← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 211

Sashe 108

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

         An tarbesu yanda basuyi zato da tsammani ba, ba kuma komai ya jawo hakanba sai dogon gargaɗin da papa da Yoohan ɗin sukayi, sai kuma sauran matan su Uncle Mike suma sunsha gargaɗi wajen mazajen nasu. Shiyyasa suka zama gaba-gaba wajen ƴan amsar amarya basu bari su mama debora sun kwafsa ba. Koba komai dangin Nu'aymah sunji ƴar nutsuwa, sai dai har cikin ransu sunji tausayinta na zama cikin waɗan nan gurguzin kahiran da idanunsu ke buɗe da wayewar karatu dana kuɗi. Amma sun rigada sunyi imani da cewar UBANGIJIN daya ƙaddara shigowarta cikinsu, yafisu sanin alkairi da hikimar yin hakan. Sun sake mata nasiha sosai, tanata kuka dai duk da bata fahimci ina aka kawota ba.
         Duk da tarin abinci da kayan sha da aka kawo musu basu taɓa komaiba, sai ma miƙewa da sukayi da zummar tafiya bayan sun leƙa ko ina na sashen nata sukaga yanda company ya tsarashi gwanin birgewa. Ƴan gyare-gyaren da suka ƙara mata ba wasu masu yawa baneba, shiyyasa basu jasu lokaci ba.
      Ganin suna shirin tafiya kamar yanda Abba daya fita tuni suna tare da papa a harabar gidan papa yace ya zasu tafi bayan ana shirin yin taro suma anan.
     Murmushi Abba yayi, yace, “Ai su anjima kaɗanma zasu koma kano, muna musu fatan alkairi dai”. Yoohan da duk ke saurarensu yay saurin cewa, “Uncle Please ka barsu, na maka alƙawarin insha ALLAH zasu sami jirgin safe saisu wuce. Itama zata damu idan taga babu family nata a wajen”.
      Ɗan jimmm Abbah yayi yana nazari, yasan gaskiya Yoohan ɗin ya faɗa, duk da dai su ba ɗabi'arsu bace yin wannan bidi'oin, to amma a yanzu basu da iko akan Aymah tunda sun kawota gidan mijinta. Basu da ikon kuma cewa su Yoohan bazasuyi nasu shagalinba tunda shi aure rahama ne, yin shagali a cikinsa kuma ba aibu bane. Abinda kawai ba'a bukata wuce gona da iri da yin almabazaranci da dukiya. (Wadda a yanzu hakan ne yafi yawa a bukukuwanmu. shiyyasa tun a filin bidi'oin ake zazzage daraja da albarkar auren atafi da gayyar sheɗanu😪🤦🏻).
       Kansa ya ɗan jinjina da faɗin, “Tom shikenan. Amma bara na fara kiran Yaya (baba malam) na sanar masa tukunna”. Wannan ɗabi'ar tasu na birge Yoohan matuƙa.
       Bayan Abbah daya koma gefe ya gama waya da Baba malam ya dawo yana faɗin, “Shikenan zasu zauna ɗin, amma yanzu su fito muje idan lokacin yayi sai a kaisu can. Idan mun koma sai ƴan uwanta suzo su tayata zama su yanzun”.
       “Muna godiya Uncle, ALLAH ya ƙara girma”.
    Murmushi kawai Abbah yayi, hakama Papa fuskarsa kamar gonar auduga.

★★★★★★

             Tun bayan magriba mai kwalliya tazo yima Aymah. Amma saita tubure akan sai tayi sallar isha'i. Dole aka haƙura akan hakan, duk da su ƴan bikima harsun fara wucewa inda za'a gudanar da shagalin. Duk yanda taso su Amal su sanar mata wanene mijin sunƙi. Dan Amal da Yusrah da wasu ƙawayen Amal ɗin biyu maƙwaftansu suna nan tare da ita. Adawiya kam batazo ba wai kanta ke ciwo tasha magani sai anjima zata biyo su Aunty hibbah. Hakan bai wani damu Aymah ba, dan ita mantawa take ma da babin wata Adawiya yanzun.
      Bayan an idar da sallar isha'i aka rangaɗama amarya Nu'aymah kwalliyar garari. Dan ko makaho ya taɓa saiya jinjina. Hakama su Amal an musu tasu. Momy daketa danne zuciyarta bisa shawarar ƙawartace da kanta ta kawoma Aymah rigar da zata saka wadda garariya garara har ƙasan amuruka akaje sayota daga aljihun papa da umarninsa.
      Nu'aymah taso yin gaddamar sakawa. Amma yanda Momyn ke mata da lallashi ita da ƙawarta ya sakata amsa ta saka ganin rigar akwai hannu a jiki. Ammafa ta bala'i-bala'in haɗuwa sai ɗaukar ido takeyi. Farace tas sai kwalliyar furanni pitch color data ƙawata rigar. Hakan yasa dogon takalminta da shi kansa abin kallone ya kasance pitch. Sarƙa ɗankwali duk pitch. Humm lamarinfa ba'a cewa komai. Ita da kanta Aymah tasan ta haɗu, sai dai zuciyarta a raunane take, dan ta tabbatar ba Yah Ab ɗinta bane angonta. Musamman data san danginta basa irin wannan shirmen bidi'ar, kuma tasan ba Yah Naser bane shima, dan da ace shine katsina za'a kaita. ‘Ni Zainab wanene iyayena suka bama ni’ ta faɗa cikin zuciyarta tana kukan zuci, a fili kuwa idanunta sun cika da ƙwalla. Tayi jarumta sosai wajen ganin basu zubo ba.
Chapter 108 · 0% Book details