← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 211

Sashe 22

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dak'yar na samu na Shawo Kan Naseer akan ya koma gidan Sabida Kar Umma ta zargi wani Abu Yama nuna Mata ya hakura Dani zai zauna da Hindatu anan ya harareni nayi dariya nace yayi maganinta cikin sauki da kafarta zata gudu sai a lokacin yace na kawo shawara Mai kyau shi Kuma zai na karyar tafiya Yana zuwar mana.

A ranar da zai koma goron dutse da yamma Inna zuwaira da zata iya haifata tazo gidan Ashe Naseer Mai Tayani Zama ya Nemo min wacce Kuma zata ringa Tayani aikace aikace idan ya dawo Kuma sai ta tafi idan zai tafi sai ta dawo.

Sosai naji dadin zuwanta Dan Zan samu Mai debb'e min kewa kila ma har Abu Idan ya shigemin duhu Zan iya neman shawarar ta.

Naseer sai daya ajiye Mana komai har da kudin da bansan Mai zai yi.dasu ba Wanda har dagewa.nayi bazan karba ba Dan cemin yayi kullum sai yazo har abinci ma anan Zai ringa ci kwanciyar bacci ne zai ringa Mai dashi gidan.

Wajen karfe Tara ya Isa gidan fuskarsa kalar tausayi kamar gaske irin neman Naeema yake.

Tun Kan ya karasa Hawa sama yake jiyo Shewa.

Da Sallama ya tura k'ofar

Ba Wanda ya amsa sai juyowa da sukayi gabad'aya suna kallonsa Hajara har da mik'ewa tayi dage tana kallon bayansa Wai ko ya dawo da Naeema sai data ga shi ka dai ne ta washe baki tana "ko Kai fa ka hakura kazo ka zauna da Yar albarka tace.tana nuna Masa Hindatu.

Naseer Bai ce komai ba ya hau kallon mutanen palon Hindatu ce da Saffiya da Lami har dasu Tijjani sun zauna a tsakiyar Palon sai barjen Naman kaza suke ga kwalaban lemo a bubude.

Wato ma budurinsu kawai suke da Naeema ta tafi shi Kuma daga tafiyarsa shine su Saffiya suka dawo gidan.

Ba wacce yayiwa magana a cikinsu har Tijjani dake gaishe shi

Ya d'auke kansa tare da nufar d'akinsa Kai tsaye yana Jin muryar Umma tana duk hade Ransa Naeema bazata dawo ba idan ma.zai ware ya ware.

Sai daya Dan gyara d'akin ya watsa ruwa ya kwanta ya hau tunani su Naeema Dan lokacin ba wayar hannu da ya Kira yaji lafiyarsu Naeema

Dan kwanakin da yayi dasu ba karamin nutsuwa da kwanciya hankali ya samu ba babu abinda ya Kai Zama da iyali dadi.

Bai San da shigowar Hindatu ba sai ji yayi ta fado kansa shi kuwa ya mik'e da Sauri ya wancakalar da ita ya fara binta da wani mugun kallo Yana "duk ranar da Kika Kara shigomin daki wlh sai na balla Miki kafa juya ki fita"

Hindatu da Sauri ta fita ko minti biyu baayi ba Suka dawo d'akin da Hajara cikin masifa ta fara magana tana "Wai Mai kake nufi dani.ne. Naseer akan me zaka auri Yarinya Kuma ka ringa wulakanta ta toh wlh ka kaini bango Kar sake ka Kara korarta daga d'akin Nan Dan nan da wata tara inaso a haifomin jika Ni naga masifa duk da shegiyar matarka ta Shiga duniya ka ki nutsuwa ka dawo hankalinka toh wlh ka nutsu Dan nasan Tama Dade da mutuwa an rage mugun iri"

Wani irin kallo Naseer yabi Hajaran dashi ya d'auke kansa Bai ce Mata komai ba sai data gaji Dan kanta ta fita waje tare da Kara rufo musu kofa har da su mukullin.

Hindatu kuwa har da wani murmushnta ta Kara haye.gado tana murmushi.

Naseer shima mik'ewa yayi ya kullo k'ofar da mukulli ya zare ya saka key din a aljihunsa ya Shiga bandaki ya dauro alwala yazo ya hau Kan Sallaya.

Tuni ya ware murya ya fara karatun Qurani Hindatu kuwa ta mik'e hankali a balain tashe ta nufi wajen kofa ta fara jijigawa sabida Karatun sosai yake kona fatar jikinta.

Naseer kuwa Yana ganin Haka ya mik'e ya Ajiye Quraninsa ya nufi wajen Hindatun ya rik'e hannayenta biyu da k'arfi ya cigaba da karatunsa da k'arfi Yana tofa Mata yawun bakinsa.

Hindatu kuwa da iya karfinta take ihu tana Kiran sunan Hajara Dana Mahaifiyata take Hajara ta Gane Mai ke faruwa hankalinsu ya tashi.

Hajara kuwa ta bud'e k'ofar d'akin sai dai Naseer ya kulle k'ofar ta ciki itama da Sauri ta dawo Baya

Abinda basu fiye Yi ba b'acewa Dan sai Abu yaci tura sosai suke amfani da Wanan karfin.

Akan Dole Hindatu ta b'ace daga hannun Naseer

Duk da Naseer ya tsorata sai Haka ya cigaba da karatunsa da k'arfi tsoro na Kara shigarsa
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸

®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_

*Free Novel*

*Page 20*

Duk da yasan Hindatu da mahaifiyarsa suna cikin kungiya Bai San haka Abun yake ba yanzu macen da take tsafi wacce take Mayya mahaifiyarsa ta aura Masa Maganar Allah ne basa so suji kenan ma Mahaifiyarsa ba musulma bace toh a wane sahu zai sakata kenan kafura ko me innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Amma Abun mamaki mahaifinsa ya bashi labarin Mahaifin Hajaran Dalibansa ne Kuma musulmi toh Ina Hajara ta Samo wanan halin nata ko a cikin danginta akwai kafuran arna da basa sallah ne shiyasa ta Kauce hanya Haka bacewar da Hindatu tayi a hannunsa ya Kara gasgata Masa zargin su suka d'auke Nadeeya Yana ta imagining yanda hakan zai yiwu Wai mutum.ya b'ace sai da yaga zahiri.

Sosai.ya Kara k'arfin muryarsa Yana Shan alwashin ma Kiran mutane zaiyi suzo su Masa Saukar Qurani a gida.

Yana Jin Hajara na kwalla Masa Kira daga nesa da d'akin ya shareta

Shugubarsu kuwa ranta ba karamin b'aci yayi ba dan karatun ba iya Hindatu ya tab'a ba har da ita hakane yasa cikin bacin rai ta bayyana gabansu Hajara da lami Hajara kuwa suka zub'e a kasa suna k'ok'arin Magana ta daga musu hannu ta Shiga d'akinsu ta d'auke tukunyar Tsafin su da mudubinsu da duk shine karfinsu.

Tace wa Hajara sai ta hukunta su zata dawo musu dashi Kuma Hindatu bazata sake dawo wa Naseer ba

Kafin ma suyi magana har ta b'ace.

Hajara zaman dirshan tayi a kasa ta hau kuka Dan ko kad'an Bata San abinda zai rabata da Karfin tsafinta gashi Naseer yaja Mata daga ita har yayan nata an kwace musu k'arfin.

Naseer kuwa tsoro yasa ko bacci baiyi ba sai da aka Kira sallah asuba ya fito da alwala baiga kowa a palon ba sai Tijjani dake ta sharar bacci.

Shau da Masa carbin hannunsa yayi ya mik'e a firgice

Naseer kuwa yace Masa ya tashi su tafi.massallaci ya Fadi hakane sabida yaga ko shima baya sallar ga mamakinsa sai yaga ya mik'e yayi band'akin palon ya d'aura alwala ya fito.

Tare.suka.tafi Massallaci Naseer kuwa Bai dawo gidan ba sai da gari ya waye sosai wajen Shidda da rabi ya shigo gidan.

A Palo ya tarar da Hajara da idonta ya kumbure sabida kuka ta zauna tana ta jijiga kafa.

Wani irin kallo take Masa kamar zai wuceta kuma ya fasa ya tsugunna ya hau gaisheta.

"Burinka ya cika ka batamin komai Naseer na Haifeka Amma bakada burin da ya wuce ka bak'antamin toh burinka ya cika Hindatu ta bar rayuwarka Amma fa kasani wlh Tallahi sai na Kara Nemo wata na aura maka ita Idan Dan Naeema.kake ta haukar Nan toh wlh gwara ka Shiga hankalinka"

"Umma Maganar Allah ne bakwaso ko me karatun Qurani ne bakwaso nayi a gidana umma kinsan kuwa Allah ya hallicemu ne Dan mu San shi.mu Kuma bauta Masa Umma jiya karatun Qurani nake Hindatu ta b'ace a hannuna Umma kinsan kuwa hanyar da kike Kai b'ataciya ce ba mai billewa bace Umma Dan Allah Dan annabi ki tuba ki komawa Allah Umma wanan tsaface tsafacen ba Inda zai bille dake Umma tun sanin Dana Miki ban taba ganin kinyi Sallah ba Umma balle azo Kan sauran ibadan Umma lokaci Bai kure Miki ba ki tubarwa Allah ki dawo kan hanya Umma na saka ki a islamiyya ko Ni na koya Miki sabida kisan Allah "

"Naseer Ni ka saka a gaba kana zagi yanzu so kake kace bansan Allah ba kafura ce Ni ko me a takaice dai kana so kace Ni jahila ce ko Naseer Dan Hindatu ta b'ace a hannunka sai aka ce maka nima Ina bacewar Naseer Banga laifinka ba Naseer Kai da ka daga hannu ma zaka Mareni yanzu ai kanka ba daidai bane tunda wancan mayyar yar ta Shiga duniya ka haukace tunani ma ba daidai kake ba maganar da nake ma daban Wanda kake min daban idan ma.duk.kana wanan surutan ne Dan Kar Kayi aure wlh sai kayi

Kaji ma na Gaya maka.sanan wadanan munafikan daka saka a shago ban yarda dasu ba ka koresu Tijjani ya rike maka shagon.

"Umma Tijjani bazai iya rikemin shaguna uku ba ba yanda Zan Kori mutanen da suke samu a karkashina Zan dai bawa Tijjani jari ya rik'e kansa namiji ne shima ai ya kawo girman da zai Yi aure.

Safiya da Lami Kuma ya dace ace sun fito da mazajen aure Haka Dan wanan ba rayuwa Mai kyau suka zabawa kansu ba"

"Naseer a takaice dai kora da Hali kakeso kayi Mana toh bari kaji na fada maka babu Inda zamuje Kuma jari ba iya Tijjani zaka bawa ba har dasu lamin ka Gama duk abinda ka Dama Aurene sai kayi Dan ban Haifowa Naeema Kai ba yarinya duk tabi ta saka ka fice daga hayyacinka"

Naseer tashi yayi ya Shiga d'aki ita kuwa ta cigaba da bambamin fad'a kamar zata Ari baki.

Ahaka ya shirya ya zo ya fice daga gidan

Bai tsaya a koina ba sai a sharada lokacin Naeema tana daki tana bacci Inna zuwaira Kuma tana Dan Kara gyagyara gidan su Zahira kuwa Suna makaranta

Sai a gidan ya Rama baccin dake kansa yaci abinci ya huta sukayi ta Hira kamar basu da wani matsala yaso kwana sai da Naeema ta dage Masa Akan Kar ya kwana Dan Hajara na iya ganewa
Chapter 22 · 0% Book details