← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 211

Sashe 162

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

..............A hankali soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ta cigaba da shiga tsakanin ma'auratan masu banbancin yare da yanki cike da birgewa. Yayinda Aymah ke matsayin malama ga Yoohan a ɓangaren ilimin addini shima sai ya zame mata malami a ɓangaren sanin soyayya da rayuwa. Dan sosai yake yawo da ita a lungu da saƙo na ƙasar Austria har wasu jihohinma suna zuwa yawon buɗe ido.
      Tun tana tsoro da masa raki a shimfiɗa harta fara sakin jikinta da sabawa. Dan jarumin nata namijin gaskene babu wasa. Baya takura mata yanda zata wahala. ba kuma ya barinta ta shagala.
      Sai ga Nu'aymah tai wani irin murjewa da ƙibarta na dawowa, (kunsanfa wannan harkar na gyara wasu matan harma da mazan🙈, shiyyasa da yawa amare farkon aurensu zakaga sunyi ɓulɓul da su🏃). To ga Nu'aymah ma dai an dace. Balle abin ya haɗa da kwanciyar hankali data samu, babu mai hantararta babu mai damun rayuwarta. Abinci saita zaɓa. Kullum zatai waya ko video call dasu Umm. Ga lafiyar jikinta Alhmdllh sai ƙaruwa take ƙarayi dan tana shan maganinta da ƙa'ida kasancewar Yoohan tsaye yake akanta da tsantsar kulawa.
      Takanji yana waya da papansa da momynsa (Madam Chioma) sai dai yanda bai taɓa cewa gashi su gaisaba itama bata taɓa nuna sha'awar hakanba. Garama Momy ranar ta kira yana wanka har sau uku. Ganin wayar na wajenta ya sakata ɗagawa suka gaisa. Sai dai yanda Momyn ta amsa mata a daƙile ya sosa ranta. Dan ta fahimci har yanzu da sukai nesa da juna ba ƙaunarta takeyiba. Su Momy Destiny ne dai ta gaisa dasu kusan sau uku-uku harda su Victoria. Amma su tom and jarry mama debora ko yaya jiki basu taɓa aiko mata da shiba balle suce zasu gaisa da ita a waya. kuma taji ranar duk sai da suka gaisa da Yoohan. Gebrail nema ta lura idan ya kirashi baya ɗagawa, daga bayama sai taga ya sakashi a black list.

         Gaba ɗaya ta hana Solomon musu gadi. Dan yanzu duk inda zasuje tuburewa take akan itadai bazataba inhar sai Solomon ɗin ya bisu. Hakan yasa Yoohan ya yanke shawarar kawai ya sallamesa ya koma Nigeria, dan baiga amfanin kisan kuɗin da yake ba a dalilin zaman Solomon ɗin tare da su.
       Randa ya samu Solomon da maganar komawa Nigeria hankalinsa yayi matuƙar tashi. Ya kira iyayen gidansa ya sanar musu da hukuncin Yoohan ɗin. Hakan yasa papa kiran Yoohan ya nuna masa bai amince da dawowar Solomon gidaba. Dan bazai yarda ya barshi shi kaɗai yana yawo ƙasashen duniya a cutar masa da shi ba.
       Yanda Aymah ta tubure kuma akan indai Solomon zai cigaba da kasancewa da su sai dai ita ta koma Nigeria wlhy yasa kan Yoohan ɗaukar zafi. Yayima Aymah lallashin duniya akan tabar zancen Solomon tunda papa ya dage amma sam taƙi saurarensa. har takaisu dayin ɓacin rai ranar akai barci kowa na ƙarshen gado. Washe garima taƙi kulasa shima ya shareta. Sai daga baya yaso su shirya taƙi. (A raina nace hummm Yoohan bakasan kafiyar Aymah bane ba).
        Wannan tuburewar tata ya ƙara bashi haushi. Harya yanke shawaran ta shirya ta koma Nigeria tunda bazataji lallashinsa ba.
      A mamakinsa kuwa sai yaga ta hau haɗa kayanta. Dan itafa tabbas tayi alƙawarin bazata sake zama inuwa ɗaya da Solomon ba. Dan tsaf ta gama fahintar wannan nanema Yoohan ɗin da yakeyi akwai wata a ƙasa. tabbas da gaske akwai abinda su papa suke ɓoyewa game da Yoohan ɗin. Inba hakaba minene na nana masa guard a duk inda yake. Sannan sau biyu tana kama Solomon na waya da papa. Na farko yare taji yanayi sai turancin daya saka kaɗan ya sakata fahimtar papa ne. na biyu kuwa da turanci sukai magana. Hakan ya sata jin komai akan duk wani motsinsu Solomon yana sanarma papa. Dan a ranar shi papan har maganar ya kamata ta koma Nigeria yayma Yoohan. Amma shi Yoohan ɗin ya nuna baya bukatar yana wani ƙasa matarsa na wata ƙasa. A ransa kuwa ya ɗau alwashin Aymah bazata ƙara zama a gidanba baya kusa saboda Gebrail. Dan ba ƙyalesa yayiba. ya ɗau alwashin duk randa ya dira Nigeria sai Gebrail ya yabama aya zaƙinta.
      Ganin da gaske shirin tafiyar take ya sakashi sakkowa daga fushinsa shi. Ya fara lallashinta amma taƙi saurarensa. Saima kuka da take masa mai cin rai. Daga ƙarshe dai dole ya kira baba malam akan dan ALLAH ya lallasar masa ita. Dan shikam a yaune ya kuma tabbatar da borin Aymah bana wasa bane. Dan ko abinci taƙi ci, taƙi shan maganinta. ta birkice masa ita kawai ya kaita airport ta wuce gida kokuma ta tafi da kanta.
       Murmushi baba malam yayi kawai yana girgiza kansa. kafin ya sauke ajiyar zuciya ya farama Yoohan nasiha. Daga ƙarshe ya koma masa faɗa akan sakacinsane ai ya saka Nu'aymahn iya bijirema umarninsa. Dan haka ya nutsu sosai wajen riƙe gidansa da ƙyau. dan su mata wani lokacin zuma ne sai da wuta. Sannan wutar kara ne sai da iji. Ba'a sakaci da su sannan ba'a musu tsauri da yawa. ana riƙesune tsaka tsaki sai a samu jin daɗin duniya.
     Sosai Yoohan yaji shawarar sirikin nasa. tare da ƙarajin ƙaunarsa a cikin zuciya da ɓargo. Daga haka ya haɗashi da Nu'aymah kamar yanda ya buƙata.
        Zata fara masa kuka baba malam yay mata jan ido. faɗa sosai yay mata akan tashiga hankalinta mijinta ba abin rainawarta bane. Idan batai wasabama sai yazo har Austria ɗin ya hukuntata. Sai da ya tabbatar tayi laushi sosai da faɗansa sannan ya koma yimata nasiha. Daga baya kuma ya buƙaci jin dalilinta na takurawa akan Solomon ya barsu.
           Kasancewar Yoohan yana koyon hausa a wajenta ya sakata yin amfani da manya-manyan hausa wajen yima baba malam bayani akan abinda ta fahimta da zaman Solomon tare da su. Ta kuma bashi labarin abinda ya faru akan maganar hoto, harma da videos ɗin da Omar (Richard) ya nuna mata kwanakin baya da suka shuɗe. shi kansa baba malam ɗin hankalinsa yayi matuƙar tashi. sannan zarginsa ya fara zama gaskiya kenan. Albarka ya saka mata sosai da faɗan rashin sanar masa zance hoton da tayi tun a wancan lokacin. Duk da ya fahimci mijinta take son bama kariya akan matsalar da gajeren tunaninta ya kasa faɗaɗa mata. Yace,
      “Mamana yanzu ina hoton yake?”.
Hawayenta ta share da jan majina. Tace, “Abba yana nan Nigeria a cikin kayana”.
       “Masha ALLAH. ALLAH yay miki albarka. Saka wani ya ɗakkosa bazai yuwuba. Dan haka zamuyi haƙuri har ku dawo ƙasar sannan musan ta inda zamu ɓuloma al'amarin. Batun Solomon kuma bata hanyar rikici zaki yakicesa a jikin mijinki ba. Cikin hikima da wayon da ALLAH ya baku na mata da tarbiyyar Umm ɗinki zakiyi amfani wajen sakashi ya sallamosa. Ko kin taɓa ganin muna rikici da Umm ɗinki ne a gidannan?”.
     Kanta ta girgiza masa tamkar tana a gabansa. Sannan tace, “A'a Abba”.
      “To amma shine ke zakije kina rikici da mijinki. har yana taroki kina ƙwacewa? Wannan shashanci ne ai. Sannan kina zubar mana da kimar tarbiyyar da muka baki. Mu mazafa da kike gani munada wuyar sha'ani dason nuna mulki a gidajenmu, shiyyasa duk macen data fahimci haka ta iya zama damu mutane suke ganin kamar ta mallake mijintane  nanko ba haka baneba. juriyace kawai da iya zama da mijin tayi. Ki kula da ƙyau. Mahaifiyarki abin koyice a gareki akan zaman takewar aure. Babu wanda zaice ga Jannat da wata matsala a gidan aurenta. da daɗi babu daɗi ta jure ta shanye komai. Yaya muka kwana yaya muka tashi ta jurema ranta. har takai wasu na ganin tsorona takeji da yawa. Nanko ba hakan bane. Mune muka san sirrin kammmu fiye da duk wanda ke zagaye damu. Karna ƙarajin haka kinji ko?”.
       Nu'aymah na sharar ƙwalla tace, “Insha ALLAHU Abba bazaka sake jiba”.
       “To Alhmdllh naji daɗin hakan kuwa. ALLAH yay miki albarka keda mijinki damu baki ɗaya”.
      Cike dajin kunya ta amsa da amin. Daga haka suka ajiye wayar. Ta ɗan saci kallon Yoohan dake kwance ciki sofa idanunsa a lumshe tamkar mai barci. Tashi tai a hankali taje ta ajiye masa wayarsa a saman ciki batare datace komaiba.
     Shima buɗe idanu kawai yayi ya bita da kallo harta shige toilet.

_________★★
Chapter 162 · 0% Book details