← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 86

Sashe 35

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Yi haƙuri ina sauraren ki ne."

To ba na son shashanci in ina magana duƙar da kunnin ki saitina za ki yi kuma duk na yi magana ki ɗaga kanki."
Ta ce sannna ta ci gaba da tafiya ta na faÉ—in." Atine ba ri na É—auko miki abu."

" Kut! Na shiga uku A.m ya san halin matar sa ya kawo ni cikin gidan nan."

Ta faɗi ta na jinjina kanta tare da tunanin irin zaman da za su yi da ita .A jiyar zuciya ta saki mai ƙarfi jin sakacin da Zainab ta yi da mijinta.

Kuɗi masu yawa ta miƙa ma Atine wacce ta sandare da jiranta,saboda har wanka ta yi ta saka kaya shara-shara wanda al'dar ta ce zama da irin wannan kayan a gida.

A lokacin Juwairiya ta gaji har ta fara gyangyaɗi ga yunwa dake ta ƙwaƙwular cikinta.

" Kin ga na jima ban dawo ba ruwa na watsa ga shi ki yi haƙuri."

Ta ce da Atine sannan ta kalli Juwairiya ." Ke ki tashi ki fara aiki kuma na manta ban gaya miki ba! Ba na son raini da ƙazanta."

Sai kuma ta ƙwala ma Baba mai aikinta kira da gudu sai ga shi ta ƙaraso mari ta zabga mata.Banza daƙiƙiya ba na ce miki za'a yi sabuwar mai aiki ba? Da kika gan su sai ki fara nuna mata aikin gidan ko sun yi miki kama da irin baƙin da zan yi ne?"Ta tambayeta ta cikin zafin rai.

"Ki yi haƙuri Hajiya ai ba ki bani umurnin haka ba kuma..."

" Rufe min baki banza maza ki je ki nuna mata."

" Allah ya huci zuciyar ki."

Ta ce tare da kallon Juwairiya sannan ta ce ." Mu je na nuna miki aikin."

Juwairiya da ta yi mutuwar tsaye ta dafe ƙuncinta don gani take kamar ita ta mara.Zainab ciki ta koma tare da ɗaukar wayarta ta yi kiran rabin ranta.
Tsananin tashin hankali Juwairiya ta shige shi ji ta yi tamkar ba za ta iya rayuwa a cikin gidan ba,a tare suka share hawaye da Baba suka kuma kalli juna.

" Ki yi haƙuri Baba haka matar gidan take miki?Gaskiya ba ta da mutunci a matsayin ki na wanda kika haife ta.Wai mai masu da shi suka ɗauki talaka shi ba mutum ba ne don kawai ya na nema a ƙarƙashin wani sai wulaƙanci."

Baba ta share hawayenta ta kama hannun Juwairiya ta ce " Humh ba zaki gane ba ne!Hajiya Zainab ta wuce tunanin ki ina tausaya miki wallahi Allah ya sa kin iya girki."

Ta ɗan ƙara matsowa kamar ta na tunanin Zainab za ta yi musu laɓe ta ce." Ina gaya miki wacce ta kora ta kawo ki da ta yi abinci juye mata ta yi a jikinta,ta rufe ta da duka wai mijinta ya ce ba ta iya girki ba.Ni fa ban taɓa ganin mutum irin maigidan nan ba,ya tsane mu sai dai shi baya duka."

Duk da Juwairiya ta san matsayinta a gidan amma sai da gaban ta ya faÉ—i ras!Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Da Juwairiya suka shiga kicin kusan ruɗewa ta yi kamar za tai hauka,irin dukiyar da aka narka da kayan na'ura,duk da ta yi aikatau gidan masu kuɗi ta san yadda ake sarrafa na'ura amma a ranar yar ƙauye ta dawo.

Abinci mai rai da lafiya Juwairiya ta shirya sannan ta shiga É—akin da aka ba ta wanda Zainab ta yi mata umurnin duk ta yi girki ta yi wanka.

Juwairiya ta da fari kasa amfani da kayan bayin ta yi sai daga baya a hankali ta fara gane yadda ake amfani da shi bayam ta ɓata lokaci ta na ƙauyanci.

Juwairiya ta yi mamakin irin kayan da ta jibga mata da sunan ta dun ga amfani da shi,haka dai ta shirya ta na ta tunani barkatai a ranta yayin da kewar su Mama ya kamata, matuƙa har ta ji hawaye na zuba a ƙuncinta.

Juwairiya na zaune a ɗakin da ya zama mallakinta bayan ta idar da salla sai kuma ta miƙe da sauri jin kamar Zainab na kiran ta.

Ta na baƙin ƙofar fita daga ɗakin suka yi kicibis da ita za ta shigo." Ke kurma ne ina kira kin yi banza dani."

Ta faɗa cikin ɗaga murya." Ki yi haƙuri ban ji ki ba ne."
Ta ce ta na kallonta amma kuma a tsorace take saboda kar ta kai mata mari.Tsaki ta yi." Maza ki je ki shirya dinning za mu ci abinci mijina yanzu zai shigo.Kuma ki cire wannan ƙazamin hijabin na ki don na san ina ya gani ba zai iya cin abincin ba."

Juwairiya ta ji jikinta ya yi sanyi jin umurnin da ta ba ta domin ba za ta iya fita a haka ba,amma sai ba ta ce komai ba ta saɓule hijabin ta koma ciki.

Hankalinta ya kwanta da ta tuna a kayanta a kwai hijabi wanda bai kai wancan tsawo ba,da sauri ta É—auko ta saka a jikinta bayan ta saka turare kamar yadda ta murceta.

Juwairiya na gyara dinning ta ji dirin mota alamun an shigo da mota,gaban ta ne ya faÉ—i ras! Don jikinta ya ba ta masoyin ta ne ya dawo haka kawai sai ta ji gaban ta na faÉ—i.

Da sauri take shirya dinnnig É—in saboda ta gama ta kauce ma ganin sa,amma sai kafin ta gama ya riga ya shigo ya na takun sa da sarsarfa irin na ingarmar namiji mai jini a jika.

Shigowar sa ya yi daidai da fitowar Zainab daga cikin É—akinta cikin wata irin shiga ta alfarma,amma fa a gurin sa wanda kuma Juwairiya ta ga bai kamata ta fito da irin wannan shigar ba,sanin a kwai ta a cikin gidan don har tafi shigar É—azu rashin kyan tsari.

Da gudu ta faÉ—a jikin sa ta na dariya cikin farin ciki.
Shigowar sa ya sa Juwairiya ta gane ashe tafiya ya yi saboda direban sa da yake janye da troley É—in sa guda biyu kuma masu girma.

Duka suke dariya sannan suka faÉ—a kan kujera suna bayyana iya kewar da sukai ma junan su.

A hankali A.m ya zura ma Juwairiya ido shi har ya manta sun yi da Atine yau za ta kawo ta.Ya É—auke idanun sa da sauri ganin Zainab ta bi in da yake kallo.

" Hubbina sabuwar mai aikin da Atine ta kawo mana ne,Allah ya sa ta yi maka sai dai na ganta kamar gidahuma ce ko ina yawo da hijabi,amma haka zamu yi haƙuri da ita don gaskiya na gaji da ɗaukar masu aiki."

A hankali Juwairiya ta É—ago idanunta ta É—ara su akan A.m duk da ba ta son hakan,amma ta na son ta ji mai zai ce mata.

Ga mamakinta sai ta ga ya taɓe bakin sa ya kalle ta kamar ya ga kashi ya ce." Uhm na gan ta sai dai ki yi mata magana ta kiyaye sosai in kuma taƙi dole ki canza wata don kin san halina."Ya ce a taƙaice sai kuma ya canza maganar ya na kallon Zainab ya ce." Na yi missing ɗin ki babyna sati ɗaya da na yi kamar na yi shekara,yanzu haka ma ban gama abin da na ke yi ba na baro A.k a can na dawo na ga kyakykyawar fuskar ki."

Ya faÉ—a kamar zai yi mata kuka yayin da idanunsa suka bayyana hakan ga Zainab da take kallon sa da wani irin murmushi ta na kashe masa ido.

" Allah ko zauji ka san ni da kai kamar hanta da jini ne É—azu ina ma wani operation, ka san Allah saura kaÉ—an na yanka sa ba in da ya kamata ba kuma fa kai na ke tunani."

Dariya suka yi duka ya riƙe hannunta ya ce." Na san za ki yi fiye da hakan akai na amma ki kula rai ya wuce wasa."

" Ke banza wawiya!Ba ki da tarbiya ko?Ko baki ko ya a gida ba in ma'aurata suna magana ki ba su wuri maza wuce daga nan stupid kawai!"

Juwairiya da ta yi mutuwar tsaye tun lokacin da A.m ya shige ta nemi hankalinta ta rasa ji take kamar ta ruga da gudu ta faÉ—a jikinsa.
Gabaki ɗaya ta manta a wace duniyar take wasu irin zafafan hawaye ta ji ya wanke mata fuska, saboda tsananin son da take masa wani irin kishin sa ya tokare mata maƙogaronta, har ta ji ta na son ta yi aman sa don ta na jin ɗacin sa ya na hawowa bakinta.

Muryar Zainab da ta daka mata tsawa ya fargar da ita halin da take cikin da sauri ta ruga da gudu,ta shige ɗakinta har ta na bugewa da bango ƙum!Amma ba ta kula ba don tsoron Zainab take yi sosai a ranta.

Ta na shiga cikin ɗakinta ta fasa kuka sai kuma ta toshe bakinta tuna ko a ina take daga ƙarshe toleit ta shige, ta kulle ta ƙara sakin kuka ta na buga kanta a bango amma ba ta kula ba ko kaɗan.

" Na shiga uku a haka zan rayu a gidan nan? Na tabbata zuciyata ta kusan kamuwa da hawan jini!Allah na roƙe ka ka yafe min laifin da na yi maka ka haɗa ni da A.m wanda da ma burin sa ya kawo ni gidan sa kishin sa ya yi ajalina!"

TO FA JUWAIRIYA AN YA DAI? GARA DAI KI TSAYA A MATSAYIN KI KISAN KE FA AUREN GWANGILA CE AKAN KI AMMA BA MATAR SO BA.INA JIRAN COMMENT TSAKANIN FANS ÆŠIN ZAINAB DA JUWAIRIYA.

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO

ÆŠUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ÆŠIN KU YA NA SAKA NI NISHAÆŠI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha shidda.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
Chapter 35 · 0% Book details