← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 86

Sashe 4

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ta yi dan aka wo kuɗin wankin za su sami su yi girki. Da sauri ta ƙarasa ta na faɗin."La Mama har kin fara."Bata ce mata komai ba sai botiki da ta miƙa mata ta ibo ruwa a randa. Basu gama wankin ba har misalin tara da rabi bayan sun gama Juwairiya ta fita tayo musu cefanen taliya suka dafa da mai da yaji.Bayan ya dawo daga sallar asuba ya kwanta don ji yake ko ina na jikin sa ya na ciwo,bai tashi ba sai da aka gama girki shi ma sai da Juwairiya ta tashe shi,dan tasan yunwa ce ke damunsa. Bayan yaci abincin ya miƙe tare da fita ya na son ya ga kanin nasa,akan maganar komawa da Ibrahim asibitin da kamar yadda likitocin suka faɗa. Ya na ƙoƙarin shiga shashinsa suka yi kicibis saura kaɗan su yi karo,Baba Sani ya matsa ya na kallon ɗan'uwan nasa ya ce."Lafiya yaya baka da lafiya ne?Ji yadda ka koma kamar wanda ake iban shi ana miya."Yace da maganar shi ta izgilanci ya na karkaɗe jakar zuwa aikin shi,dariya kawai ya yi mai kama da yaƙe yace."A irin wannan rayuwar ka na sane da halin da nake ciki ni da iyalina,yanzu ko taimakon da kake yi min ka daina."Ya ƙarashe magana da takaicin yadda ɗan'uwan nasa ya daina taimaka mishi tun tsawon shekaru da irin butulcin da ya yi mishi. Hannun shi ya watsa ya kalleshi ya na kallon agogo."Sauri nake yi yaya kaga na yi latti kuma kasan yanayin aiki na,yi sauri ka faɗi abinda ke tafe da kai.Kuma da kake maganar ba na taimaka maka nauyi ne ya yi min yawa kowa ya ji da kansa." "Haka ne Allah ya shige mana gaba,amma ya kama ta ka duba rayuwar Juwairiya kaga ni bani da shi da zan saka ta a makaranta,kuma kace ba aure zakai mata ba baka da ƙuɗin auren da ita." "Haka na ce don ni yanzu ba ta aure nake ba,sabon gidana nake son na kammala.Ya bashi amsa a taƙaice sannan ya ɗora da ce wa."Kuma da kake maganar na saka ta a makaranta baka ga yadda take mara kamun kai ba can zata dinga watsewa da mutane,ka na sane da irin ƙorafin da nake maka a kanta ni nasan halinta da nake zaman gida." Shuru ya yi ya na takaicin abinda ya faɗa ransa ya yi zafi,shi dai yasan kawai ya tsaneta ne amma yasan wacece 'yarsa wani irin hali take dashi. "Yaya na fa gaya maka aiki zan tafi amma ka tasa ni gaba kana ta wasiƙar jaki,ina sauri ne in kima baka da abin faɗe na tafi imna dawo saimu tattauna."Ya ce dashi ya na ƙoƙarin fita da sauri ya tare shi sannan ya ce."A kan maganar komawa da Ibrahim asibiti ne,kuma gashi bani da kuɗi dan Allah ka taimaka...." "Haba yaya kasan fa bani da ƙuɗi nima hidima tayi min yawa kowa yaji da kansa,amma ga dubu ɗaya kuje Allah ya ba da lafiya."Ya miƙa mishi 'yan ɗari biyar guda biyu ya fice ya barshi a tsaye kamar sanda ya na tunanin butulci irin na ƙanin nasa. A sanyaye ya shigo cikin sasan sa ya zauna akan turmi kamar babu laka a jikinsa,bai ce komai ba har zuwa wani lokaci sannan ya ja numfashi ya na kallon Mama dake ninke kayan da suka wanke har sun fara bushewa. "Lailai ɗan adam butulu ne."Yace cikin raunanniyar murya sannna ya ɗora da cewa."Wai yau ni Sani yake wulaƙanta wa kan kuɗi ya manta yadda na wahala dashi dan ya sami ingantacciyar rayuwa.Mama ba tace mishi komai ba sai gyaran murya da ta yi,dan babu wani abu sabo a cikin halinsa duka sananne ne a gurinta. Juwairiya na kwance bayan ta tashi ta yi sallar nafila ta yi addu'a ta koma ta kwanta,idanunta babu alamun bacci sai juyi take yi ganin haka sai kawai ta janyo carbi ta na ja,idanunta a rintse zuciyar ta na fatan samun maslaha a rayuwar su tunannin ta inda za'a sami kuɗi a mai shi asibiti,don likitocin suna tunanni aiki za'ai mishi a ƙafar. Kawai sai ta ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakinta tsoro ya kama ta,tunawa da ta yi ta manta bata saka sakata ba da ta fita zuwa alwala.Tsananin tsoro ya kama ta ta rintse idanunta ta na tunani ta ya ya kai wani ya shigo cikon gidan su,dan Baba Sani ya gyara gidan kuma akwai ƙofa na masu kuɗi mai ƙarfi gidan. Ba ta gama wannan tunanin ba ta ji mutum ya shigo ya nufi makwancinta,ta buɗe baki da nufin ta yi ƙara sai kawai taji an toshe mata baki da wata irin murya da nufin a ɓatar da tunanin mutum ga sanin mamallakin muryar aka ce."In kika yi ihu saina kashe ki?Ya faɗa tare da soka zungureriyar wuƙa dai dai cikinta,amma ta yadda bazai cutar da ita ba. Wani irin tsoro da tashin hankali ya ziyar ce ta taji tamƙar numfashinta zai yi balaguro zuwa wata duniyar wacce take da banbanci da wacce take rayuwa a cikinta."Da gaske abin da sautin amon kunnnuwana suke gaya min muryar Baba Sani take amo a cikin dodon kunnuwana?To mai ya shigo dashi cikin ɗakina a wannan sulusin daren?"Irin tarin tambayoyin da suke ta bijiro mata a cikin zuciyar ta wacce ba ta samu ko da amsar ɗaya ba. _Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na uku dan har yanzu shinfiɗa ne har ba'a fara ba.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Chapter 4 · 0% Book details