← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 211

Sashe 3

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

         Can bayan ɗakunan sashen samarin gidan Adawiya ta nufa, dan tasan canne kawai babu mutane. Waje ta samu ta zauna tasha kukanta, yayinda zuciyarta ke shirya mata mugayen abubuwa game da Nu'aymah da matakin da zata ɗauka a kanta na dakatar da wannan auren, tayi alƙawarin kota halin ƙaƙa saita mallaki Abdallah a safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai kuma ta rabashi da Nu'aymah, idan kuma har hakan bata tabbata ba to sai dai suyi zaman kishi ita da Nu'aymah kokuma kowa ya rasa. Dan ko sama da ƙasa zata haɗe bazata barma Nu'aymah Abdallah ba wlhy........
        “Adawiya! Adawiya!!”. ta jiyo ana ƙwala mata kira. Tsaki taja mai ƙarfi kafin ta miƙe tana kakkaɓe jikinta daya ɗan ɓaci da ƙasa, duk da ma ita ko shiryawa batayiba. Fitowa tai inda zata iya ganin mai kiran nata. Da sauri taja baya saboda karo da suka kusa ci da Yah Abdallah. Ƙirjinta yay wani mugun harbawa, a take ta fara neman nutsuwarta ta rasa. Kwarjininsa da matsanancin son da take masa suna neman birkitata gaba ɗaya ta kasa riƙe kanta....
         Sassanyan Murmushinsa ya sakar mata yana ɗan ware idanunsa a kanta, “Oh Hassanar amaryace haka bata ko shiryaba?”. Duk da maganarsa batai mata daɗiba saita saki masa murmushi, ta matsa kusa da shi tana shaƙar ƙamshin turarensa mai daɗi, “Yah Abdallah dama ka iso?”.
       “Ya za'ayi ki sani tunda ance kina nan kinata kukan rabuwa da Husainar ki”. Baki ta buɗe zatai magana sai kuma ta fasa tana kallon Amal data rako Yah Abdallahn. “Kiranmi kike ƙwalamin ke kuma?”. Baki Amal taɗan taɓe tana cigaba da latsa wayar hannunta, “Kiranmi zan miki ni kuwa, dama Yah Abdallah ne ke nemanki, shine akace anga kinyo tanan”.
      Kafin tace wani abu Yah Abdallah yace, “Nine na sakata, wani aiki zakimin, Amal jeki abinki”. Kai Amal ta jinjina masa, tai gaba abinta batare data sake kallon inda Adawiya take ba. Sai da tai nisa da su sannan Abdallah ya sake kallon Adawiya, ganin shi take kallo sai yay murmushi.
       “Yaya dai ƙawar amarya na canja miki ne?”. “Sosaima kuwa Yah Abdallah”. Adawiya ta faɗa cike da yanga tamkar ba itace ta gama darzar kukaba yanzun.
      Murmushi yayi yana ɗauke kansa da faɗin, “To na gode. Kinsan aikin da zakimin?”. Kai ta girgiza masa batare da tace komaiba. “Sonake kije wajen Walimarcan ki satomin amaryata nan inason ganinta”. Wani takaicine ya soki zuciyar Adawiya har fuskarta sai da ta nuna hakan. Da mamaki Abdallah yace, “Yaya dai?”. “Babu komai Yah Abdallah” ta bashi amsa da rawar murya.
          “Okay, to maza ki shirya saiki ɗakko min ita, karfa ki bari kowa ya ganki musamman ma Hajjo”. Kanta ta ɗaga masa kawai, dan tasan idan tai magana kukane zai ƙwace mata. Da kallo Abdallah ya bita harta ɓacema idanunsa, haka kawai tausayin yaran ya kamashi, kowa yasan irin shaƙuwar dake tsakanin Adawiya da Nu'aymah tun ƙuruciya, sun tasone tamkar tagwaye a gidan, komai tare ake musu shi, yanzu kam ace zasu rabu rana tsaka ai dolene kaji tausayinsu.

        Adawiya kam koda ta bar wajen sashen Hajjo kakarsu ta nufa, babu kowa duk ana wajen walima, dan ana idar da salla kowa ya koma, daga cikin gidanma kana jiyo lecture ɗin da aka fara. Kwanciyarta tayi dan ta rantse bazata kira Nu'aymah ba.

★★★

        Tun Abdallah na kallon hanya na jiran ɓullowar amaryarsa Nu'aymah da Adawiya harya koma duban agogo. Kamar wasa sai ga mintuna ashirin sun shuɗe babu Adawiya balle Nu'aymah, abinda zuciyarsa kawai ta basa Hajjo ta hana Adawiya ɗakko Nu'aymah ne, maybe kuma tanacan tana wayon yanda zasu baro wajen. Ɗan murmushi yayi yana lumshe ido, sosai yake cike da ɗoki da ƙaguwar son ganin Nu'aymahr sa, yanason yaga yanda ta sake komawa yanzun........
         Kiran da ake masa a wayane ya katse tunaninsa, ya zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa ya duba. Zaid ne, kamar bazai ɗagaba sai kuma ya amsa tare da ɗorawa a kunnensa. “Hello Jibiya wai kana inane?”. Kamar bazaice komaiba sai kuma yay guntun tsaki da kallon agogon hannunsa. “Ina cikin gida mana, miya faru?”. “Cikin gida kuma? To mi kakeyi acan bayan kowa duk yana nan har amarya. Gashi nan Baba malam na nemanka to”. Baice masa komaiba ya yanke wayar. Badan yaso ba ya baro cikin gidan ya koma wajen walimar.
         Inda Nu'aymah ke zaune kusa kakarsu Hajjo ya kalla, tana zaune a yanda ya barta tun ɗazun, babu kuma alamar Adawiya a wajenma. Ɗan tsaki yayi a ransa ya ƙarasa inda Baba Malam yake.

             Masha ALLAH, anyi taron walima an tashi lafiya, inda malamai suka ragargaza lectures masu ratsa jiki ga ma'abocin saurare. Gaba ɗaya an gina sune akan zaman aure da kurakuran da muke tafkawa a cikinsa da hanyoyin magancesu, inda amarya da angonta sukasha addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

____________________________
Chapter 3 · 0% Book details