← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 86

Sashe 43

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banza da shi ta yi tana mamakin wai haka yake mai ya sa yau ya ƙara zuwa da salo ne?

" To shikenan tun da kin ƙi magana da ma zan yi godiya ne na ranar nan gaskiya na ya ba sosai,wannan daren momerable and remarkable ne a gurina,Allah shi zai saka miki saboda ai ba ta ki da ƙanin mahaifin ki ya yi."

Ya faɗa ba tare da kunya ba kuma ya na kallon ƙwayar idanunta.

Juwairiya ta ɗago ta kalle shi ba tare da ta shirya ba ta ji ta sakar mishi wani lalausar murmushin,har dimple ɗinta suka losa ta ruga da gudu ta shige ɗaki tare da rufo ƙofar.

A.m ya saki dariya don kunyarta ta na matuƙar burge shi matuƙar gaske,saboda ya na son mace mai kunya juyawa ya yi zuwa waje jin shigowar motar Zainab,ya saki duk wani wulaƙanci da yake son yi mata da tsanar ta da yake ji zai more abin sa kafin zuwa ranar rabuwar su,saboda tsakani da Allah ya ji wani girmanta a ranshi tun ranar da ya mallake ta,tsananin talaucin da take ciki bai saka ta zubar da mutuncin kanta ba.
Ƴa ƴan'uwana mata don Allah mu kama darajarmu domin shine mutuncinki, don Allah ƴan mata ka da son abin duniya ko jinkirin aure ya sa ki zubar da mutunci,don ki na tunanin kin daɗe ba ki yi aure ba ba zaki yi ba,ki tuna lokacin ki ne bai yi ba,kuma duk daren daɗewa in da kina raye za ki yi,yayin da ki ka yi aure wulaƙanci shi ne abin da za ki girba har ƙarshen rayuwarki.

Kuma Æ´ar'uwa da ki yi saurin aure ki fito gara ki daÉ—e ba ki yi ba,ki daure har ki samu wanda zai kula da ke emotionally,phisically financially,and mentally.Shawara ce.

Juwairiya gado ta faÉ—a tare da É—aukar filo ta rufe fuskarta da shi.
" Mai ya sa yake min irin waÉ—annan kalamai ne wai dama ba shi da kunya haka?Kai na rasa gane wa wallahi gabaki É—aya ya canza dariya fa ya yi min."

Sai ta saki murmushi ta mirgina wani gefen ta na jin wani irin nishaÉ—i a cikin zuciyarta.

" To ko ya fara sona ne?"

Da sauri ta kori wannan tunanin a cikin zuciyar ta amma kuma ta na fatan haka ta kasance,da sai ta ce tafi kowace mace sa'ar miji duniya,don A.m wuta ne gurin kyau da tsari.

Washegari Juwairiya ta na kicin abinci take haÉ—awa hankalinta kwance cikin jin daÉ—in abin da ya faru,jiya tsakaninta da shi jiya saboda kwana ta yi muryar sa na maimaita godiyar da ya yi mata.

A hankali ya shigo ba tare da ta sani ba don ta zage ta na haɗa mishi abincin da zai ƙayatar da shi.

Ji ta yi an rungume ta ta baya ba tare da ta lura ya shigo ba.Wani irin ihu ta saki tare da matsawa gefe,sai kuma da ta lura shi ne ta É—an saki murmushi.

" Kai ki na da matsala Juwairaah!Yanzu da matar gidan na nan mai kike tunanin zai faru?Ke akan komai sai an ga gazawar ki?"

Ta yi shiru kawai ta na murmushi ba tare da ta ce komai ba,don ita ba ta san Zainab É—in ta fita ba.

"Kawo min abinci yunwa nake ji."

Ya faÉ—a tare da saka hannun shi a daidai gurin dimple É—inta ya fita.

Bin sa da kallo ta yi har ya ɓacewa ganinta ta yi ajiyar zuciya sannan ta shirya masa abinci.

Bayan ta ije masa abinci ya na zaune da remote a hannunsa ya ce ba tare da ya yi duba gareta ba."Amaryar wucin gadi zo mu yi hira tunda matar so ba ta nan,na lura kamar kina da ciwon rashin magana."

Sai ta tsaya ta na kallon shi da ya yi fuska kamar ba shi ya yi maganar ba.
" Ki zauna mana kika yi min tsaye haba sai kace wata soja."

Namma zama ta yi ba ta ce masa ƙala ba don ta lura so yake ta tanka.
A.m da ya kasa controling É—in kan sa ya matsa kuda da ita ya na mata wasu irin abubuwa.

" Don Allah ina roƙon ka bu ɗaya.".
Ta ce yayin da idanunta suka fara zubar hawaye tsayawa ya yi ya na kallonta zuwa can ya nisa ya ce da ita."Ina jin ki Juwairaah."

A hankali ta yi ƙoƙarin saita muryar ta ta fara magana cikin sanyi.
"Ka ce kar na saka soyayyar ka a zuciyata ni ma ina roƙon ka da ka dai na ƙoƙarin kusanta kan ka da ni mu tsaya daga iya sharaɗinmu,saboda ina tsoron kar zuciyata ta kamu da sonka duk da na san kai ɗin ba sa'ar soyayya da ni ba ne,kaddara ta haɗa mu ina jin tsoron ranar da zan tsinci kai na cikin soyayyar ka don na san ka yi min nisa na har abada,amma soyayya ba ƙarya ba ne kuma zuciya ba ta da ƙashi,A.m babu wata mace da za ta yi tozali da kai ba tare da ta faɗa cikin kogin son ka ba.

Jikinsa ya yi sanyi matuƙa ganin maganar da take yi daga cikin zuciyarta ta fito.

"Juwairaah kin taɓa ganin an yi zaman aure ba tare da haka ba?Duk auren da kika ga ya ginu to hakan ya gina shi.Bani da nufin na cutar dake ki yadda da ni ki yi ƙoƙarin yaƙar zuciyarki daga son jefa ki cikin wahala da take son ta yi,kafin na aureki sai da muka yi sharaɗi babu so a cikin tsarinmu don ba zan taɓa zama dake na har abada ba ,amatsayin matata.Kuma karki manta uban maƙudan kuɗi na sa na auro ki".

Ya numfasa ya na kallonta ganin kukan da take yi hannunsa ya saka tare da tarar hawayen da yake zuba kamar an buÉ—e famfo.

" Ki adana sauran hawayen ki a kwai ranar da zaki buƙace su kar fa su ƙare,na tabbata ranar da kika haifa min baby in na baki abin da na yi ninya Juwairiya zaki nemi hawayen ki ki rasa bayan kin ƙarar da su akan banza,don ni banga abin kuka a nan ba.Ki tuna mahaifiyarki na cikin kwanciyar hankali da jin daɗi shin hakan bai saka ki saka ni a cikin farin ciki ba?"

Ya tambaye ta idanunsa a kanta hawaye suka ci gaba da zuba ganin taƙi magana sai sai ya miƙe ya fice daga gidan.

"Humh ba na tunanin a kwai abin da za ka ba ni na yi farin ciki fiye da ka sani a cikin zuciyarka.Am ka ƙi ka gane abu ne na zuciya Allah ya jarabce ni da sonka tun kafin ka bijiro da manufar ka a kaina,na yi burin kar mu haɗu tun ranar da na yi tozali da kai a kundin rayuwata."

Kuka take kamar wata zararriya ta na maganganu sosai daga baya miƙewa ta yi,bayan ta fahimci ya fice daga gidan ta ci gaba da aikinta.

A haka rayuwa take wucewa A.m ya na more amaryar wucin gadi duk da ya ƙosa su rabu,amma ya na girmama lamarin Juwairiya a zuciyar sa.

Tun ta na ɗari-ɗari da shi har ta saki sosai da shi domin ya bada duk wata ƙofa da zai saka ta saba da shi,har ta kai ga A.m ya na waya da Juwairiya a ɓoye su sha hira ya na tambayarta ko ya jefa ƙwallon a raga.
Duk sadda ya yi mata wannan maganar hankalinta ya kan tashi matuƙa ita gani take irin abubuwan da yake mata son ta yake.

Juwairiya ta saba da A.m ta na jin sa a ran sa kullum sai sun haɗu da juna ranar da Zainab take gida kuwa,dole sai ya kira ta a waya sun yi hira wannan ya ƙara saka ma Juwairiya son shi na mutuwa ta na jin duk ranar da ya rabu da ita mutuwa za ta yi.

Amma idan Zainab ta na nan ko kallon Juwairiya ba ya yi,har yau in zai yi maganar ta ko Zainab ta yi mishi nuna yake bai riƙe sunan ta ba,sai dai ya ce wancan ko wa ta ke da suna.
Tun Zainab na mata ƙorafin ta rinƙa cire hijabinta har ta gaji,ta dai na don ta fuskanci ko mai za ta yi mata ba za ta dai na ba,kuma ina ruwanta tun da ta fahimci Juwairiya a kwai tsafta da kula da kai.

Juwairiya ta goge ta waye ta ƙara wani irin kyau jikinta ya ciko ko ina,ita kanta mamakin yadda ta goge take yi,sai dai ko hoda ba ta saka wa bayan kwalli duk da Zainab ba ta hana ta ba.

To ina ma take da lokacin kanta daga aiki sai chert,don in dai ba ta gurin aiki ta na riƙe da wayarta,ko magana take hankalinta na kan wayarta.
Duk lokacin da Juwairiya ta samu tsarki sai ta samu lemun tsami da ruwan gishiri ta sha,ita burinta ko a matsayin mai aiki za ta zauna in dai ya na nuna mata irin wannan soyayyar za ta rayu da shi na har abada.

Kimanin tsawon wata bakwai A.m ya na jiran ya ji ta ce mishi ta na da ciki,amma shiru kake ji malam ya ci shirwa,har ya fara tunanin to ko shi ma baya haihuwa.

Hankalin sa ya fara tashi sosai gashi A.m har ya kasa daurewa ya tambayi Juwairiya shi fa ya ƙosa,lallaɓasa take yi ta na faɗa mishi Allah ne bai kawo ba,amma a ranta ta san abin da take yi.

Ya na zaune a falo zuciyar sa na tafarfasa da ya tabbatar Zainab ta ƙara tafiya ba tare da ta sanar mishi ba,ya ji a ran shi tunna ya na da Juwairiya zai ci gaba da haƙuri har zuwa sadda za su rabu,amma duk da hakan dole ta ɗauki mataki saboda ya kamata ta sanar mishi ko da bai amince ba,ba wai ta kashe wayarta tafi ba.

Wayar A.k ya katse masa tunanin da yake yi sai dai bai É—auka ba wayar ta katse ya bi,amma ba network sai a ka ce wayar a kashe.

Wani irin bugu ya ji ana yi mishi wanda ya tada hankalin sa da sauri ya fita don shi a zaton shi ɓarayi ne suke so su shigo mishi,duk da ce wa ƙarfe huɗu da rabi ne na yamma.
Chapter 43 · 0% Book details