Sashe 145
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
su koma tunda hutu Yoohan ya ɗauka harna watanni biyu. Gaba ɗayansu su goma sha biyu ne har Aymah da Yoohan. Hakan yasa komai ya gudana cike da birgewa da nutsuwa. Sunsha shagalinsu na awa ɗaya da rabi sannan aka tashi. Su Richard dai tun anan sukaima Nu'aymah sallama. Dan da safe zasu wuce ba lallai ta gansu ba. Godiya itama ta musu, ta shigo tabar Yoohan na ƙarasa magana da su. Bayan su Dr Liam sun wuce, Osin ya shige masaukinsu wai zaiyi toilet🤧. Solomon ma dai tafiya yayi can nasa masaukin inda suka fara zama da Yoohan. Hakan ya bama Yoohan da Richard damar kasancewa su kaɗai. Maganace a bakin Rich sosai gameda firar papa da Dr Mateo da yaji, sai dai baisan ta yadda zai tunkari Yoohan ɗinba kai tsaye tunda Papa mahaifinsa ne. Ajiyar zuciya Yoohan dake ɗan nazarinsa yayi, “Rich kamar akwai magana a bakin nan naka tun kafin ka wuce kwanaki. Sai dai bansan miyasa ka gaza yiba. Duk da nasan dai bazai wuce akan komawata musulmi ba. Na yarda da kai Rich, dan baka taɓa cimin amana ba a tsahon shekaru goma sha shida da mukasan juna. Dan haka zan faɗa maka sirrin komawata mai salla a yanzu koda kuwa bazaka fahimceni ba”. Batare da ya jira amsar Richard ba ya shiga bashi labarin tun farkon haɗuwarsu da su Nu'aymah a ƙofar Orphanage. Fasa masa glass ɗin mota da tayi da tilasta musu shiga cikin Orphanage akan yaron da suka bige. Fara mu'amularsa da su baba malam har zuwa musulintarsa da aurensa da ita. Babu abinda Yoohan ya ɓoyema Rich. Sosai tsantsar mamaki da firgici ya bayyana ga Richard. Wani irin rauni da ƙwaɗayin shiga musulinci ya ringa kutse cikin ɓargon jikinsa da zuciya. Sai dai baice komaiba akan hakan sai magana akan ƙullin da akaima Aymah na maganar ciki. Ya janye hannunsa da ga dafe kan da yayi yana duban Yoohan da ke kallon wani waje da ban. “Ka yafemin Yoohan”. Juyowa Yoohan yayi yana dubansa. Cikin ɗan lumshe idanu yace, “Akan mi? Ni bakamin laifin komaiba ai”. “Niko na maka laifi X-man. Dan na zargeka akan abinda ba haka yake ba. Sannan na zargi in-lows ɗinka suma. Da ga yau na maka alƙawarin tayaka wannan yaƙin, zan taimakeka wajen cikama iyayenta alƙawarin daka ɗauka na bayyanar gaskiyar maganar cikin da suke zargin ta zubar”. Kallonsa Yoohan yake cike da so da ƙauna. Ya riƙo hannun Rich cikin nasa yana faɗin, “Nagode sosai Rich, kai ɗin na dabanne a gareni koda bakina bai furtaba”. “Ba nine na daban a garekaba Yoohan, kai ne na daban a gareni. Dan kamin abubuwa da yawa da ni kaina bansan hanyar da zan iya saka maka ba. Indai ni ɗin ɗan halak ne dolene na kasance a cikin yaƙin nan daka ɗauki alƙawarin yi. Sai dai zan baka shawara ɗaya zuwa biyu”. Numfashi Yoohan ya furzar da lumshe idanu ya buɗe akan Rich. “Ina jinka”. “Ka ajiye maganar ƙanƙantar matarka ka fara nuna mata ɗunbin soyayyar da kake mata. Waddama bata kaita shekaruba tana ɗaukar namiji balle ita dana fahimci tanada wayo sosai. Kaifa likitane, kasan sirrin mace duk da kuwa karatun likitancinka ba'a kansu kayisa ba. Amma na sanka da bincike, ta wannan hanyarne kawai kaima kanka zaka fahimci gaskiya ko akasin abinda Doctors ɗin suka faɗa a wancan karon, tare da naka gwajin, sai ka bita a sannu yanda kake buƙata.........” “Amma Rich.......” “Karkace komai Mr X. Wai shin kai baka tunanin shekarunka ƙaruwa suke ba raguwa ba? Ya kamata kasan sirrin dake cikin wannan tafiyar. Ko dai baka da lafiya ne Yoohan?”. Harararsa Yoohan ɗin yayi kawai ya kauda kansa. Rich ya kwashe da dariya yana faɗin, “Kai ɗinne kana abu kamar dutsi oga. Ga dama ka samu a hannu amma kana son kasa damawa. Idan da kace kana ƙyanƙyami da gudun matan waje wannan dai matarkace ai ko.......” “To naji mai shegen surutun tsiya. Muje shawara ta gaba”. Yoohan ya faɗa yana talle ƙeyar Rich. Shafa ƙeyar Rich yayi da faɗin, “Mugu, ashe dai kanaso. Shawara ta ta biyu itace karku koma Nigeria da ita yanzu har sai na binciko maka duk yanda komai ya kasance”. “Taya zaka binciko abinda baka saniba. Sannan wannan abun nasu yayi kama dana family, kai da ma ko sakin jiki ka kasayi da Uncle ɗin kanata faman jin haushinsa”. Murmushi Rich dake kallonsa ya keyi, a ransa kuwa yanason hana Yoohan komawa Nigeria da Aymah ne saboda abinda ya jiyo a wajen papa a wannan komawar da yayi gida. Saboda hirar papa da Dr Mateo ta kasa barin ransa tun wancan karon. A wannan zuwan koda suka koma dasu baba malam a abuja ya sauka shi. Anan ya ɗanbi diddigin papa shine ya sakejin kwangilar kashe Aymah da ya bada ayi masa saboda wai ya ganta a cctv ta shigar masa ɗaki. Duk da basusan mitayiba a ciki saboda cctv ɗin iyakarta parlornsa ne, (Tab, kenan randa Aymah taje ɗakin papa. Ya salam🤦🏻♀️) Abinda yasa suka gaza gane mitayi su basuga komai a hannuntaba. To amma shi papa ya tabbatar ta ga sirrinsa shiyyasa yake buƙatar a kauda masa ita kafin bakinta ya faɗama wani. duk da yana zargin ta faɗama baba malam, yaso kuma ƙyaleta yabi a hankali harya gano abinda tayo a ranar amma su Uncle Mike sukaita tunzurashi aka ya kasheta kawai, shine ya bama Dr Mateo kwangilar kasheta a wajen aiki batare da an zargesaba, dan Yoohan ya sanar masa a inda za'ai aikin da masu tayasa. shine aikin ya gagara kuma. Wannan abu da Richard yajine ya sakashi zaunar dasu G-boy akan su haɗa kuɗi su saka Yoohan zaman Honeymoon a Austria. Sai dai su basu san dalilinsa nayin hakanba dan bai fito fili ya faɗa musu ba........ Taɓashin da Yoohan yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa. Ya sauke numfashi, cikin son kauda tambayar mi yake tunani da Yoohan yay masa yace, “Yoohan ka bani dama. Zanyi bincike nane iyakar likitocin da suka gwadata. Sai kuma ƴar aikin da kace an kawo muku tunda kace ka saka mata abin ɗaukar magana a ɗakin da kuka ajiyeta”. “Okay Rich, sai dai banason ka saka kanka a haɗari Please”. “Karka damu kamin addu'a kawai. Kuma ai tare zamuyi aikin ma da kai”. Murmushi Yoohan ɗin yay masa suka rungume juna cike da so da ƙauna. Daga haka Rich ya korashi wai yaje madam na jiransa shima zaije yay video call da tashi dan gobe ma wajenta ya nufa, tare zasu wuce 9ja daga can..........✍🏻