Sashe 61
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Motocin na shigowa anguwar ana fara kiraye-kirayen sallar magriba. Yoohan na kwance shiru a jikin kujera idanunsa a lumshe. Baisan inda ake shiga da fita ba har saida motocin suka tsaya a ƙofar katafaren gate ɗin. Hakan sai yayi dai-dai da fitowar baba malam da Abban su Adawiya, sai Malam ƙarami da Omar da sauran samarin gidan da yara amma iya mazan kawai.
Duk da yanda guards ɗin Yoohan suka firfito suka zagaye motar da yake a ciki hakan bai saka fuskokin su baba malam sauyawa daga fara'ar dake tattare da suba. Akan idonsu Hamza Ibrahim ya fita. Kafin Yoohan da Solomon ya buɗemawa shima.
Shima a gaban idanun nasu ya fito, bayan ƙafarsa kuma da sarƙar Cross ɗinsa suka fara cin karo kafin cinkusashshiyar fuskarsa. Abinda zai baka mamaki a tare su baba malam sukayo caa a kansu. Cikin ƙyaƙyƙyawan tsari na masu ilimi da baiwar hikima suka tarbesu. Wani iri Yoohan yaji a ransa shima duk da kuwa dama ya fahimci masu gayyatar tasa musulmai ne, amma sai ya dake ya basar.
Duk yanda yaketa faman musu shan ƙamshi da cika da batsewa babu wanda ya canja yanayin nasa, saima sannu da zuwa da suka shiga jera musu tare da basu hannaye suna musabaha har guards ɗin. Kafin baba malam ya bama Malam ƙarami da Omar damar shiga da Yoohan ɗin ciki. Danshi Hamza Ibrahim ya buƙaci a inda zaiyi alwalane kai tsaye.
Yoohan dai baiyi musu ba yabi bayan su Omar, sai dai idonsa da zuciyarsa nakan hasaso masa a inda ya taɓa sanin fuskar baba malam a rayuwarsa. Guards ɗinma bin bayansu sukai. Omar zaiyi magana baba malam ya girgiza masa kai alamar ya barsu.
Tun a farkon shigowa gidan Yoohan yasan masu gidan sun wuce raini, dan babu abinda nasu gidan zai nuna masa sai dai kayan ƙawa da ƙyale-ƙyale, nasu baba malam ma yafi nadu girma sosai. A haka su Omar suka kaisa har falon, guards ɗinsa biye da dasu kamar wasu jela ko suna ganin za'a cutama Yoohan ɗinne oho musu. Sai da sukaga ya zauna suka ajiye masa ruwa da lemo kozai buƙata sannan sukai masa sallama suka fito, duk da basuji ya amsa musu da ƙyau ba. Dan Solomon ma tunda ya fahimci inda suka kawo kansu sai takaicin ogan nasa da buɗaɗɗen ra'ayinsa ya shiga masa zafi a rai. Dolene yay saurin sanarma Madam Chioma kafin a bama Boss ɗin nasu wani abin yaci a tsafesa.
Yana cikin shawara da zuciyarsa ta yanda zai silalo daga cikin falon ya kira madam ɗinsu sai ga sallamar su Baba malam, da alama ana idar da sallar magrib basu zaunaba suka shigo gidan. Aiko takaici kamar ya kar Solomon, amma duk da haka saida yayi dabarar turama Momy text message ko za'a dace wayar na a hannunta ta gani.
Koda suka shigo Yoohan na'a zaune yanda yake baiko motsaba, sai dai yana binsu da kallo ne ta ƙasa ido. Abban Adawiya da suka taɓa haɗuwa a orphanage ranar da suka buge yaron nan sai ganin Yoohan ɗin ya sakashi matuƙar jin mamaki. Duk da ya jima a ransa yana zargi da hasashen kodai shine mai musu wannan ɗawainiyar. Rashin tabbas ɗin hasashen nasa yasa bai taɓa yin magana ba sai yanzu ya ɗan gwargwaɗa ma baba malam cikin harshen larabci.
Murmushi kawai baba malam ɗin yayi, cike da kulawa ya maida hankalinsa akan Yoohan da suka fahimci a takure yake da kasancewarsa a wajen. Basu damuba, dan sunyi gamo da waɗandama suka fisa taurin kai da aƙida amma cikin amincin UBANGIJI sun sami nasarar canjasu. To balle shi kuma dama suka fahimci zuciyarsa nada rangwame tunda har ya iya kasancewa maison ƙyautatawa marayu.
Duk da baba malam yaga saɓanin abinda yay tammani daga Yoohan hakan baisa ya canja komaiba daga ɗokantuwa da mutunta baƙon nasu. Hakam ɗan uwansa da ƴaƴansu basu nuna wani mamakinsu a fili ba ko ƙyanƙyamin su Yoohan ɗin, kowa ya shanye a ransa. Ba Yoohan kawai ba, dai-dai da guards ɗinsa an mutuntasu fiye da zatonsu, dan suma ca akai su zauna ayi buɗa bakin dasu. Duk da suna noƙewa saboda boss ɗinsu haka baba malam ya matsanta musu. Ganin Yoohan kuma bai tanka musu ba, yamayi kamar baisan mi akeyiba sai suka saki jiki aka kwashi gara da su, a ransu kuma suka koma zuba santi dajin kimar mutanen musamman yanda aka nuna musu suma mutanene masu daraja ba bautace kawai aikinsu ba.
Yoohan kansa da keta noƙewa da farko tuni baba malam ɗin ya tsaresa sai yaci, harda nuna masa idanfa baici da hannunsaba shi zai basa da kansa to, kuma ɗura zai masa. Karan farko a rayuwata da ni kaina mai ɗakko muku rahoto naga murmushi a fuskar Yoohan yau. Dan shi kansa a bazata ya saki lallausan murmushin ga baba malam ɗin.
Baba malam yace, ‘Masha ALLAH’ a ransa, duk da yau ya fara ganin Yoohan sai yaga murmushin yay bala'in masa ƙyau. Haka dai suka gudanar da buɗa baki cikin nishaɗi da farin ciki. Guards ɗin Yoohan dake ɗar-ɗar harda Solomon mai hasashen banza sai gasu sun kwashi gara suna washe baki dajin farin ciki a ransu.
Kiran sallar isha'i ya saka su baba malam ficewa massalaci akabar Yoohan da tawagarsa. Sai dai kuma bayan fitarsu babu jimawa shima sai ya miƙe da nufin ɗan yin tattaki ko cikinsa zai sauka. Shi kansa yasan ya jima a rayuwarsa baiyi irin wannan cin abincinba, ballema a ɗan tsakanin nan da yake cikin halin ha ula'i. Ta ƙaramar ƙofar da yaga su baba malam ɗin sunbi shima ya bi, kai tsaye ta kaisa ƙatuwar harabar massalacin kuwa.
Ko'ina ƙwanyar yake da haske tamkar rana. Ga mutane maza da mata harma da yara cike da massalacin harda mata. Yoohan yay tsaye jikin katanga yana kallonsu cike da nazari har aka tada salla. Ba massallacin kawai ba hatta anguwar kanta sai yaji ta ɗauki shiru gaba ɗaya, babu abinda kakeji sai sautin karatun salla da baba malam keyi. Lokacin da ya kammala karanta fatiha mamu suka amsa da “Amin!!!!” sai gaba ɗaya tsigar jikin Yoohan ta tashi, zuciyarsa tai wani bala'in tsargawa har saida ya rumtse idanunsa.
Baisan dalilin daya hanashi komawa ciki ba, haka ya cigaba da tsaiwa har sukai ruku'u. suka sake ɗagowa sukai sujida. Tsigar jikinsa sake tashi tayi a karo na biyu, dan yanda sukai sujidan gasu a sahu nagartacce dolene ko musulmin ya gani yaji ƙarin imani a ransa balle wanda bai taɓama yin sujudar ga UBANGIJI ba.
A hankali Yoohan ya ɗaga ƙafafunsa ya fara ja baya da ƙyar harya fice a harabar massalacin ya koma cikin gidan. Haka ya cigaba dajan jiki harya isa falon da aka saukesu da ƙyar. Tsitt guards ɗinsa daketa faman surutun santin abincin da sukaci sukayi ganin ya shigo kamar a birkice. Da sauri duk suka miƙe tsaye domin girmamawa. Solomon ya taimaka masa ya zauna.
Sai kuma duk hankalinsu ya tashi, amma yanda baiyi maganaba suma sai basuyiba sukai dai masa tsaye cike da tsoron kodai an cutar dasu ɗinne kamar yanda sukai hasashe tun farko?.
Har aka idar da sallar asham Yoohan bai dawo hankalinsa ba. Baba malam da ayau baije tafsir ba dama ya ɗauki alfarma suka sake shigowa. A yanda yaga Yoohan ɗinne ya saka hankalinsa tashi. Tambayar guards ɗin ya shigayi a ruɗe. Nan sukai masa bayanin abinda suka sani kawai. na cewar Yoohan ya fitane shan iska sai ya dawo musu a haka, dama kuma bashi da isashen lafiya, bama suyi zaton zai iya zuwa nan lafiya lau hakaba.
Ɗan shiru Baba malam yayi cike da nazarin bayanin da Solomon yay masu na rashin yin barcin Yoohan, kafin ya zauna kusa da Yoohan ya janye hannunsa daya dafe kansa da shi ya maye gurbinsa da nasa, addu'oi ya fara masa yana tofawa, ya kuma saka Abban Adawiya yin wasu addu'oin a ruwa ya miƙo masa. Kamar Solomon zaiyi maganar karsu bashi sai dai ya kasa saboda nauyin da bakinsa yay masa da kuma kwarjinin mutanen.
A gabansu akaba Yoohan ruwan addu'ar yasha. baba malan ya zuba a hannunsa kaɗan ya kuma shafa masa a fuska. A take ya fara sakin tagwayen ajiyar zuciya a jajjere. Ya buɗe baki da ƙyar yace, “Thanks”. Murmushi baba malam yayi kawai, kafin yace, “inaga ya kamata a kaiku masauki ka huta, dan da alama idanun nan naka barci sukeji”. Cike da mamaki Yoohan ke kallon baba malam, duk da dai ya kasa yarda su haɗa idanu da ƙyau dan bala'in kwarjini baba malam ɗin ke masa shikam. Sake murmusawa baba malam ɗin yayi. Ya ɗauke kansa ya maida gasu Omar.
“Farukh a kaisu masauki ko”. Da sauri Omar yace, “To Abba”..
Da gaske Yoohan barci yakeji fiye da zatonsa, dan haka ya kasa musama baba malam duk da kuwa shi a yau yaso su juya zuwa Abuja shi da Solomon da Manager, guards ɗinsa kawai yay shirin bari su kwana a kanon da safe suma su wuce. Amma sai yaji babu abinda yafi buƙata kamar kwanciya a yanzun.
Su Malam ƙarami sun kaisu gida mai ƙyau matsakaici dake gaba da gidansu kaɗan, inda nanne masaukin da su baba malam ɗin kan sauke baƙi daman. Tsaf yake gidan, saima uban ƙamshi mai saka kwanciyar hankali da ya keyi. Duk da babu wutar nefa nanma an tada gen.....
Abin mamaki sai ga Yoohan kamar bugagge, suna shiga wajen kwanciya ya buƙata. Yana ganin gado kuwa ya zube akai yana sauke ajiyar zuciya abin tausayi.
Takalma da necktie ma sai Solomon da Manager ne sukai
dabarar zare masa. Hakama jacket ɗin suit ɗinsa. Sai suka barsa da shirt ɗin da dogon wando kawai.
Manager ne ya kwana tare da Yoohan duk da shi Solomon baiso hakaba. Bawan ALLAH nan yanda ya kwana bautar UBANGIJI haka ya ja doguwar addu'ar samun haske daga Yoohan ɗin. Hakama su baba malam, ranar mafi yawan addu'oinsu akan Yoohan suka yisu da ga su har iyalansu. Da asuba aka kawoma Hamza abin buɗa baki, daga Yoohan har guards ɗinsa barci suke kwasa masu a lokacin.
★★★WASHE GARI★★★