← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 211

Sashe 65

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

..............Cike da jin haushin Yoohan Nu'aymah ta fito daga sashen hajjo. Hakan yayi dai-dai da shikuma Yoohan ɗin zai koma dan ya kammala wayar.
         Karo sukayi, goshin Nu'aymah ya bugu da sarƙar Cross ɗinsa. Da sauri tai baya saboda azaba. Shima bayan yaja kaɗan yana wani yamutsa fuska idonsa a kanta. Kasancewar Nu'aymah bata taka ɗan step ɗin ƙofar falon hajjon dai-dai ba lokacin da tai baya sai ta sake yo gaba zata faɗi.
           Yoohan ya tabbatar idan ya barta ta faɗi zataji mugun ciwo ne, dan haka da saurinsa kuwa ya tarota ta faɗo jikinsa. Sai kuma ta firgice saboda tsoratar da tai najinta kwance a ƙirjinsa, ta wage baki zata tsala ihu yay azamar ɗora lallausan tafin hannunsa saman bakin nata ya rufe ruf.
         Cikin tashin hankali Nu'aymah ta fara mutsu-mutsun kwatar kanta, jikinta sai rawa ya ke yi. Shikuma yaƙi sakinta dan ya tabbatar yana sakin nata faɗuwar daya gudar mata a farko sai tayi wadda ta fita a yanzu, cike dajin haushi ya daka mata tsawa, dan jiyayma kamar ya saketa ta faɗin ma yaga ƙarshen rashin kunya.
          Duk da tsawan da yay mata bata nutsuba, sai ma cigaba dayin mutsu-mutsunta nason ƙwacewa takeyi, tuni hawaye kuwa sun fara bimata kumatu, dan a rayuwarta da hankalin kanta kuma hakan bai taɓa faruwa da itaba. Ko hannu bata yarda samarin gidansu wani ya riƙe mata balle akai ga runguma irin haka. Sai gata yau kwance a ƙirjin ƙaton kahiri, da ko yayunta basu taɓa aikata haka a gareta ba. gashi ya rufe mata baki babu damar magana. Kuma ƙarfi ba ɗaya ba.........
       Jin ya manneta da bango sai tashin hankalinta ya ƙaru, dan ta zata wani abun kuma zai aikata mata, ta kasa nutsuwa ta fahimci taimakonta yayi. hannayenta duka biyu ta saka tare da dukan ƙarfinta tana ƙoƙarin ture masa hannunsa daya rufe mata baki da shi. Ko gezau baiyiba, saima wani shegen kallo da yake binta da shi tamkar ya manta a inda suke, ga fuskarsa a matuƙar ɗaure balle kai tunanin da biyu yay hakan, sai dai shima zuciyarsa wani irin harbawa take da sauri-sauri.
      “Ouch!!” ya faɗa da sauri yana janye hannunsa da ya toshe mata baki da shi, dan kuwa daddagewa tayi ta gasa masa cizo a tafin hannun. Yaja da baya yana yarfe hannun nasa da faɗin, “Are you mad?!”.
       Nu'aymah da har yanzu jikinta bai bar rawa ba ta galla masa harara tana share hawayenta. “Eh banda shi. ALLAH ya isana kuma, wlhy ka sake gigin taɓani saina fasa maka kai, danni ba ƴar iska baceba!”.
      “Silly girl! Waye ɗan iskan?” ya faɗa da turanci kamar yanda ta faɗa itama yana galla mata harara tare da cafkota, iya ƙarfinsa ya fisgota tayo baya ta sake faɗawa jikinsa. Mannata jikin bangon ya sakeyi, ya toshe mata baki da ɗayan hannunsa. kafin ya ɗago ɗayan hannun ya kalli inda ta cije sa, yamutse fuska yay ganin yanda shatin haƙoranta suka fito masa, ba wajen data ciza ɗin kawaiba, tafin hannun gaba ɗaya yayi jaa abinka da ba'asan wahala ba...
       Nu'aymah ta rikice iyakar rikicewa yanzun kam, dan ta yarda a ranta da gaske Yoohan son cutar da ita yake. Ƙilama abinda ya kawosa gidan kenan. Sake kaima ɗayan hannun cizo tayi. Yayi saurin janyewa ya maye gurbin hannun nasa da bakinsa. Shi kansa baisan yaya akai hakan ta faru ba, ya tsinci kansa ne kawai da haɗe bakin nasa da nata ya shiga kissing ɗinta.
       Yanda take kuka da turesa da yakushinsa ne ya sashi janyewa daga gareta da sauri. Duk da halin daya ganta na ƙololuwar shiga ruɗani da tashin hankali hakan bai hanashi kallonta ba, tare da zazzaro mata manyan idanunsa da suka sauya kala zuwa ja.
      Harga ALLAH Nu'aymah ta tsorata yau kam, dan ta tabbatar tunda har ya iya mata wannan abun a cikin gidansu to lallai zai mata duk abinda yazo masa rai. Tunda tasan su basu ɗauki keta mutuncin mace a komai ba. Amma tsabar ƙarfin hali irin na mutuniyar taku ana sakar mata baki sai ko ta murguɗa masa bakin da sake zuba masa harara. iya ƙarfinta ta turashi dan har yanzun yana manne da ita ne a bangon, amma ko gezau baiyiba balle tasa ran samun hanyar kuɓuta. Waige-waige take gudun kar wani ya fito ya gansu a haka, tana kuma hawaye, cike da tsiwa cikin harshen turancin data san yafi fahimta sosai tace,
        *_“Dama ku babu abinda kuka iya sai son taɓa mata da ɓata musu rayuwa, ALLAH ya isana ɗan iska kawai. shiyyasa wanda baya salla an haramta ma sa jin daɗin duniya. Sannan zai gamu da wahalhalu a wurare guda huɗu: A nan duniya, da ranar mutuwa, da cikin ƙabari da ranar hisabi. A duniya ana ɗebe ma sa albarka, a cire ma sa kwarjini daga fuska, a sa ma jama'a ƙyamar sa. A ranar mutuwa zai mutu da wulaƙanci da yunwa da ƙishirwa. A cikin kabari ALLAH zai ƙuntata ma sa, a hura ma sa wuta a cikin sa, a aika ma sa kumurci a tsakanin fatar jikinsa da namansa. A ranar hisabi za a baƙanta fuskarsa, a yi masa hisabi dalla-dalla, sannan a haɗa shi da zabaniyawa da za su wurga shi cikin wuta. Lallai, sallah ita ce ginshiƙin addini. Idan kaƙi gaskiya zaka faɗa ɓata. Idan ba ka ji nasiha ba, zaka yi da-na-sani. Wanda baiji bari ba ya ji hoho!......”_*
     Ta ƙare maganar da sake turashi da ƙarfi. Yanzun kam da kansa ma ya matsa ya bata hanya, da gudu tabar wajen kuwa tana kukanta har yanzun.
         Cike da takaicin kansa ya rumtse idanusa da ƙarfi, tare da ɗora hannunsa a goshi yana murzawa da abaton “Oh lord!, mina aikata?!”.

★★★★
Chapter 65 · 0% Book details