Sashe 39
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya ta yi ta na ɗaga musu hannu ta ce da ƙarfi ta yadda za su ji ta don motar su ta fara tafiya." A huta gajiya a haka nake son abina kuma sai mutuwa za ta raba mu.Kayana zan shigo na karɓa."
Sannan ta juya da nufin ta shiga gida yayin da gabanta yake dukan tara!Tara!! Don ta san ba za su kwase da sauƙi ba.
A.m ya juya da nufin ya yi ma Juwairiya magana amma sai ya ga ba ta a cikin É—akin har ya fara taku zai bita sai kuma ya dawo,jikinsa na rawa da shi kan sa ya kasa gane kansa ya na jin wani canji a jikinsa.
Sai kawai ya nufi cikin bayi don ya tsarkake kan shi ya yi salla amma sa ya fasa jin ana buÉ—e gida da alamun Zainab ce ta shigo,da sauri ya Æ´arasa gurin windo ya buÉ—e ilai kuwa ita ce ta shigo da gudu saboda ruwa da yake dukanta.
Girgiza kan shi ya wuce cikin bayi da sauri don ya san in Zainab ta same shi a haka za ta fahimci wani abu,kuma rashin mutunci yake son ya yi mata sai dai yanayin da yake ciki na rashin ƙarfi ba zai ba shi damar yin hakan ba.
Ya jima a cikin bayi duk da kiran da Zainab take kwaÉ—a masa bayan ta shigo ganin ba ta gan shi ba,amma hakan bai sa ya ko É—aga kan sa ba ya na ta tunanin da shi kansa in aka tsare shi ba zai ce ga dalilin tunanin ba.
Ikon Allah dama Baba Sani ƙarya yake yi wa Juwairiya mace ce mai nagarta da kamun kai?Haka kawai sai ya ji tsanar mutumim ya kama shi har ya na jin zai iya komai don ya taimaki rayuwarta.
Ko da ya fito faga ɗakin bai ga Zainab ba wacce ya tabbata ta ga ji da zaman jiran shi ƙila ita ma ta na bayi ta yi wanka.
Sallah ya yi da sauri don yau ne karon farko da ya rasa jam'i shi lokacin ne ya wuce gani yake yau gari ya yi saurin wayewa.
" Hubbyna oyoyo zuciya ta yi kewar ka da gangar jiki."
Ta faɗa lokacin da ta buɗe ƙofa duk da cikin tsoro take amma sai ta daure ta kauda tsoronta ta furta hakan,don ita a shirye take koma mai zai faru ya faru in dai akan fita ne saboda ta ji daɗin fitan sosai.
Wani irin mummunan kallo ya watsa mata wanda ya sa ta firgita ta tsaya tare da fasa rungume shi da ta yi ninya.
A.m da yake a zucuye da ita ya miƙe tare da fasa shafa addu'ar ya gaura mata mari ji kake kau!
" Banza mara mutunci ni zaki maida ɗan tasha ki tafi wata ƙasa ba tare da sanina ba ki dawo ki na min ilinbo ko.To wallahi sai dai ki zaɓa ko ni ko fita zuwa waje."
Zainab ta saka kuka iya ƙarfinta kamar yadda ta san ya tsani kuka tare da watsi da kayan shafar shi da suke jere a madubi ta ce.
" Ai wallahi ka mari auren ka ba sai na zaɓa ba dama na sha gaya maka duk ranar da ka ƙara marina sai na bar maka gidan ka!Don kawai na fita zuwa waje saboda ba ka wayewa ba za ka mare ni,da ka zo nai man aurena da ka yi bincike ba'a gaya maka Momina ta na fita zuwa waje saro kaya ba,ai kai ma ka san dole na yi sana'ar ta kuma in baka manta ba har jari Daddy ya ba ni lokacin da za'a kawo ni gidanka."
Da takaici ya kalleta ganin ɓarnar da tayi mishi ya matsa kusa da ita daidai lokacin da ta ruga za ta fita don ganin yanayin sa ta san dukan ta zai yi,amma sai ya yi nasarar kamota ya riƙeta kamar zai ɓallata.
" Zainab ba cin son ki da nake yi da rabuwa zan yi dake saboda baki da tarbiya ni kaina na yi kuskure da ban yi bincike ba,saboda mun ga Daddyna na tare da mahaifin ki ashe Æ´ar mace na aura.To bari kiji wallahi ba zan zauna dake a haka ba maza ki fice min daga gida mara mutunci kawai."Ya ce zuciyar sa na tafasa kamar za ta fito.
Ya saketa cikin rashin tsoro ta tsaya ta kuma kauda duk tsoron da take ji na sa tuna huɗubar da Yayyinta,suka yi mata cewar su ma duk sai da suka sha artabu da mazajen su sannan suka haƙura suka bar su.
" Na gode da cin mutuncin da kake yi ma uwata amma ka sani yadda ba ka daraja mahaifiyata ba ni ba babu wani da banza da zan daraja, kuma Daddyna zan kira na gaya mishi dukana kake yi mugu azzalimi mai dukan mace."Ta ce ta na kuka da ƙarfinta.
Wani marin ya kawo mata ya na faɗin ." Ok haka kika ce to bari na ƙara miki sai kiji daɗin faɗin kashe ki na yi,kuma yanzu zaki bar min gidana ba sai an jima ba ki je can ki sami shashasha irin ki ki aura,amma ni ba zan bar mace mafi soyuwa a gare ni ta na cuɗanya da wasu mazan ba ke ko kishin kan ki ba ƙya yi ...."
Katse shi ta yi ta na faɗin."Babu in da za ni wallahi ai nasan ɓaɓatun banza kake yi,amma ba zaka iya rabuwa da ni ba."
A.m ya zaro bell É—in shi ya na kallonta ya ce " Tunna haka kika ce zan nuna miki halina baki san wane ne ni ba,amma sai kin tafi gidan ku in ya so in iyayenki suna son ki yi zaman auren sa hana ki tunna ni kin raina ni."
Zainab ta yi mamaki sosai ganin duk abin da za ta yi mishi ta yi amma ya kafe kan dole ta tafi,hankalinta ya tashi sosai domin in har ta tafi ƴan'uwanta za su din ga mata dariyar a she dama ba ta fi ƙarfin mijinta ba.
Sai dabara ta faÉ—o mata lokacin da ya janyo mata akwatinta ya tura mata ta É—auki waya za ta kira Daddynta, sai ta canza shawara ta kira Daddyn A.m ta fashe da kuka ta ce.
" Daddy A.m zai kashe ni da duka mun samu saɓani na kuma bashi haƙuri,amma kuma yaƙi dukana yake sosai.Don Allah Daddy ka zo ka taimake ni!Ga shi nan da bell ya nifo ni."Ta ce tare da saka sabon kuka ta saki ƙara ganin A.m ya yo kanta don ko kaɗan bai yi tunanin Daddy za ta kira ba."
" Baki da hankali ko mahaifina zaki kira uban me ya sa baki kira naki ba?"Ya ce tare da doka wayar a ƙasa.
Hakalin Daddy ya tashi matuƙar gaske jin wayar ta mutu wanda ya zargi A.m ya karɓe wayar,sai ya shiga safa da marwa don ya san halin ɗan na sa ba shi da haƙuri sam!
Har ya danna numbar ainihin mahaifinsa da nufin ya kira sa sai kuma ya fasa ya kira numbar A.m,wace ta yi ta ringing bai É—aga ba duk da ya na kallon wayar.
A karo na ba adadi A.m ya É—auki wayar tare da kanga ta a kunninsa cikin fushi ya ce.
" Hello Daddy."
"Abdurrahman ba da hankali ko! Ƴar mutane kake duka wa ya ce maka ana dukar mace in ka saba mata da haka,kafiya za ta din ga mata ita mace ai ƴar lallashi ne.Ka taɓa ganin wani ya duka matarsa a cikinmu irin tarbiyar da na baja kenan?"
Daddy ya tambaye sa cikin zafi ba tare da ya tsaya jin mai zai ce ba." Wallahi Zainab ta rai na ni nina san halin da take min!Daddy wata ƙasa ta sallake ta tafi saro kaya har zuwa Dubai bayan na hana ta.Shin Daddy na gaza ɗaukar ɗawainiyar ta ne?"
Shi ma ya furta cikin ɓacin rai da kuma murya mai sauti don ya manta da Daddy yake magana.
Daddy ya ji maganar wani iri tabbas ya ji ba ta kyauta ba,amma shi A.m har yau ya kasa gane wace irin mace yake aure kuma Æ´ar waye.
Jin Daddy bai ce komai ba sai ya yi ƙuta ya ce." Na rantse dole ta bar min gidana tunna ba ta da tarbiya ni ba zan yadda ta mai da ni namijin tace ba."
Ya ce ya na huci don Zainab ta ba shi haushi matuƙar gaske shi ya sa dama ya ɗauki alƙwarin in ta dawo ba za su kwashe ta daɗi ba,sai ta gane shi baya ɗaukar raini shi ya sa ya ɓoye sonta a wani guri na zuciyarsa don kar ya han shi ɗaukar mataki.
" Abdurrahman dama ka auri ƴar abokina ne saboda ka tozarta ni, ka nuna ban isa dakai ba saboda ba ni na haife ka ba ko?Ka na son ka tada min da taɓon ba na haihuwa ko?"
Daddy ya faÉ—a a raunane wanda hankalin A.m ya tashi da jin abin da ya faÉ—a don ji ya yi kamar kuka yake yi.
" No Daddy don Allah kar ka ce haka wallahi kai É—in kafi mahaifina don zan iya bijire masa,amma ban da maganarka ka yafe min."
Ya ce hankalinsa a tashe ya na ma mata mugun kallo saboda yau ne rana ta farko da Daddy ya yi mishi irin wannan maganar.
"To ina baka haƙuri tabbas ba ta kyauta ba karka ƙara dukan matarka ta sunna yanzu gani nan zuwa gidan,zan yi mata faɗa kuma dole ta daina tunna baka so ai kai kake da iko da ita."
Daddy ya ce masa cikin muryar taushi da lallashi ya na son ya kwantar da hankalinsa,ya san zai iya yin ɓatatta.
" To sai ka zo."
Ya kashe wayar ya na huci kamar mesa daga ƙarshe ficewa ya yi a ɗakin ya bar ta ya koma farfajiyar gidan ya na jiran Daddy,don har yanzu bai huce ba dole Zainab ta zaɓi ɗaya duk da ya san barazana kawai yake mata amma ba zai iya rabuwa da ita ba.