← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 211

Sashe 114

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Tun daga bakin ƙofar sashesa take ƙarema gidan kallo, babu ƙarya gidan ya haɗu, musamman idan kana sama kake kallon tsarin falon ƙasa. Hakama idan kana a ƙasa kake kallon upstairs ɗin. Ga koma tsaf babu wani datti alamar dai ana kula da tsaftar gidan yanda ya kamata. A yanzu haka ma'aikatan gidan daketa shara da goge-gogen yamma sai risinawa suke suna gaishesu. Shi kaɗai yake amsawa. Ita kam binsu kawai take da kallo da takaicin ganinsu ƙattan maza.
            Ta saman upstairs ɗin suka nufi sashen Momy dake jikin na papa. Corridor ne mai ɗan faɗi da ƙofofi uku a cikinsa. saɓanin Nasu da zaka iske falo. Knocking ɗin ƙofar tsakkiya yayi. Daga ciki wata murya ta amsa. Juyowa yay ya ɗan kalleta sannan ya tura ƙofar. Ita dai biye take da shi. Yanda taji yace, “Excuse me” itama Excuse me ɗin tace a hankali. 
       Murmushi madam Chioma dake waya da ƙawarta tana bata wasu dabaru ta saki saboda ganin rabin ranta. A yau ɗin nan duk da zafin zazzaɓin nan da takeji sai taji a ranta garama da take yinsa. Dan koba komai a dalilin zazzaɓin ta samu kusanci da lokacin yaronta mai tsaho tare da ita. A gaba ɗaya yinin yau sai zirga-zirga ya keyi a kanta da son ganin jikinta ya dai-daita. Ɗazuma da taita langare masa yafi awa biyu zaune tare da ita.
       A hankali kuma sai fara'ar fuskar tata ta fara gushewa saboda ganin abinda ke a bayansa.......
       “Masha ALLAH Mom sauƙi yazo sosai” ya faɗa yana zama a gefen gadon nesa da ita kaɗan batare da ya lura da canjawar fuskar tata ba. Nu'aymah kam dake mata kallon ƙasan ido taga komai da madam Chioma tayi, murmushin farko da canja fuskarta da tai saboda ganinta. Dai-dai Aymah na zama bisa sofa ɗin ɗakinne Momy ke bama Yoohan amsar maganarsa. “Ƙarfin haline kawai my boy, dan dana tashi ma kamar zan kiraka kazo ka sake dubani sai nayi tunanin ko baka a gidan ne?”.
      Ɗan murmushi kawai yayi batare da yace komai ba, saboda gaisheta da Nu'aymah keyi. Shiru tayi kamar bazata amsaba, ita kuma Aymah daga gaisuwar nan guda ɗaya bata sake wata ba.
     “Mom tana gaisheki fa”. Ya faɗa yana kallonta. Daburcewa ta nema yi, dan batai zaton zai saka baki ba. Cikin kame-kame tace, “Oh Daughter Am sorry, hankalina nakan Son, kina lafiya?”. Cike da mamakinta Aymah tace, “Alhmdllh” daga haka taja bakinta tai tsit fuska babu walwala. Itama Madam Chioma bata sake bi takan Nu'aymah ba. Gaba ɗaya hankalinta naga Yoohan. Sai takalarsa da zance take yaƙi magana ƙwaƙwƙwara, daga guntun murmushi sai um sai a'a. Ita Aymah ma abin dariya yaso bata. A ranta sai gulmar ɗan da uwar takeyi tana kwasar dariya. A fili kuwa fuskarta babu ko ɗigon walwala a cikinta. Ta tsume abinta kamar tama manta da su a ɗakin.
             Sosai Yoohan yake lure da ita, amma idan ba shiba bazaka taɓa fahimtar hankalinsa na gareta ba. Agogon hannunsa ya kalla yana faɗin, “Momy bara muje ta gaida Papa nasan ya shigo yanzun”.
        “A to muje sai na rakaku ai” ta faɗa tana miƙewa. Da sauri Yoohan yace, “Haba Momy, keda ke fama da kanki”. “Karka damu ai da sauƙi” ta faɗa tana bin bayan Aymah da tunda ya ambaci tafiyar har ta kai ƙofa. Bayansu kawai yabi yana mamakin halin Momynsa.

        Koda suka fito Aymah tsayawa tai baya suka wuce gaba tunda sune ƴan gida. Sun shiga sashen papa dake da falo babba, dan har yafi nasu girma ma. bata cuci kanta ba, koda suka zauna sai da ta ƙarema kowace kusurwa ta falon kallo lokacin Momy ta shige bedroom ɗin papa dan basu sami kowa a falon ba. Yoohan kuma yanata latsa waya. 
         Lokacin da suka shigo shima papan ta ƙasan ido ta gama ƙare masa kallo tsaf. Shima ƙyaƙyƙyawa ne kuma fari, dan suna kama da Yoohan, sai dai Yoohan ya fisa ƙyau da ƙwarjini da ƙuruciya. Da alama dai Yoohan ɗin ya kwaso kamannin wanu bayan shi. Papa na zama Aymah ta zamo ƙasa ta zauna. Ba Yoohan ba har Madam Chioma hakan da Nu'aymah tayi ya bata mamaki. A ranta kuwa ayyanawa take, ‘Wato ni wannan ƴar shilar yarinyar ta raina kenan?, ina zaune sama tana zaune itama a ɗakina’.
       Maganar papa ce ta katse madam Chioma. Cikin fara'a sosai yake amsa gaisuwar da Aymah ke masa, harda haɗawa da ƴar tsokanarta. Itako tanata zuba murmushi kanta a ƙasa. Tambayoyi ya rinƙa mata dake nuna kulawarsa a gareta. Hakan ne ya sakata ɗan sakin jiki da shi tana bashi amsar da duk ya buƙata.
     Shi dai Yoohan ma abin sai ya bashi mamaki, dan koshi bata sakin jiki da shi kamar hakan. Papa daketa murmushin jin daɗin yanda Aymah ta saki jikinta da shi ya dubi Momy yana faɗin, “Darling a tattaro min duk members na gidan nan da masu aiki, zan gabatar musu da daughter in-low ɗina. Itama na gabatar mata da su.
         Cikin ɗan yatsine fuska madam Chioma ta miƙa hannu ga wayar landline dake a table ɗin jikin kujerar da suke zaune ita da papan ta hau danne-danne. Kira tayi, bayan an ɗauka daga can tace, “Joy, ki sanarma kowa na gidan nan yazo Master parlor yanzun nan”.
        “Okay maa!”
Joy ta amsa daga can tana ajiye wayar.

       Cikin mintuna ƙalilan kowa ya shigo falon, hatta da maigadi bai zaunaba, kulle gate ɗin yayi ya taho. Shi dai Yoohan kamarma baya cikin falon. Babu wanda ya damu da shariyar tasa tunda sunsan halinsa kenan. Victoria ce ma uwar surutu taje jikinsa zata zauna ya harareta. Da sauri ta canja mazauni tana tura baki gaba na shagwaɓa.
       Sai da kowa ya nutsu sannan papa ya fara magana. “Na taraku anan ne domin na sake tabbatar muku da ƙaruwar member da family ɗinmu ya samu duk da nasan kun sani. Karku ganta ƴar ƙarama kuce zaku ɗauketa ƙasa da ku, har wani raini ko abu mara ƙyau ya faru a tsakaninku. Duk wanda ya aikata hakan zan saɓa masa da saɓawa mafi ciwo. Dolene kowa na gidannan idan ka cire su mama da Darling dake matsayin kakanni a gareta da Uwa kowa ya bata girmanta. Saboda mata ce ita a wajen John, kowa kuma yasan a gidan nan bayan ni John shine uba, dan shine babban ɗana abin alfaharina. Sunanta Zainab, amma ana kiranta Ayimah. My daughter ko ba haka bane?” ya ƙare maganar yana kallonta. Murmushi Aymah tayi, batare data ɗagoba ta gyara masa da cewar, “Nu'aymah”.
       Sake maimaitawa yayi duk da dai yanzunma bai faɗa dai-dai ba. “Nasan dai baku manta da sharaɗin John ba. Zainab ɗago kanki zan nuna miki kowa da sunansa anan kema”.
     Babu musu kuwa ta ɗago, dan ganinsu cike da falon baisa taji ko ɗarba a ranta saboda tun fil azal ita ALLAH yayita mutum mara tsoro. “Wannan itace mamana sunanta Mama debora. Itace ta haifeni tare da ƙannena. Maza mu uku, mata su biyu. Gasu nan”  ya nuna ƙannensa biyu mata dake zaune a wajen. Maman Favour, da maman Destiny. “Akwai maza biyu suma zan nuna miki su idan sunzo. Sai wannan itace Maman Darling. Momyn John kenan gata nan” ya nuna madam Chioma da mamanta. Daga haka ya dawo kansu Joy, Gebrail, Abraham, Victoria ƙannen Yoohan kenan. Sai Miracle ɗiyan ɗan uwansa Uncle Mike. Sai Aunty Blessing kuku, daga haka ya koma kansu Solomon daki-daki da ayyukansu a gidan duk ya sanar mata har zuwa kan maigadi.
      Cikin murmushi tace, “Nayi murnar haɗuwa da ku duka”.
        A tare suma duk suka amsa mata da hakan, duk da dai da yawansu ba har cikin zuciya bane ba. Sun faɗane kawai saboda tsoron Yoohan da duk abinda sukeyi yayi kamar baya falon.

       Sallamar ma'aikatan gidan ya farayi, kafin ya sake duban family nasa ya shiga musu nasihar zaman lafiya (Su papa kenan😂lol). Daga haka ya sallami su Miracle ma daketa antayama Aymah harara ta ƙasan ido ita da joy. ya rage daga shi sai su mama debora da su maman Destiny. A gabansu ya fiddo keys ɗin mota guda biyu ya miƙama Nu'aymah ɗaya.
      “Dota wannan shine wedding gift ɗinki daga ni. Kai ma John ga naka. ALLAH ya sanya muku albarka a cikin aurenku”. Da hannu biyu Aymah ta amsa bayan taje gabansa ta durƙusa. Tai masa godiya sosai. A ranta kuma tana addu'ar ALLAH ya shiryesa idan yana da rabo, idan baida kuma ALLAH yay maganinsa. Shima oga Yoohan ya amshi nasa. Tare da rungume papansa yana mai nuna masa jin daɗinsa da waɗannan ƙyaututtuka shi da matarsa. Buɗe masa hannaye madam Chioma tayi wai itama ya bata hug.... Kafaɗa ya maƙale mata yana faɗin, “Sai kin bamu naki gift ɗin sannan”.
       Kusan a tare duk falon akai dariya. Banda Aymah da sam abin ita bai birgeta ba. Dan haka kawai madam Chioma duk da mahaifiyar mijin nata ce batai mataba ko kaɗan. Su mama debora ma duk sun bama Yoohan ƙyauta, amma basu bama Aymah ba. Ko a jikinta ita kam, dama bata buƙata. Ganinma lokacin salla yayi saita miƙe tana faɗin ita zataje tai salla lokaci yayi.
        Papa ne kawai ya amsa mata. Sai Yoohan da ya bita da kallo saboda ganin yanda tai maganar kanta tsaye babu wani inda-inda a ciki. Harga ALLAH ta birgesa, dan da watace sai tai ta nuku-nuƙu musamman data san su ɗin sun rinjayeta a gidan.
       Ko kallon inda yake bataiba tai ficewarta, dan tasan zata gane hanya abinta. Acan downstairs ta hango su Miracle sun baje suna kallo, ta girgiza kai da taɓe baki tana faɗin, ‘ALLAH ka rabamu da gafalalliyar rayuwa dai’.
       Sai da ta tsaya a falon ta gamai masa kallon tsaf tana jinjina yanda ya haɗu, da jin ƙaunar iyayenta. Ganin zata makara salla ta nufi hanyar bedroom. Tana buɗe ƙofar zata shiga aka buɗe ta falon. Kallon inda ƙofar take tayi, ganin shine ya sakata ƙarasa shigewa batare data nuna alamar tasan da shigowar tasa ba. A fili ta furta, ‘Ai nazata tuban mazuru kayi, bazaka taso kayi sallan ba’.
         Oho, shidai baisan tanayi ba. Dan ɗakinsa shima ya shige kai tsaye dan gabatar da sallar, tunda an ja masa makara bai tafi massallaci ba.

________★★★★________
Chapter 114 · 0% Book details