Sashe 71
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sai ya durƙusa a ƙasa yay sujida hawaye na sauka masa a fuska.
Yoohan dake binsa da kallo yay saurin duƙawa shima yana zaro manyan idanunsa a waje. durƙushewa yay gwiwa bibbiyu yana kallon malam harya ɗago daga sujidar da yay.
Fuskarsa ɗauke da murmushi ya kama Yoohan suka miƙe tare, sai kawai ya jawosa jikinsa ya rungume.
Duk da ba yaune karan farko da aka fara yima Yoohan irin wannan rungumar ba sai yaji ta yau ɗin kamar daban ce a rayuwarsa. Kamar ba irin wadda Papa da sauran mutane ke masa bace. Kamar girman ta yau ɗin na musamman ne.
Baba malam ya ɗagosa da sauri tare da riƙe hannunsa. Yace, “Lallai yau zaka fara sani da ga rahamar UBANGIJINA, domin kuwa, *HASKE da RAHAMAR UBANGIJIN* al'arshi ta bayyana a zuciyarka da harshenka Yahya!. Sai dai bazaka taɓa fahimtar tarin ni'imomin dake cikin musilinci ba daga wajensa har sai ka shigo cikinsa”.
Yoohan da bai fahimcesa ba yay shiru yana kallonsa ƙasa-ƙasa. Sai kusan seconds goma ya ɗago kaɗan ya kalli baba malam ɗin da ƙyau, sai kuma ya sake maida kansa ƙasa. “Uncle ban gane mikake nufi ba”.
Murmushi baba malam yayi, ya sake gyara tsaiwarsa cikin harshen turancin da suke magana yace, “Ina nufin bazaka taɓa fahimtar ni'imomin dake tattare da wannan addini mai daraja ba har sai ka kasance musulmi Yoohan. Ta wannan hanyar ne kawai zaka ƙwanƙwaɗi madarar ni'imar UBANGIJI fiye da zaton hasashen ka”.
Babu ko tantama Yoohan yace, “Inhar zan sani ɗin ta wannan hanyar zan biya ko nawane na shiga addinin naku dan na sani, dan na tabbatar idan ban sani ɗinba natsuwa zata cigaba da yin nisa da ni har abada”.
“UBANGIJI kai ne gagara misali a tunanin hankali ko hasashen zuciya. Tabbas kai mai ikone ga wanda kaso, a kuma lokacin da kaso. Yahya shiga addinin musilinci ba'a biyan ko sisi. *_ALLAH maɗaukakin sarki ya halicci halitta ne domin su bauta masa, kuma ya sawwake musu abinda zai taimaka
musu na arzikinsa, ALLAH maɗaukakin sarki yana cewa:_*
_“Kuma ban halicci aljan da mutum ba sai domin kawai su bauta mini. Bana neman wani arziki daga gare su kuma bana bukatar da su ciyar da ni. Lalle ALLAH shi ne kaɗai mai azurtawa kuma ma’abocin karfi sosai”._ Suratuz Zariyat, aya ta:56-58.
*_Mutum a halittar da ALLAH ya yi masa zai bautawa ALLAH ne shi kaɗai inda za’a bar shi, ya zama mai son ALLAH ya na bauta masa ba ya yi ma sa shirka, sadai abinda ya
ɓata wannan (dabi’ar) kuma yake karkatar da ita shi ne abin sheɗanun aljanu da na mutane su ke ƙawata mata na abinda sashin su yake yi wa sashi wahayi na ƙawatacciyar Magana kawai don ruɗi, shirka wata aba ce da ta zo daga baya kuma ta kutsa kai ga halittar da ALLAH
ya yi wa mutum, ALLAH maɗaukakin sarki yana cewa:_*
_“To, ka tsayar da fuskarka ga wannan addini kana mai kaucewa shirka, halittar ALLAH wacce ya halicci mutane a kan ta, babu mai canza halittar ALLAH”._ Suratur Rum, aya ta: 30.
*Kuma Ma’aikin ALLAH (S.W.A) ya ce: “Dukkan abin haihuwa ana haihuwarsa ne akan musulunci, to iyayan shi ne su ke yahudantar da shi, ko su Nasarantar da shi (kiristan da shi) ko su majusantar da shi”. Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito.*
Dan haka Yahya UBANGIJI baya buƙatar ko sisi da ga gareka face amsa kalmar *_La'ilaha illallah......._*”.
Sosai abin ya bama Yoohan mamaki da wannan bayani na baba malam. dan haka ya gyaɗa kansa yana mai gyara tsaywarsa da faɗin, “Na shirya amsar wannan kalma Uncle”.
Murmushi sosai ya sake faɗaɗa a fuskar baba malam, batare da ya sake cewa komai ba ya kama hannun Yoohan sukabi ta ƙaramar ƙofa zuwa cikin gida. Abban su Abdallah na biye da su zuciyarsa fal tunanin inda ya taɓa sanin mai kama da Yoohan ɗin a wasu shekarun baya..
Sashen mahaifinsu kai tsaye suka nufa, ko ina fes yake dan ana gyarawa saboda sukan zauna a ciki musamman randa sukaso nishaɗi. Duk hidimar bikin salla ma jiya a ciki sukayita su huɗun. Sai da duk suka zauna, Yoohan da Abban Abdallah kowa nama ɗan uwansa kallon sani baba malam ya katsesu da faɗin.
*_“Shaidawa Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai ALLAH, Kuma Muhammadu MANZON ALLAH ne”_*.
_“Waannan kalmomin shahada guda biyu, sune ƙofar shiga musulunci, sune kuma rukuninsa mafi girma, kuma ba a yin hukunci da musulusncin mutum, sai da furuci da su, da kuma aiki da abin da suka ƙunsa, da wannan ne kuma kafiri yake zama musulmi._
1-Ma’anar kalmar shahada: Ma’anar shaidawa da cewa babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH, shi ne yin furuci da ita tare da sanin ma’anarta, da kuma yin aiki da abin da ta ƙunsa, zahiri da baɗini, malamai sun haɗu akan cewa furuci da kalmar shahada, ba tare da sanin ma’anarta ko yin aiki da abin da ta ƙunsa ba, ba shi da amfani, kai sai dai ma ta zama hujja a kansa, kuma ma’anar (La Ilaha Illallah) shi ne babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH shi kaɗai matsarkaki maɗaukaki.
_Rukunan wannan kalmar (shahada) sune: (korewa da tabbatarwa), wato kore haƙƙin bauta daga wanin ALLAH, kuma tabbatar da shi ga ALLAH shi kaɗai ba shi da abokin tarayya. Haka kuma wannan kalmar ta ƙunshi kafircewa ɗagutu (shi ne dukkannin abin da ake bauta masa wanda ba ALLAH Maɗaukaki ba, ko da kuwa ya kasance mutum ne (tare da yardarsa da bautar da ake masa), ko dutse, ko bishiya, ko son zuciya, ko sha’awa), da nuna masa ƙiyayya da yin kuɓuta daga gare shi._
*_Wanda ya faɗi wannan kalmar (shahada da bakinsa) amma bai kafircewa abubuwan da ake bauta
musu wanin ALLAH ba (a aikace), to tamkar bai faɗeta ba. ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Kuma abin bautarku abin bauta ne guda ɗaya.
Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Mai rahama Mai jin ƙai”.(Baƙara: 163)._*
*_Kuma Maɗaukaki ya ce: “Babu tilastawa game da (shiga) addinin
(musulunci), haƙiƙa shiriya ta bayyana daga ɓata, saboda haka wanda ya kafirce wa ɗagutu kuma ya yi imani da ALLAH, to haƙiƙa ya riƙi igiya amintacciya, (wadda) ba ta yankewa. ALLAH kuwa Mai ji ne, Masanine”._* (Baƙara: 256)
_Kuma kalmar (Ilah) tana nufin abin bautawa da gaskiya, duk wanda ya ƙudurci cewa abin da ake nufi
da kalmar (Ilah) shi ne: Mai halitta, Mai arzutawa, ko wanda yake da ikon ƙirƙira, kuma ya ƙudurci cewa yin
imani da wannan kawai zai wadatar, ba tare da kaɗaita ALLAH da ibada ba, to haƙika faɗin kalmar (La Ilaha
Illallahu) ba za ta amfane shi ba, a nan duniya wajen shiga Musulunci, kuma a Lahira ba zata kubutar da shi ba daga azaba madawwamiya._
ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Ka ce (da su): “Wane ne yake arzuta ku daga sama da ƙasa? ko kuma wane ne yake mallakar ji da gani?, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wanene kuma yake tsara al’amura?” To za su ce: “ALLAH ne”. To ka ce (da su): yanzu ba za ku ji tsoronsa ba?”
(Yunus: 31).
*_ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Ko wane ne ya halicci sammai da ƙassai, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan (da wannan ruwan) muka tsirar da (shukokin) gonaki
masu ƙayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba?, shin akwai wani abin bautawa tare da ALLAH, A’a, su dai mutane ne da suke kauce wa (gaskiya)”. (Naml: 60)._*
Kuma ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Kuma lallai idan ka tambayesu, “Wanene ya halicce su?, Lallai za su ce: “ALLAH ne” To, yaya ake juyar da su (daga bauta wa ALLAH)?” (Zukhruf: 87).