Sashe 192
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abban Abdallah da keji kamar ya tashi ya ƙarasa rayuwarta saboda zuciya data kumesa ya yunƙura zaiyi magana Hajjo ta dakatar da shi ta shanyar ɗaga masa hannu. Dole kuwa ya koma ya zauna yana zare idanu. Tai gyaran murya sannan ta gyara ƙafarta mai ciwo da dubansu ɗaya bayan ɗaya ta fara faɗin, “Karma ka wahal da kanka wajen ƙaryata abinda duk Fauza ta faɗa Lurwanu. Idan bakai tunanin ana kallonku ba yau zan sanar maka cewar na jima da fahimtar kai da ita su wanene a cikinmu. Na barkune saboda na muku talalar zuwan wannan ranar. Na jima ina zargin akwai wani abu a zuciyar Lurwanu game da ɗan uwansa, dan yasha kawomin sukarsa akan miyasa kaza da kaza dole sai da umarnin ɗan malam akeyi a gidan nan?, sai dai ina nuna masa ɓacin rai. Amma ban sake tabbatarwa ba sai bayan tsaida ranar auren Abdullahi da Zainabu. Da kunnena naji dukkan abinda kuka tattauna akan soyayyar da Adawiya kema Abdullahi, tare da shirinku na bayan mutuwar Zainabu zai aureta. Hankalina ya tashi, dan zan iya cewa wannan shi e sanadin girmama samuwar hawan jini na ma. Na riƙe komai a raina na kasa faɗa har ƴar uwata tazo diba ni (Ananah) banso faɗa mataba. amma na fahimci dolene na samu shawara daga wani kafin lokaci ya ƙure. Dan wannan abune mai matuƙar sarƙaƙiya. haka na samu lokaci a wani dare mukai maganar. Itama hankalinta yayi ƙololuwar tashi dajin wnanan zance. Itace ta kawo shawarar ai tunda SARAN ƁOYE kukeyi muma yakamata mubi ta ZAGON ƘASA mu kamaku a hannu dumu-dumu. Itace ta kawo shawarar sace Zainabu ranar daren aurenta, dan hakanne kawai zai wargaza auren cikin sauƙi. A cikin shirinmu Ameer ya shigo rayuwar Zainabu matsayin abokin Abdullahi. Ameer kuwa abokin Naser ne, dan Naser shine mukaba aikin a hannunsa. Nice da kaina na shiga na haɗo kayan Zainabu a ɗakinta, na kuma jajjefa wasu ta taga. Ina cikin yi Yusrah ta shigo ɗakin da alama banɗaki zata shiga. Na tabbatar taga mutum, sai dai ban saniba kota gane waye ko bata ganeba. Abdullahi yaso lalata mana shiri a ranar saboda jan ra'ayin Zainabu da yay tayi akan suyi hira. Sai dai kuma ta dalilin Adawiya hirar batai tsaho ba. Naser ya samu damar ɗauke Zainabu ya kaita wani gida. Bamu dawo da itaba sai bayan sati biyu. Daga haka muka cigaba da bibiyar duk wani taku naku. Hatta da sace Number likitan da zaima Zainabu aiki naji a raina wani a cikinkune ya saceta, sai dai banida hujja shiyyasa nai shiru. Ina kan sani na amince da aurama Abdallah Adawiya saboda ɗana tarkon farko a gareku, inason kuma tabbatar da hannun Abdallah akan shirinku, kokuwa kuna amfani da shi ne kawai batare dashi kansa ya sani ba?. Na kuma hana Yusrah tarewa dan dama bazan yarda ta tare ɗinba. Tafiya da Zainabu Umrah yanada nasaba da son sake tabbatar da komai. Na kuma tabbatar ɗin. Waya da aka ɗagama Khadijah na hana Abdullahi zuwa Nigeria duk a cikin shirinmu ne. Munsa Nasiru ya dawo rayuwar Zainabu ne daman dan ya sake wargaza magar auren da Abdallah keta naci da son sake ganin ya ƙullu tsakaninsa da ita. Da kuma sanin da nai duk cikin shirinkune”.. “Maman Aaida data zama ƙawar Adawiya a saudia duk a cikin shirinmune itama. Mune muka sakata samun kusanci da Adawiya da ɗorata mataki-matakin kasancewa da Abdallah, a tunaninmu ko zaku dawo hayyacinku ku yarda da ƙaddara. Amma sai kuka sake tura kanku a cikin ramuka. A tarayyar maman Aaida da Adawiya ne ya bamu damar sake fahimtar bada sanin Abdallah kuke wani abunba. Dan ba komai kuke sanar masa akan shirinku ba, sannan lallai da gaske yana son Zainabu duk da ya raba hankalinsa biyu akan soyayyarta da dukiyar mahaifinta da kuka ƙwaɗaita masa a rai. Ta kuma hakane muka fahimci banzar sana'a da Abdallah yake ƙoƙarin jefa kansa a ciki. Amma Alhmdllh munyi ƙoƙarin maidosa hanya ta dalilin mijin maman Aaida ɗin, wanda ta hannunsa mukejin duk wani motsin Abdallah a yanzu haka. Maganar cikin Zainabu shine ya hautsina min tunani, saboda batare kukai aikinba yasa ban fahimci komaiba a ciki ba, duk da ina zargin kuɗinne duk da haka. Koda na tabbatar Zainabu takai mutuncinta gidan aure wannan ruɗanin na maganar ciki bai barniba sai yanzu da Fauza ta warware komai akan samuwar ciki da fitarsa. Na kai Uwaliya aiki Abuja ne dama dan Lurwanu yay yunƙurin yin amfani da ita kamar yanda Nasiru ya gano mana hanyar da sukebi wajen aamfani da Rabi itama. Na tabbatar alwashin da yahya ya ɗauka akan gano ko wanene bazai tashi a banzaba. Bakuma zai samu sauƙin ganowarba sai da wani a tsakani. Shiyyasa na tura Uwaliya ta fara sauka gidan Lurwanu ta kwana biyu sannan aka kaita wajen Zainabu. Ita kanta batasan amfani zamuyi da itaba, na ɓoyene saboda fahimtar idanunta a buɗe suke dasan kuɗu itama. Ko nawa Lurwanu ya bata lallai zata amince tai masa aikin daya buƙata akan Zainabu. Ankoyi sa'a shirinmu ya tafi dai-dai saboda Nasiru ma mutumne mai ƙwaƙwalwa da hikima. Hatta da yawan shigowa Najeriya da Abdallah ke yawan yi suna ganawa da Lurwanu duk mun sani dan duk inda yasa ƙafa Nasiru na biye da shi batare da yasani ba. Kai hatta binmu da Abdallah yayi ƙasar da akaima Zainabu aiki nasani. Dan ko a randa Yahya ya gansu suna magana shi da Lurwanu nima na gansu, sanin da nayi babu ta hanyar da zasu iya cutar da Zainabu saboda tsaron da take samu a wajen yasa na watsar da al'amarinsu. A yanzu haka mijin maman Aaida shine ya taso mana ƙeyar Abdallah zuwa Najeriya harya halarci wannan bikin duk da yazone a makare”. Ta ƙare maganar da nuna inda Abdallah ke zaune kansa a duƙe tamkar munafuki. Harga ALLAH da yawan mutanen dake falonma sai yanzu sukasan da zamansa a falon. Hajjo ta sake gyara zamanta tana duban kowa. “Nasan wasu zasuce miyasa duk nasan wannan amma na ɓoye matsayina na mahaifiya ga waɗan nan yara su duka?. Amsarku itace duk da ni mahaifiyace a garesu fitowa da lamarin kai tsaye dasa sabuwar fitinace da zatafi wadda muke ciki girmama. Dan inhar da tun a wancan lokacin na fiddo komai zasu kare kansu akan ba haka bane, su jefa zuciyarmu a ruɗani mu duka kokuma su canja salo, ko komai ya ɓaci duniya tasan halin da muke a ciki maƙiyanmu dake a waje su sami ƙofar yin kutse cikin wannan zuri'a su ƙarasa ɓarar da sauran abinda ya rage daga garemu. Ƙyaƙyƙyawar rayuwar da aka gina tsahon shekaru zata wargatse ta lalace kowa ya fita a hayyacinsa. Idan hakan ta kasance banci riba ba. Sannan wahalar da malam ya sha akan son gina zuri'arsa baici riba ba kenan shima. Dukansu ni na haifesu, tun a ƙuruciya nasan halin kowannensu. Dama can Lurwanu hatsabibine tun yana ƙanƙaninsa, a cikin ƴan uwan nan nasa babu wanda baisha wahalarsaba. Kaifin addu'a ne kawai ya ladabtar da shi, sai kuma kawaici da iya zama da su da ɗan uwansu yayi. Na yarda inhar ka samu ƙyaƙyƙyawar tushiya a cikin yabanyarka da izinin ALLAH zaka azurta da ƙyaƙyƙyawar albarka. Kasancewar ɗan malam ɗa nagari, mai haƙuri da kawaici, mai juriya da riƙe girmansa matsayin babba ga ƴan uwansa shine ya taimaki wannan zuri'a da kaiwa haka batare da mutanen waje sunyi tunanin samun ɓarakar shigowa cikinmu su wargazamuba. ALLAH yayima ɗan malam baiwa da ƙyautar abubuwa da yawa. Ilimi, hankali, dattako, dukiya, sanin ya kamata, nasaba. Sai dai hakan ba yana nufin zai more rayuwarsa ɗari bisa ɗari ba tunda ya haɗa komai. Shiyyasa ALLAH ya jarabcesa da atsabibancin Lurwanu dana matar ɗan uwansa Mustapha. Suka dinga wajiga rayuwarsa saboda UBANGIJI ya gwada ƙarfin imaninsa. Koni da nake mahaifiya a garesa inajin sha'awar koyi da halayensa na haƙuri da juriya duk da zuciyarsa na ƙonuwa shi da matarsa da ƴaƴansu. Wannan kawaicin da uziri shine ya kaimu ga matakin nasarar da a yau gashi su da sukecin dunduniyar sane a gabanmu suna faɗin tsiyatakun da suka aikata da bakinsu, miyafi wannan nasarar daɗi ga bawa kuwa?”. Abban Adawiya ya share hawaye da fadin, “Babu inna, wlhy babu makamancin wannan nasara kuwa, dan hakan yana nuna mana duk mai haƙuri da tsayawa akan gaskiya, da adalci gana ƙasa da shi, ma'abocin bautar UBANGIJI, ALLAH bazai taɓa taɓar da shi ba, ALLAH bazai taɓa ƙasƙantar da shi ba. ALLAH bazai taɓa wulaƙanta rayuwarsa a hannun azzalumai ba. Ni shaidane akan hakan, dan Lurwan yaso jan ra'ayina sosai akan lamarin Yaya, kullum zancensa shine Yaya cutarmu yake a ɓoye. wai tayayama za'ai ace a raba mana gado tare, amma yazo ya fimu komai. Yafi kowa kaso mai tsoka a duka kamfanonin mu. Ga wasu harkoki da yakeyi kuma a gefe masu bala'in bashi kuɗi. Sannan kuma wai ai muduka munada ilimin addini amma tayaya za'ace kowa yafi sonsa da ƙaunarsa dajin maganarsa. Hatta mahaifiyarmu sai abinda Yaya yace takeyi a gidannan. Acewarsa wai Yaya ya asirce kowane kawai amma yake fakewa da malanta. Da farko na fara bin ra'ayinsa. Sai dai ba'ai nisaba ALLAH ya soni da rahamarsa ya fargar dani, danni dai ban taɓa ganin wani abu saɓanin ƙyautatawa ga yaya ba. Da kuɗinsa na gado ya tsaya mana mukai karatu duk da kuwa muma muna dasu. Da kuɗinsa na gado ya dinga mana hidimar rayuwa tamkar mahaifi. Idan mukai kuka shima sai kaga ƙwalla a idanunsa. Idan mukai ciwo shima sai kaga raɗaɗin a fuskarsa. Idan mukai dariya sai kuga tashi fuskar faɗaɗe da murmushi mai tsada. Shine ya nuna mana hanyar tashi mu nema na kanmu, dan shine ya fara shan wahalar kafa dukkan kasuwancin da ayanzu sune suke riƙe da duk wani motsinmu. Shine ya tsaya akanmu mukai karatu tuƙuri bayan ya tattare martabar mahaifinmu ya riƙe mana bai bada ƙofar da zamuyi sakacin da zata kufce mana ba. To miyasa son zuciya zaisa zamuyi sakaci ya sargafe tunaninmu?. Hakan yasani janye jikina daga wannan mummunar a ƙidar naita istigifari akan zargin da aka sakani nai masa babu gaira babu dalili. Ashe ya koma sun ƙulle da matata suna cutama yaya da zuri'arsa da basujiba basu ganiba. Minene laifin waɗan nan ƙananun yaran da basuma gama