar zumincine mai ƙarfi da kowa ya sani a tsakanin Umm da ita.
Tunda aka fara wanan kace nace Nu'aymah ta ɗora hanunta saman kai ta riƙe. Cusashi tai a tsakanin cinyoyinta jikinta na wani irin tsuma. Ga kanta ya fara sara mata sama-sama. Duk yanda taso ta daure ta kasa. Dan haka cikin ƙarfin hali ta shiga laluben wanda ke a kusa da ita. Cikin sa'a ta damƙo hanun Aunty Magajiya yayar Umm. Hankali tashe Aunty Magajiya ta dubeta, sai kuma yanda taga jikin Nu'aymahr na karkarwane ya sakata ambaton ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ da ƙarfi.
Kusan mafi yawan ƴan ɗakin sai hankalinsu ya dawo wajen. A take kuma sai duk sukai tsitt tare da zabura kan Nu'aymah......
Gwaggo Ramma ce ta hana ɗaga maganar mawuyacin halin da Nu'aymah ke a ciki a gidan har lokacin da su baba malam suka dawo. Dan Umm ma bata fasa kai da kawowar da takeyi tsakanin sashen Addah da sashentaba saboda son ganin baƙi kowa ya samu abinci. Yin komai takeyi cike da ƙarfin hali. Sai ta fakaici idon mutane take share hawayen dake cika mata idanu. Duk da kuwa ita tasan da maganar auren. Kuma tana cikin masu goyen bayan ɗaurashi a yau ɗin saboda wasu dalilainsu ita da baba malam da hajjo.
Key da baba malam bai gani bane a inda suke ajiyewa ya sakashi kiran wayarta. Cikin sa'a kuwa wayar tana a tare da ita. Dan haka ta ɗaga ya sanar mata gashi ya shigo amma baiga key ba. Ta kira masa Nu'aymah ko ta canja masa waje.
“To” kawai tace masa ta yanke wayar.
Ɗakinta ta fara shiga inda danginta ke zaune jigum-jigum da Nu'aymah shimfiɗe bisa gado tana fidda wahalallen numfashi tamkar mai Asthma. Aunty Juwairiyya sai shafa mata ruwa take a fuska wasu kuma na tofa mata addu'oi. Wani Key ɗin ta ɗauka a drawer ta fita batare da tace musu komaiba ta fice.
A kallo ɗaya baba malam ya fahimci akwai matsala. Tunkanma ta buɗe ya shiga jero mata tambayoyi akan mike damunta?. Sai da ta buɗe ƙofar suka shiga sannan tai masa bayani. Shima hankalinsa ne ya tashi, dan haka yace taje su maido Aymah sashensa, karsu bari kowa kuma ya fahimci halin da ake ciki. Bara ya kira Doctor.