← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 211

Sashe 160

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

        Suna isowa wanka Aymah ta shiga. Sai faman complain take wai ƙafafunta na ciwo.  Baice mata komaiba shi dai tunda itace ta ja musu shan wahalar ai. Amma da yake ta fisa baki shine take cewa shine.
    Wanka tayo ta fito tana ɗingisa ƙafa wai ciwo take mata. Da kallo kawai ya bita shi dai, ya ɗan girgiza kansa yana miƙewa da faɗin, Silly girl maganinki kenan ai”.
       Juyowa tai tana hararsa. Sai dai shi baimasan tanayi ba dan tuni ya shige toilet ɗin abinsa. Koda ya fito ya iske har tayi shirin barci. Sai dai bata kwanta ba. Tana kwance a sofa tana kallo. Shirin barcin shima yayi. Yana kammalawa wayarsa tai Ring. Miƙewa tai zata kawo masa sai taga ya nufota. Hakan yasa ta koma ta zauna harya ƙaraso. Yana amsa yaga Rich ne, sai ya maida kallonsa gareta. “Please sa hijjab muje mu ƙarasa maganarnan yana jiranmu”.
      “Okay” ta faɗa tana miƙewa. Ta ɗauki hijjabin sallarta ta saka tare da zura Slippers suka fito harabar hotel ɗin wajen swimming pool ɗin nan da mutane keta shanawarsu tamkar rana. Daga can gefen garden ɗin hotel ɗin suka koma. dan shima dai mutane ne keta hidimarsu. Aymah ta fahimci mutanen nan sam basa banbance dare da rana halan. Dan koda yaushe su dai hidimarsu suke hankali a kwance.
       Zama sukai inda suka iske Richard. Ta gaishesa da ƴar sakewa fiye da ko yaushe. Shima fuskarsa da murmushi ya amsa mata harda tsokanar wai ta ƙwace masa aboki.
      Murmushi tayi kawai batare datace komaiba. Shi dama Yoohan bai saka bakinsa ba, sai dai ya bama Rich ɗin hannu sun gaisa.
      Bayan an kawo musu Coffee ɗin da yay musu order itama Aymah aka kawo mata lipton data buƙata sai suka fara tattaunawa akan yanda zasu ɓulloma lamarin. Suna gamawa da maganar gidansu Aymah Rich ya turama Joseph saƙo akan ya janye masa hankalin Yoohan.
     Haka kuwa akayi, ko mintuna biyu da tura saƙon ba'ayiba kira ya shigo wayar Yoohan. Ɗagawa yay suka gaisa da Joseph batare da ya tashi ba. Sai daga baya kuma ya miƙe saboda magana da Joseph ɗin yace yanason suyi.
           Yana barin wajen Rich ya kalli Aymah data ɗauke kanta daga garesu tana kallon wata mata da yaranta twins da babansu dake gefensu. Sai soyayyarsu suke zubawa da tattalin ƴan yaran nasu. jitai sun bata sha'awa sosai har tana kwatanta kanta da Yoohan ace yaran nasune wai (ƴar baba malam an fara hankali kenan🤣).
      Gyaran murya da Rich yayine ya sakata juyiwa taɗan kallesa. murmushi yayi shima dan haka kawai yay zargin abinda take tunani akan mata da mijin da yaransu.
       “Inason muyi magana Please, sai dai tsakanina da ke ne banason Yoohan ya sani”.
      Cike da mamaki ta tsura masa idanun tana tsuke fuska. Saurin girgiza mata kai yayi yana murmushi. “Am sorry sister akan gidansu ne karki zargi komai”.
      Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye da ɗan shafa gefen wuyanta alamun taji kunya. Shima sai ya ƙara murmusawa dan ta birgesa. Hakan na nufin a duk inda take zata karema ɗan uwansa mutuncinsa. Wayarsa ya miƙa mata tare da miƙewa yabar wajen. Can ya koma inda Yoohan ke zaune yana waya dan ya fahimci shima hankalinsa na kansu.
      Binsa da kallo Nu'aymah tayi. sai kuma ta buɗe video ɗin data gani akan wayar, da alama shi Rich ɗin ke buƙatar ta gani. Ba ƙaramin bugawa ƙirjinta yayi ba, saboda cinkaro da kanta a ranar data shiga ɗakin papa ta ɗakko hoto. Sai dai iya falone. har shigowar Papa da Andrew falon. Shigarsa bedroom ɗin da fitowarsa da sake komawarsa. Harma fitarta da kayan harƙallar papa da suke magana akai shi da Andrew. Cocaine ce da wasu ƙwayoyi, sai abinda ke cikin ɗayar jikkar dai bai buɗeba, hakan yasa batasan minene ba. Hannu tasa ta sharce zufar data tarar mata a goshi. Ta ƙara playing ɗayan video ɗin dake a ƙasan wancan shima. Shi kuma papa ne da wasu mutane yana bada kwangilar a kasheta duk sanda suka dawo Nigeria. Randa aka kashetan kuma a kashe baba malam shima. ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ ta shiga maimaitawa tana kallon inda Yoohan da Rich suke zaune. Ganin Rich nata jan ra'ayinsa ga barin kallontane ya sakata kauda kanta tana taunar lip ɗinta. A ranta kuwa sake jinjina lamarin papa take da jin tsanarsa a ranta. Lallai saita tona dukkan sauran sirrin mutumin nan duk da kasancewarsa mahaifin mijinta. To amma shi wannan Richard ɗin mi yake nufi da bata video ɗin ta gani?.
     Kafin ta nemo amsar tambayarta taga sun miƙe sun nufota. Fita tai daga cikin folder ɗin da sauri ta ajiye masa wayarsa da ƙoƙarin control ɗin kanta dan kar Yoohan ya gane.
        Rungumeta Yoohan yayi cike da tsantsar farin ciki yana faɗin, “Oh my Sweetheart ke haske ce a rayuwarmu. Rich yace yanason zama musulmi”.
       Cike da razana Aymah tace, “What?!!”. Sakinta Yoohan ɗin yayi yana dariyar farin ciki da jinjina mata kansa. kafin yace wani abu Rich yace, “Tabbas abinda X-man ya faɗa ashine gaskiya Sister. Zama da mahaifinki ya ƙwaɗaitamin son kasancewa musulmi. Hakan ya ƙara tasiri ne a raina a ɗazun dana ganku kuna salla abin ya birgeni”.
      Kallonsa kawai Nu'aymah take cike da tuhuma. Dan gani take wani ƙullinne kuma yake shirin musu ta hanyar shiga musilinci.
     Fahimtar hakan da yayine ya sakashi girgiza mata kai idanunsa na kawo ruwan ƙwalla. “Na rantse da ALLAH ni Richard inason shiga musilinci ne da zuciya ɗaya bada wani daliliba. Ki yarda ke haske ce a garemu kamar yanda mijinki ya faɗa”.
        Numfashi Aymah ta sauke tare da furzar da iska ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata a hankali. Sai kawai ta faɗa jikin Yoohan ta rungumesa tare da rushewa da kuka. “I love you so much Yah Yoohan”. Ta faɗa a bazata tana ƙanƙamesa da ƙyau.
       Da sauri Yoohan ya ɗagota yana kallon fuskarta. “Cikin rawar muryar zuwan bazatan maganar yace, “Really? Please sake faɗa naji dan ALLAH”.
       “Babu ƙarya ko yaudara a maganata. Da gaske ina SONKA Yah Yoohan. Na rantse da ALLAH ina sonka da gaba ɗaya zuciyata”. Ta kuma rungumesa.
      Ai gaba ɗaya yama manta da wani Rich dake wajen. cikin sauri yaja hijjab ɗin jikinta ya shige ciki tare da zame mata fuskarta itama ta koma ciki. lalubar bakinta yayi ya manne da nashi. Duk da kunya da tsoron abinda ya faru dake cikin ranta hakan bai hanata tayasa abinda yakeyiba batare da tasan ta zurma ba.
        Dariya Rich ya sanya musu tare da miƙewa yabar wajen, can inda suka baro da Yoohan ya koma ya zauna yana kallon wani wajen daban, zuciyarsa fal da wani irin farin ciki da shi kansa baisan na minene ba.
Chapter 160 · 0% Book details