← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 86

Sashe 86

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ƙaramin hauka ta yi duk da ta san A.m zai cika mata alƙawarin da ya ɗaukar mata,amma ta ji kishin ta matuƙar gaske kamar ta je ta kashe ta,amma babu yadda za ta yi saboda ta san cewa ta yi sakaci sosai.

A ƙalla sai da ta yi sati ɗaya a asibitin sannan ta warware ta samu lafiya sosai.

Yara sun ci sunan kakannin su wato Dadddy da Abbu,wayyo Allah zo ka ga murna gurin takwaran Hassan wani irin gata ya nuna musu na ban mamaki.

Momi ta ce a kai Juwairiya gidanta har ta gama wanka,daga nan sai ayi taron suna da shagalin bikinta da ba su san da auren ba,amma A.m ya nuna ina sam hakan ba zai yu ba domin ba zai iya kwana ba tare da yaransa ba,sai dai in za ta ba shi gurin kwana to ya yarda,daga ƙarshe Momi aka ce ta je ta kula da ita,ƙila ya manta yana da wata matar da zai tare a gidan,saboda ta lura yarda take zumuɗin yaran babu abin da ba zai iya ba.

A.m da ya ɗaukar wa kan sa alƙawarin in har mai asibitin ya dawo sai ya yi masa nasiha,akan ya kula da asibitinsa don ranar gobe kiyama sai Allah ya tamabaye shi akan yadda yake sakaci da rayuwar al.umma.

Sai dai ya kama bakinsa ya tsuƙe saboda ganin sa da ya yi,zai iya cewa tun da ya ke bai taɓa ganin mutum mai ɗagawa da girman kai irin sa,duk da cewa shi ma ya san yana da na sa,amma doctor Garkuwa ya dame shi ya shanye,yana kallon mutum kamar kashi wanda sam A.m bai fahimci haka halintar idanunsa take ba,shi a bin da ya ƙara ba shi haushi da shi zuwa da gajeren wando da yake yi a asibitin,wanda ya fahimci dabi'ar sa ne,saboda ya ji ƴan asibitin suna gulmar sa ko waje zai fita da gajeren wando yake fita,kamar zai tsallake wuta.Sai dai kuma matashi ne mai kyau da kuɗi da aji ɗan kwallo wanda sunan sa ya zagaye nahiyar duniya.

Sau ɗaya Zainab ta danne zuciyarta ta je asibitin sai dai ta sha kuka,ta yi alƙawarin ba zata ƙara zuwa ba,saboda abubuwan da ta gani yadda suke ji da ita,don Hajiya Binta take mata wanka,Momi kuwa kullum tana asibitin .

Ta sha kuka ta bari a sallamota su yi ta taƙare da A.m ya karɓi yaran ita za ta shayar da su ya sallami Juwairiya don zuciyarta za ta buga,wataƙila kuma ta amshi ta yi da Momi take mata,saboda ba za ta iya barin sa da ita ba na har abada,duk da ta san ko yau ta bar gidan ta fita na har abada ganin yadda danginsa suke nan-nan da ita kamar za su lashe ta don so.

Wani irin so yake nuna musu na fitar hankali don a yarda yake ji da su ko kan sa ba ya ƙauna haka.

Hajiya Binta ta hana shi sakewa da Juwairiya, saboda tun da ta haihu ta canza mi shi babu tsiwa,sai shiru-shiru sai kuma hawaye da take yawan zubarwa in har ya yi mata magana,wanda hankalinsa yana tashi matuƙar gaske,ya yi mata tambayar duniya ba za ta amsa mi shi ba,gabaki ɗaya ta canza mi shi kamar wata kurma,wanda hakan yake ɗaga hankalinsa matuƙa.

Zainab ta raina kanta ta muzanta tun tana mamakin halin da yake mata, har ta daina tana kallonsa kawai don ta fahimci shi bai É—auke shi wani abu ba.

Ko kwance suke haka zai É—auki hoton su ya yi ta kallo yana dariya kamar mahaukaci,in har tana son ya yi mata magana to ta ce ai Hasan ya buÉ—e ido ka ya yi kaza,sai ya saki baki ya yi ta zuba yana hira,gabaki É—aya bai da lokacin ta sai na yaransa.

Duk da cewar Hajiya Binta tana mi shi faÉ—a amma bai san lokacin da yake aikata hakan ba,shi dai ya san yana musu son mutuwa.
Kwance suke Zainab tana gefen sa da kofi a hannunta tana shan tea,domin ya É—umama mata jiki,kasancewar lokacin sanyi ne.

A.m da waya a hannunsa yana ta kallon video na yaransa da ya yi musu,yau kwanan su sha takwas.

Dariya yake sosai yana kallon Husain da yake buɗe ido sai ya rufe da sauri ya ƙuma ƙara buɗe wa.

Zainab ta miƙe cikin fushi ta fisge wayar da take hannunsa ta kwaɗa ta da ƙasa ta tarwatse.

Hannu ya ɗaga da sauri zai mare ta ko mai ya tuna ya fasa ya dunƙule hannun sa ya saki.

" A she ba ki da mutunci kishi kike da yarana Zainab?"

Kawai sai ta fashe da kuka ta ce." Na gaji A.m zuciyata gab take da ta buga! Ka san yarda nake son ka kuwa?Ka dai na kula ni ba ka da lokacina kullum sai na yaranka ba dole na yi kishin su.Ka sani ko da yaran nan sun dawo gurina ka ce haka za ka rinƙa yi musu,wallahi ba zan lamu ta b..."

" Ya she ki kar ki kawo mini maganar banza! Idan yaran ki ne za ki furta hakan,in har kika ce za ki yi kishi da yaran da na haifa to kin saka ma kan ki wahala,don ina son yarana fiye da komai Shekaru nawa na É—auka ba tare da na samu magaji ba."Ya katseta da faÉ—in haka.

" Zan yi kishi da su har ƙarshen rayuwata in har haka za ka rinƙa yi musu,sannan Juwairiya ta haihu don haka ka cika mini alƙawarin da ka ɗauka."

Kallonta ya yi sheƙeƙe ya ce."Sai ta gama wanka zan tara ku na yanke duk abin da na zartar."Ya faɗa a ɗaure ya ɗauki wayarsa ya koma ya kwanta.

" Ai ko wallahi ka ɗauko ma kan ka tashin hankali matuƙar ka ce ba zaka rabu da ita ba,domin ba zan zauna ku kashe ni a gidan nan ba,son da nake maka ba zai bar ni na iya barin mata kai ba.Bari na gaya maka ka ji ina sonka in har kace za ka haɗa ni da wata zan ɗauki mataki sosai kuma na bi duk yadda zan yi na rabaku ban damu da girman zunubin da zan ɗauka ba,domin zuciyata ba za ta iya bar ma wata mace kai ba,don haka kashedi nake maka da kakkausar murya!"Ta fice daga ɗakin da gudu tana kuka.

TO MASU KARATU KU DAI BIYO NI KU JI YADDA ZA TA KAYA A TSAKANIN SU YAU BAN YI TYPIND DA YAWA BA,SABODA BA NA JIN DAƊI KU YI HAƘURI DA WANNAN ANA TARE.

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY

TALLAH!TALLAH!!TALLAH!!!

INA ƳAN MATA DA MATAN AUREN DA SUKA SHAYAR SUKE SON MARTAR ƘIRJIN SU YA DAWO?

INA MATAN DA SUKE FAMA DA RASHIN ƘIBA KO INA A ƘAME?

MAZA GARZAYO KI SIYA INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO DA ƘIBA,MAGANIN AN RIGA AN GWADA KUMA YA NA DA AKYAU ƘWARAI.BARI IN GAYA MIKI YAR'UWA DUK WADDA TA CE MIKI MARTABAR ƘIRJINKI,ZAI DAWO MATUƘAR JIKINKI BAI MURJE BA,TO GASKIYA KUƊIN KI KAWAI ZA TA CI.

IN HAR KINA SON MAGANIN YA YI AIKI A JIKIN KI SAI KIN DAURE,KIN SHA SAFE DA YAMMA.SANNAN MUNA AIKAWA KO INA SIYAN NAGARI MAIDA KUÆŠI GIDA.

MAGANIN AKAN FARASHI MAI TSAUƘI IN KINA SO MAZA GARZAYO KI KIRA WANAN NUMBAR ( 07088268243) KO (08144072423)

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW READ AND SHARE.
Chapter 86 · 0% Book details