Sashe 41
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Amma Yaya ka.......” hannu baba malam yay saurin ɗagama Abban su Adawiya dake son masa bayanin ainahin abinda ya faru. Ya kallesa fuskarsa babu wasa, “Banason jin komai akan hakan Mustapha. Kaje ka shirya mu wuce banason yazam mu ake jira”.
Kai kawai Abban su Adawiya ya kaɗa masa. Kafin ya kalli su Abba Musbahu ya bar wajan jiki a sanyaye. Da sauri su Abban Abdallah suka nufi mota da nufin bin bayan su Nu'aymah, sai kawai a bazata suka tsinkayi muryar Baba malam na faɗin, “Na haramtawa kowa bin bayanta a cikin gidan nan, idan kuma wani ya aikata koda ban saniba zai fuskanci fushina”.
Cak suka tsaya daga yunƙurin shiga motar, kowannensu goshinsa na tara zufa. Babu wanda ya iya sake cewa komai har Baba malam ya shiga sashensu ya fito cikin shirin fita. Ta gabansu ya wuce zuwa sashen Hajjo data sha maganin mura tun ɗazun ta kwanta. Duk wainar da ake toyawa bata saniba dan barci takeyi. Baifi mintuna biyarba sai gashi ya fito. Yanzunma bai kalli sashen da kowa yake ba ya nufi inda motar da zasu tafi take, sauran motocin uku da ɗalibansu zasu shiga da ƴan agaji kuma duk suna a harabar massallaci.
Suna kallo motar ta fice batare da ko mutum ɗaya ya iya cemasa a dawo lafiya ba, shima kuma bai nuna ya damu da hakan ko jiran cewar tasu ba.
Umm ce ta fara sulalewa ta koma ciki, kafin sauran suma su fara zare jiki ɗai-ɗai suna shigewa sashensu. Addah dai bayan Umm tabi tana share hawayen da ke sakko mata batare data farga da fitowarsu a cikin idanunta ba.
_____________
*_ABUJA_*
Tunda labarin kama Nu'aymah ya isa kunne Papa farin ciki ya mamayesa shi da Madam Chioma, breakfast da suke shirin zamanyi ma su kasawa sukayi, sai kai kawo sukeyi zuciyoyinsu fes kamar an basu rabin duniya.
Dolene yasa a koyama yarinyar hausawan nan hankali, dan shi a rayuwarsa idan da abinda yafi tsana a rayuwarsa to ƴan yankinta ne. Ya tsani yarenta fiye da mutuwarsa, a cewarsa babu abinda suka iya sai haihuwa, ƴaƴan nasu kuma babu tarbiyya sam, daga ƴan bangar siyasa sai masu bara. Sam mutanen da yankinsu basu masaba, inda ace zai iya zama shugaba, sai ya shafe yankin ko tarihinsu baza'a sake aji ba. (hummm Papa, a ringa sara dai ana duban bakin gatari).
Abinda papa ya keta faman rayawa a ransa kenan yana murmushi. Waya ya sake ɗagawa yay magana da d.p.o ɗin akan yanzunan a bama guards ɗin Nu'aymah su taho masa da ita Abuja. Shi kuma d.p.o ya turo da accaunt Number ɗinsa yanzu zaiji alert.
Cike da farin ciki d.p.o ya amsama papa. Babu ko tunanin komai a ransa ya aika da accaunt details nashi, ya kumayi zaman shirya takardar ƙarya akan laifin da bashi Nu'aymah ta aikataba.
(Humm! Ya ALLAH ka shiryemu ka shiryi shuwagabannin mu da jami'anmu. Ka tsame bara gurbin cikinmu, idan masu shiryuwane ka shiryesu. Idan bazasu shiryuba UBANGIJI kafimu sanin miya dace dasu, mun barka dasu😭🙏🏻).
________________
*_LAGOS_*
Fitowarsa kenan daga ɗakin theatre a matuƙar gajiye. yanda yake tafiya kawai zai baka wannan amsar. Tare yake da likitoci uku da suka tayasa aikin, sai Nurses suma guda uku. Dai-dai sun ƙaraso ƙofar wani office nurse ɗin dake a gefen damarsa ta miƙa masa tasar hannunta ya jefa hand gloves ɗin daya cire daga hannunsa ya jefa a ciki, hannu ya ɗaga musu kawai alamar su dakata anan ya tura ƙofar ya shige.
Basu damu ba, dan kowa yasan Dr Yoohan haka yake, mutum ne mai ƙoƙari akan aikinsa da himma, ga tausayi sosai musamman ga marasa ƙarfi. Bashi da yawan magana, sannan baida fara'a. Wanda bai fahimcesa ba zaita ɗauka kamar kullum shi cikin ƙuncin rayuwa yake, kokuma girman kaine bisa ga ɗaukakar da ALLAH ya basa. Idan kuma ka fahimcesa zaka gane cewa haka halayyarsa take, shi kawai aikinne a gabansa ba shiririta da shashanci ba. Akance likitoci mafiya yawansu sunada son mata, sai dai ga Dr Yoohan sam ba haka baneba. Duk yanda matan ke binsa da soyayya shi bama su ishesa kalloba, shi fa a rayuwarsa damuwarsa kawai shine aikinsa, sai ko family ɗinsa da taimakon marasa ƙarfi. Idan ya shiga cikin musulmi bazaka taɓa cewa shi ba musulmin bane, musamman daya ajiye ƙasunba da yanda yake gudanar da al'amuransa sak halayyar musulman ƙwarai. Sai dai fa idan kaci karoda sarƙar Cross a wuyansa da akoda yaushe baya fashin sakawa ne zaka gane daga ina ya fito. ALLAH ya ɗaukakashi a duniya a dalilin ƙwaƙwalwar aikin likitanci daya azurtashi da ita, likitane shi da kota wane fanni zai iya gunar da aikinsa akan mara lafiya, sai dai abinda ba'a rasaba kam, dan UBANGIJI shine mai komai da kowa.
Office ne daya amsa sunansa office. Bakajin komai sai sassanyan ƙamshin turarensa dana ac. Wanda ke zaune a rikunin kujeru uku dake can gefen office ɗin yana aiki ya miƙe yana masa barka da fitowa cike da kukawa.
Kansa ya ɗaga masa fuska a yamutse na alamar gajiya. kafin ya ƙarasa ga kujerar zamansa yaja wani file dake a jiye ya fara singing.
Tasowa Richard yay da sauri garesa yana murmushi, ya ajiye files ɗin hannunsa gaban Dr Yoohan ɗin yana faɗin, “Doctor akwai mutane biyu da zaka ganifa yanzun kafin ka tafi hutun awa uku da rabi, idan lokaci ya cika zaka sake shiga theatre room, na mutane biyu da suka rage suma”. Da sauri Yoohan ya ɗago yana kallon Richard fuska a marairaice kamar zai fasa kuka. Richard yay saurin haɗiye dariyar dake neman kufce masa dan yasan shima da gaske Yoohan ɗin ya kai iyakar gajiya, amma sai ya fiske yace, “Da gaske nake Yoohan, gama files nasu na kammala dubawa”.
“Rich.. Please, wlhy na gaji, sai dai kai ka dubasu” ya faɗa yana sauke numfashi da miƙewa ya nufi wata ƙofa.
Murmushi Richard yayi yana binsa da kallo harya shige. Ya ɗan girgiza kansa da kwasar files ɗin ya fice daga office ɗin zuwa nashi shima.
ALLAH ne ya haɗashi da Yoohan tun a secondary school, a farkon haɗuwarsu sam basa shiri, dan abokan faɗan junane a aji. Ba komai yasa rashin jituwa tsakaninsu ba sai kasancewar su duka sunada matuƙar ƙoƙari, kafin Yoohan yazo school ɗin shike ɗaukar na ɗaya a ajinsu, amma Yoohan na zuwa ya amshe wannan matsayin. Kafin zuwan Yoohan ɗin kuma kowa sonsa da girmamasa yake a ajin, hasalima shine Monitor, ƴammatan ajin ji suke tamkar su haɗiyesa kuma. Amma Yoohan na zuwa nanma komai ya canja, kan ƴan ajin ya rabu biyu, wasu na ɓangaren Yoohan wasu Richard. Dan haka aka zama abokan dabin juna, duk da sam Yoohan baya kula duk haukarsu. Rashin kulawar Yoohan ɗin tasa a koda yaushe shi da tawagarsa suke ɗauka Yoohan matsoracine, dan babu wanda ya taɓa ganin faɗansa. Sai fa wataran da suka kaishi bango yayma Rich dukan mutuwa, da ƙyar aka karɓesa a hannunsa dan Yoohan akwai zuciyar tsiya. Tun daga wannan duka da Yoohan ya masa suka koma abokan juna, tun sauran ɗalibai na ƙalubalantar abotar tasu har suka fahimci ta gaskiyace suma sukabi. Shi da Yoohan duk burinsu ɗaya ne akan karatu, dan haka haɗewarsu waje guda ta ƙara musu himma da ƙwazo. Koda suka kammala secondary kuma cikin amincin ALLAH iyayensu suka amince musu tafiya karatu tare. A gaba ɗaya rayuwarsu tare ta gudana, sai daga bayane Yoohan daya cigaba da wasu kwasakwasai (Courses) ne suka ɗan rabu, danshi ya amshi aikin da aka bashine a ƙasar London bayan zamowarsu cikakkun likitoci, saɓanin Yoohan daya ƙi amincewa.
Daga baya Yoohan ya kuma samun ɗaukaka fiye da tashi, danshi ya ƙara faɗaɗa wasu karance-karancen daya bashi damar iya duba marasa lafiya ta kowane fanni, aikinsa ya zam zai iya yinsa a kowacce ƙasa kuma.
Bayan shekara ɗaya da fara wannan gwagwarmayar Yoohan ya fahimci bazai iya shi kaɗaiba sai da taimakon Richard, dan haka yaje ya dabaibayesa da daɗin baki har saida ya amince suka sake curewa waje guda suke gudanar da aikin a tare. Yanzu haka shekararsu ta biyu kenan da fara aiki, suna ɗaya daga cikin manyan matasan likitoci da duniya ke alfahari dasu bama ƙasarsu ko yankin Africa kawai ba.
A yanzu haka dai shi Richard ana shirin aurensa ma da wata baturiya, shiko Yoohan yaƙi motsawa sam, a cewarsa shi bama zaiyi aure yanzuba sai nan da wasu shekarun daya tsara.