← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 86

Sashe 54

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin hajijiya na kishin abin da ya faɗa ya kamata,amma ba ta son ran sa ya ɓace ko ta ɓata na ta,sai ta kalle shi ta yi dariya har da kashe mishi ido ta ce." Allah ko duk da ni matar shige ce ba matar so ba amma ka rubuta ka ije,zan nuna maka soyayya wanda ba zai taɓa gogewa zuciyar kaba ko da kuwa mutuwa na yi ba rabuwa mu kai ba."

Ta bashi amsar abin da ya faÉ—a duk da ranta bai yi mata daÉ—i ba.

" Allah ya sa ni dai na san tsabar shagwaɓarki ba zai baki damar haka ba, matar wucin gadi domin ke ma buƙata kike a lallashe mai hawayen banza.

Jin abin da ya ce sai ta saka kuka sosai ta na ƙarawa har da diddire ƙafafunta a cikin ruwan.
"Na rantse ka rubuta ka ije watarana wannan hawayen da kake kira na banza,sai sun zama abu mafi daraja a gurin ka wanda zubar su zai zama guba a cikin zuciyarka kuma da hawayen ka za ka rarrashe su."

Lakuce mata hanci ya yi tare da shiga cikin abin wanka ya ƙara dannata cikin ruwa ya ce." A kwai kuwa tabbas ranar da kika haifa min yarona kina kukan rabuwa da shi,ni ma zan zubar da nawa saboda tausayin ki da na ɗana wanda ba zan taɓa gaya masa ya na da wata uwar bayan Zainab."

Da sauri ta duƙar da kanta cikin abin wankan lokacin da ya saka hannun sa ya na ƙoƙarin yi mata wanka,hawayen dake zubo wa a fuskarta suka haɗe da ruwan suka gauraye ba tare da sanin ta yi kuka ba.

Wata irin kula A.m yake ba ta sosai sun sha yawo kusan babu ai da bai kai ta ba,ya yi yawo da ita ko ina tare da yi mata siyayya har ya na tonon ta da kayan lefe ya yi mata tunna bai yi ma matar wucin gadi ba.

Irin rayuwar da A.m ya nuna mata a ƙasar ta haƙiƙance ma kanta tabbas ya na sonta,kuma kafin su bar ƙasar za ta ƙara gaya masa ta na sonsa a karo na biyu,don har yanzu ba ta yadda ba ya son ta ba.

Bayan sun dawo daga yawo Juwairiya ta na kicin girki take yi,wanda A.m ya takura mata sai ta yi mishi tuwon ta mai daÉ—i na shinkafa da miyar taushe.

Tare suka je suka yo cefane ko da ta shiga kicin ɗin bin ta ya yi da wayar sa,ya saita ta na girki ya na mata video,hakan sai ya yi matuƙar burgeta ta na ƙara son A.m,saboda namiji ne wanda ya iya kula da mace ko da baya sonta,amma yanayin kular da yake mata ya isa ya nuna mata cewar ya na sonta.

Ko da ta gama abincin a ranar cewa ya yi shi zai ba ta a baki saɓanin da da ita take ba shi.

Haka ta zauna ya din ga ciyar da ita ya na É—aukar ta hoto.

Da suka zo gun kwanciya A.m ya rungumota ko mai ya tuna,sai ya miƙe ya tsaya a bakin windo tare da zuge labule ya na kallon waje.

Hakan da ya yi sai ta gane a kwai magana a bakin sa, ba ta miƙe ba amma ta tattara dukkan hankalinta ta na kallonsa.

"Juwairaah gobe za mu je akan maganar dashen ciki da za'a ayi mik, likita ya ce za ayi miki gwaje-gwaje kafin ayi."

Gabanta ne ya faɗi jin abin da ya ce ba ta ce masa ƙala ba,amma ta ji sanyi matuƙa da ta ji ya ce sai an yi gwaje-gwaje kafin a farke ta,ta san likitan ba zai yi mata in ya gwada ya ga lafiyarta ƙalau.

Dawowa ya yi kan gadon ya kama hannunta ya riƙe cikin murya mai sanyi ya fara magana.Na san ce wa ban kyauta miki ba don ba mu yi da yi miki aiki ba,amma ki taimake ni wannan ne kawai damata na yi miki alƙawarin ba ki duk wani jin daɗin duniya, in har za ki yadda a yi miki dashe ki haihu ."

Wasu zafafan hawaye suka wanke mata fuska wato har yanzu ya na kan bakan sa,abin da yake yi mata ya na yi ne don ta yarda a farke ta ba soyayya ba ne.

Jikinta ya yi matuƙar yin sanyi kamar ruwa ya cinye ta ayau ta yi ninyar ta gaya masa ta na son sa,amma ta cire ran A.m zai so ta a rayuwa ta na son a karo na biyu,kawai sai ta yanke shawarar gara su je Allah ya saka likitan ya ce ba ta haihuwa ya yi mata aikin,fatan ta a ce shi zai zama sanadin numfashinta ta huta da tarin baƙin cikin da take fuskanta.

"Na amince in dai hakan zai saka ka farin ciki saboda burina kenan,na saka ka a cikin sa ko da ace ni zan fuskanci akasin haka."

Hannunta ya riƙe kam sai ya rungumeta." Na san cewa duk ranar da muka rabu zan yi kewar mace,mai haƙuri da hali na gari ina miki fatan Allah ya baki rayuwa ingantacciya,kuma na miki alƙawari zan bawa ɗanki kulawa."

Komawa ta yi ta kwanta ba tare da ta amsa ba ta na zubar hawaye.

Washegari A.m da kan sa ya shirya ta suka tafi asibitin.Bayan gwaje-gwaje da likitan ya yi musu har da ita,ya tabbatar masa da lafiyar ta ƙalau ba sa buƙatar wani dashi.Magani ya ba su wanda duk lokacin da zai yi tarayya da ita ya yi amfani da shi.

Duk da cewar bai ji daɗi ba ya so ayi komai a wuce gurin,amma haka ya baro asibitin cikin jimami,ran sa duk babu daɗi bayan ya karɓi maganin.

A.m da gaske yake nufi da ya ce mata kafin su koma gida sai ya ba ta tsaraba,ita dai dariya ta ke masa suna gudanar da rayuwa a ƙasar mai wuyar mantawa.

A ranar da zasu dawo ta na kwance ta na tunanin in da za ta kai abubuwan da ya siya mata,saboda ya yi mata siyayya ya kashe mata kuÉ—i na ban mamaki ta san ko hauka ta yi ba za ta kai ma Mama kayan nan ba,haka kuma ba za ta kai gidan sa ta na amfani da shi ba amatsayin ta na Æ´ar aiki,mamakin sa take da ko tunani bai yi ba ya yi mata irin waÉ—annan siyayya.

Ta yanke shawarar kai ma Mariya ta ije mata kuÉ—in kuma sai ta din ga sakawa a banki.

Kamar yadda suka tsara jirgin su na sauka ta wuce gida kan sai ta ƙara sati,in ya so sai ta ce jikin Mama ne ya tsananta.

Juwairiya ta tsorata lokacin da ta yi sallama Mama ta amsa mata ta na ƙudundune da bargo,sai hankalinta ya tashi ganin ta yi wa Zainab ƙaryar Mama ba ta da lafiya gashi ta same ta ba lafiyar,shi ya sa ƙaryar ciwo babu kyau don ita gani take kamar ƙaryar da ta yi ne ya kama Mama.

"Mama dama baki da lafiya shine baki kirani kin gaya min ba."Ta faÉ—a cikin tashin hankali ganin ta na jin jiki.

"Na so na kira ki ita ta hana gani take kamar jikin ba zai yi zafi haka ba."

Ibrahim ya ba ta amsa don ta kasa magana sai hawaye dake gangarowa,saboda tsananin zafin ciwo kuma duka kwana biyu ta fara ciwo.

Asibiti ta samo mai adaidaita ya kai su bayan an yi mata allura aka ba ta magani,suka dawo gida ta shiga jinyar Mama.

Rashin lafiyar Mama sai ya hanata komawa gidan ta na jinyar Mama da yanzu ta fara jin sauƙi.

"Juwairiya ya kamata ki koma aiki kin san yau saura kwana goma sha biyar shekara ɗaya ya cika,kuma kin san na gaya miki ko duk duniya mutumin nan zai baki ba zan lamunta ki ƙara ko da kwana ɗaya ba."

Mama ta ce mata cikin murya mai ɗan zafi duk da jikinta babu ƙarfin da za ta ɗaga murya.
Gabanta ne ya faɗi ta ɗago ta kalli Mama sai jikinta ya yi sanyi ta ce."Na sani Mama kuma da zarar lokaci ya cika ni kaina gida zan dawo na yi aure kamar yadda kike buƙata,amma ki kwantar da hankalin ki kin ga yanzu ba kya jin daɗi."

Ta miƙa mata kofin kunu tsamin da ta sa ta dama mata saboda tafi son abu mai ruwa-ruwa.

"Ai ina tuna miki ne don ranar da shekara É—aya ya cika in har baki dawo ba sai dai ki ji na kai Baba Sani kotu."
Ta karɓi kofin kunun da ta miƙa mata ta fara sha.Jikinta ne ya yi sanyi ta miƙe ta fice daga ɗakin domin ba ta ƙaunar ta ji Mama ta irgo mata kwanakin rabuwar su duk sai ta ji hankalin ta ya tashi.

A yau take son ta je ta gyara layinta da kampani m t n suka kulle mata tun washegarin da ta dawo saboda ciwon Mama ta kasa zuwa ta gyara,amma yau ta ga jikinta ya yi sauki ya sa ta shirya don ta san A.m zai neme ta har ma da Zainab saboda ta ƙara kwanaki akan sati biyu.

Kasancewar da yamma ne sai ta yanke shawarar ta tafi a ƙasa tun da babu wani nisa.

Tafiya take a hankali kamar ba za ta taka ƙasa ba ji ta yi wata mota ta sharo ta na shirin tureta.

Da sauri ta matsa gefe cikin tashin hankali ta na tunanin waye wannan mahaukacin da zai kasheta.

"Ke amaryar wucin gadi ina za ki je ba tare da izini mijinki ba?"
Muryar A.m ya daki kunninta lokacin da yake saukar da gilas É—in motar sa.
Mamakin ganinsa da tsorata ta da ya yi ya sa ta ɓata fuska amma da murmushi ɗauke a fuskarta.
"Allah ka ba ni tsoro na yi mamakin ganin ka"Ta ce mishi lokacin da ta tsaya a gefen shi.

A.m ya kashe mota ya fito ya tsaya kusa da ita ya ce."Ina ta nemar wayarki ba ta shiga na kira wannan kwaÉ—ayayen Baba Sani amma kin san me ya ce."Wai sai na biya shi zai haÉ—a ni dake hankalina ya tashi hakan nan na daure na zan zo gidan ku sai gashi mun haÉ—e kin yi satar fita."
Chapter 54 · 0% Book details