← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 211

Sashe 63

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

           Cike da farin ciki Abdallah ya faɗa saman gadonsa yana murmushi, insha ALLAH indai su baba malam suka amince zuwan nasu ya koma sai bikin su Kubrah yanada yaƙinin samun cikar burinsa. Dan babban fatansa shine shirinsa akan mallakar Nu'aymah ya tafi dai-dai, shima ranar ɗaurin auren su Kubrah a ɗaura nasa da masoyiyarsa, farin cikin rayuwarsa.
       Wayarsa ya jawo dake a gefensa, ya shiga ma'adanar hotunansa yana kallon hotunan da yaytama Aymah a wannan zuwan nasu batare da ita kanta tasan yana ɗaukarba. Ya jima yana kallon hotunan kafin barci yay awon gaba da shi a wajen
            Barcin nasa bai kai mintuna ashirin da ɗaukarsa ba Adawiya ta shigo gidan ita da maman Aaida. Ganin ɗakinsa a buɗe ya sakata nufar can tana faɗima maman Aaida, “Aminiya zauna ina zuwa, naga kamar Yah Ab yana gida ma”.
     Ɗan murmushi maman Aaida tayi da bata amsa cike da zolaya. “To adaibi a hankali azumi ake hajjaju”. Batare da Adawiya ta bata amsa ba ta shige tana dariya.

          Hajjo da dariyarsu ta sakata farkawa da ga ɗan barcin daya figeta itama ta fito dan taji ba muryar Adawiya bace kawai. “Baƙuwa mukayi a gidan?”. Ta faɗa lokacin da take fitowa falon. Maman Aaida dake latsa waya ta ɗago idanunta ta sauke akan Hajjo. Sai kuma tace, “Barka da fitowa hajiya”.
      Hajjo dake mata kallon sani tace, “Barka dai ƴar nan, gashi kuma kamar na sanki”.
     Da sauri maman Aaida ta zaro idanu waje da mamaki, sai kuma ta tuna maganar hajiya datai mata gargaɗi tun farko akan zuwa gidan, amma yau tsabar taurin kai sai gashi ta biyo Adawiya data dinga mata daɗin baki..........
      “To ko dai kamanni ne?”
Hajjo ta katse mata tunani. Da sauri maman Aaida tace, “Eh gaskiya hajiya inaga hakane, dan ni ƴar nance”. Cike da nazarinta Hajjo tace, “Oh to ALLAH sarki, kinsan idon tsufa ƴar nan. To barka da zuwa, halan ke ƙawar Adawiya ce?”.
      “Eh hajiya”. Maman Aaida ta bata amsa a ɗarare, dan tasha jinin jikinta da kallon ƙurulla da hajjon ke binta da shi...

         Ɓangaren Adawiya kam tana shiga ɗakin Yah Ab sai ta iske yana barci, ga wayarsa ajiye saman ƙirjinsa kamar wanda ya rungume mace. Harta juya zata fita, sai kuma zuciyarta ta ƙwaɗauta mata wani abu daban. Dawowa tayi da baya a hankali ta ɗauka wayar, kasancewar ta jima da sanin password ɗinsa sai batasha wani wahalar buɗewa ba. Gabanta yay bala'in faɗuwa saboda cin karo da hoton Nu'aymah da tayi, ta kafe hoton da idanunta da suka ciko da ƙwalla, sai kuma ta kalli Abdallah dake barcinsa hankali a kwance batare da yasan tanai ba. Harararsa tayi kamar idanunta zasu faɗo, mikuma ta tuna oho mata, saita ajiye wayar a inda ta ɗauka ta fito a ɗakin.
     Karo da taci da hajjo ta fito suna ɗan hira da maman Aaida yasata haɗiye damuwarta ta zauna tana gaisheta.

WASHE GARI

        Washe gari ya kama ranar salla, a kuma ranar Nu'aymah ta fito daga ittiqafi bayan sakkowa sallar idi. Duk da tayi ƴar rama sai gata ta ƙara haske saboda yanayin zafinsu da kuma zama cikin ac a koda yaushe. Tayi mamakin ganin Abdallah yazo ɗaukarta. Da farko taso taƙi binsa, amma ganin rana zatayi saboda yau zasu wuce sai ta haƙura ta bisa.
      Motar tayi shiru babu mai magana a cikinsu har suka isa ƙofar gidansa. Tana ƙoƙarin buɗe ƙofar yay saurin saka lock. Juyowa tai tana kallonsa fuska a ɗaure, shima sai ya ɗaure tasan, batare da ya kalleta ba yace, “Inason muyi magana da ke a yau”.
    Kamar bazata tanka masaba, sai kuma tace, “Yah Ab maganar mi? Dan ALLAH ka cire komai a ranka kamar yanda na cire nima, bana buƙatar wata sabuwar fitina dan girman ALLAH”.
        Cikin zafin rai yace, “Saboda kin samu wanda ya fini? Nu'aymah minai miki ne a rayuwa har kika zaɓi sakamin da waɗanan abubuwan? Mina rasa irin na sauran maza ne.....?”
      “Baka rasa komaiba Yah Ab, sai dai ka sani mu wannan itace ƙaddarar mu, UBANGIJI kuma shine yasan hikimar dake cikin yin hakan. ALLAH shine shaidata ban gujeka ba, ban kuma daina sonka ba. Sai dai wata katanga mai tsauri tariga da tayi gicci a tsakanin ƙaddarar mu. A ganina kuma babu amfanin maida yanda akayi domin bakin alƙalami ya riga da ya bushe.........”
        “Sai dai idan kece kika busar da shi Nu'aymah, idan har kin amince inason a wannan karon mu cika burinmu na mallakar juna, na yadda da kaifin wuƙar data datse zaren ƙaddarar mu a wancan karon, sai dai a yanzu na sake ɗaura ɗammarar ɗaure zaren domin mu zama abu guda kamar yanda mukai fata”.
     Murmushi mai ciwo Nu'aymah tayi, ta gyara zama tana fuskantar Yah Ab, cikin raunin murya tace, “Yah Ab, karka manta a yanzu kai ɗin mijin Adawiya da Yusrah ne, tayaya kake tunanin zan yarda ka sake ƙulle wancan zaren ƙaddarar da kaifin wuƙa ya datsa ta. A ganina muyi haƙuri kawai da yanda yau tazo garemu, domin kuwa jiyanmu ta wuce sai labari. Muyi haƙurin fuskantar gobenmu sai muzama masu cin riba. Wlhy Yah Ab bazan taɓa iya haɗa zaman kishi da Adawiya da Yusrah b.........”
     Da sauri ya saka hannu ya rufe mata baki, cikin matuƙar ɓacin rai yace, “Hakan ya zamemiki dole kuwa Nu'aymah, idan kuma kikace zakimin taurin kai, wlhy a yanzu sai kunbar ƙasarnan da Adawiya tare da takardar sakinta ɗai-ɗai har uku kuwa”. Yana gama faɗar haka ya cire lock ɗin motar tare da ficewa a fusace.
           Nu'aymah da tun farkon fara maganarsa akan su Adawiya ta ɗaura hannu a ƙirji da faɗin, “Na shiga uku ni Zainab! Yah Ab mi kake faɗi haka?”. Bai saurareta ba ya shige gida, da sauri itama ta buɗe motar ta fito ta bisa da ɗan gudu tamkar zata faɗi.

          Adawiya dake a ƙwance bayan motar tai saurin cire hannunta data toshe baki, dan daƙyar tai control ɗin kanta lokacin da Abdallah ya furta zai sakesu inhar Nu'aymah bata amince da buƙatarsa ba. Motar ta buɗe ta fito itama da sauri tana faɗin, ‘Tabɗi jan, ashe lokacin yin yaƙin duniya na uku ya gabato kenan, lallai yanzune za'a fara wasan na gaske wlhy’. Ta ƙare maganar hawaye masu zafi na gangarowa a kumatunta.
    Tun lokacin da taji Abdallah na sanarma Hajjo shine zaije ɗaukar Nu'aymah bayan an idar da sallar idi ta ƙudiri aniyar binsa a ɓoye. Dan haka kawai taji a ranta akwai manufa a zuwa ɗaukar, dan ta gama fahimtar take-taken Abdallah tun lokacin dasu Nu'aymah suka zo ƙasar. Shinefa ta lallaɓa taje ta shige motar ta ɓoye sannan ya samama hajjo inda zatayi sallar idi a massalacin, shi kuma batare dayin wani tunani ba yana zuwa yaja motar ya wuce. Kuma harya ɗakko Nu'aymah hankalinsa bai kai akan Adawiya dake lafe a ciki ba. wadda ko sallan idi ita batayi ba.

        Tana shigowa cikin gidan duk a falo ta iskesu har Nu'  Abdallahn. Duk suka bita da kallon mamaki dan sunta nemanta bayan idar da salla basu gantaba, shine Ahmad yace suyi tahowarsu tunda ita ɗin ƴar garice ai.
      “Ke kuma dama ba gidan kika dawo ba?”.
Abdallah ya faɗa cikin kaushin murya dan har yanzu ransa a ɓace yake. Kamar bazata tanka masa ba, dan ranta a bala'in cinkushe yake, ji take kamar ta burmama Nu'aymah wuƙa ta mutu kowama ya huta. Amma komi ta tuna oho mata, sai tai kalar tausayi tana haɗiye ƙududun daya tokare mata maƙoshi. “Eh na biya nan maƙwafta wajen Umm-Farukh, dama wasu kayane mukai da ita zan amsarma su Aymah to kuma ma dai anyi rashin sa'a basu isoba, dama daga Mexico ake kawo matasu”.
       Ɗauke kansa yay bai tanka ba, sai Ahmad ne da Hajjo sukai magana. Nu'aymah da tasha jinin jikinta akan yanda Adawiya ke magana ma bata tanka ba, sai dai a ƙasan ranta bata yarda da itaba sam.

★★★

      Duk yanda Abdallah yaso sake keɓewa da Nu'aymah dan su sake cimma matsaya akan zancensu taƙi basa dama har suka wuce Nigeria bayan awanni huɗu da sakkowa idi, dan kobi takan bikin sallar da ƴan saudia ke gudanarwa basuyi ba, dama Adawiya ƙin dafa komai tai saboda takaici. Abdallah zaiyi magana kuma Hajjo ta hanashi, acewarta su da zasu tafi yanzu mizasuyi da wani abincin salla bayan nasu nacan na jiransu a ƙasarsu.

      Sun sami ƙyaƙyƙyawar tarba kuwa daga su baba malam, dan ana sakkowa daga sallar juma'a (da yake ranar sallar ta kama juma'a ne) suka nufi airport domin tarbar mahaifiyarsu tamkar yanda suka saba. Babu kunya Nu'aymah taje ta rungume Baba malam, dan harga ALLAH tayi kewarsa shi da Umm da Muhammad. Kai dama ƴan gidan duka.
     Fuskar baba malam ɗauke da murmushi ya shafa kan ƴar tasa yana faɗin, “Ja'ira, duk ga iyayenku cike da wuri bakiga kowaba sai ni ko?”. Fuskar Nu'aymah washeda murmushi tace, “Abba nayi kewarka ne sosai, kuma ALLAH kullum sai nayi mafarkinka kai da Ummuna”.
     Baice da ita komaiba sai murmushi kawai daya sakeyi, dan shi mutum ne mai tsananin kawaici ga yaransa, yanama ƴan uwansa kara sosai. Dan haka suma a kullum suke ƙoƙarin koyi da ɗabi'unsa akan nasu ƴaƴan.
          Bayan Nu'aymah ta ƙarasa ta gaida sauran iyayenta uku suma cike da girmamawa. Suma suka amsa mata da tsananin kulawa sai suka runguɗa gaban mahaifiyarsu suna jera mata sannu da zuwa. Cike da kulawa da kewa take dubansu, fuskarta faɗaɗe da murmushi. Ta kama hannun Abba Musbahu tana faɗin, “Wayyo autana duk ka faɗa, ko azuminne?”.
     Dariya Nu'aymah da Ahmad sukayi, Malam ƙarami da Omar na tayasu kuwa. Hakama su baba malam sunata murmushin akan diramar autan nasu da mahaifiyarsu.
Chapter 63 · 0% Book details