← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 86

Sashe 40

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zainab kuwa ba yan fitarsa ta yi tsaki tare da saka makulli a ɗakin ta na shafa ƙuncinta da ya sha mari ta ɗauki wayarta da ya fasa ta ce.Wahalalle kawai ka gama jarabarka sai ka siyar min wata wayar kuma ba zan fasa sana'a ta ba ƙarshen da zarar na samu lokaci wata ƙasar zan koma.Sai dai in hauka za ka yi ka yi."
Ya na tsaye a farfajiyar gidan ya ji hon wanda ya tabbata Daddy ne ya zo,mai gadi ya buÉ—e masa get ya shigo.

Da sauri A.m ya ruga kamar wani ƙaramin yaro ya faɗa jikin Daddy ya na magana kamar zai yi kuka.Dariya ya yi ya shafa bayan shi suka shiga ciki.

Faɗa sosai Daddy ya yi ma Zainab wacce ta ɗauke shi a matsayin son kai kuma ya tursasa mata ta ba A.m haƙuri,sannan ƙar ya ƙara jin ta fita ko unguwa ba wata ƙasa ba in dai ba da izinin sa ba.

Ya kuma ƙara da ce wa." Tunna A.m ba ya so ta dai na zuwa in ya so ko shi zai iya yi mata oder.

A kasale ta miƙe ta na ganin kamar son kai Daddy ya yi mata,amma ta rantse ko sama da ƙasa za ta haɗe ba wanda ya isa ya hana ta fita waje,don har ta fara saka kanta a cikin matan da za'a fara irgawa suna da kuɗi a cikin Nigeriya, so ba wani ƙwaro da zai hana ta fita.

Amma a fili sai ta ƙara sakin kuka ta ce " Na yi nadaama kuma na ba shi haƙuri Amma ya ƙi haƙura."

" Shikenan Daddy ya wuce amma kar ta ƙara."

Ya faɗa cikin ɓacin rai sannan ya miƙe ganin Daddy ya miƙe." Ok Allah ya kyauta ku yi haƙuri dama aure ɗan haƙuri ne ni zan tafi."

A.m ya shafa kan shi ya na murmushi ya ce." Daddy ya zo gidan son amma ko ruwa ba'a kawo mishi ba,ka yi haƙuri Daddy ni kaina haƙuri nake da ƴar taku komai ba ta iya ba sai shegen yawon tsiya da rai na miji,Allah Daddy ko ruwan zafi ban taɓa sha ba wanda Zainab ta dafa,asalima ce wa ta yi ba ta iya ba.Shi ya sa nake tunanin ta rako mata ne kawai.

Daddy ya saki dariya ya na faɗin daidai lokacin da ya nufi ƙofa." Ah ah wanan to magana ake yada min ba haƙuri ake ba ni ba,amma kuma a haka ka ga ƴar tamu ka kace in ba ita ba sai rijiya."

Tsaki ya yi ya na hararar ta ya ce " Shigo shigo ciki akai min ban san halin ta ba na ba ta amanar zuciyata."

Zainab kuwa mai da mishi da harar da yake mata ta yi ta ce." Ba wani nan wahala ce na ce ba zan yi ba ai ko addini bai ce dole sai na yi ba,kuma yanzu ai baka da matsalar abinci tunna ga Juwairiya nan mai aiki."

A.m ya watsa mata wani kallo wanda shi ya sa ma'anar sa jin ta ambaci Juwariya.
Ganin Daddy zai fice sai Zainab ta ce." Daddy bari na yi kiran Juwairiya ta kawo maka abinci,na san yanzu haka ta na kicin kuma zaka yaba don ta na da zaƙinn hannu."

Wani irin tashin hankali A.m ya ji ganin ta nufi kicin ɗin har ya na dana sanin maganar da ya yi gashi ƙilu zai jawo mishi bau!

Ya buÉ—e baki da nufin ya yi maganar da bai san me bakinsa zai ce ba sai ya ji Daddy ya ce.

" Karki damu ƴata kin san bana karyawa sai sha ɗaya bari na tafi Allah ya yi muku albarka,kuma don Allah ku din ga haƙuri da junan ku."Sai ta dawo ta fasa ta na murmushi.

Wani irin wawan ajiyar zuciya ya saki wanda ya sa har sai da Zainab ta juyo ta kalle shi,ya watsa mata harara,ya shige sama da sauri ya nufi ɗakinsa ya kwashi zanin gadon da ya saka a warshing mashine ya kunna da sauri har ya na sheƙa ruwa a ƙasa garin ya zuba a ciki.

Zainab ce ta shigo ta zauna a kan gadon ta na ƙare ma ɗakin kallo ganin ya na bayi sai kwanta ta na jiran sa,amma sai yaƙi fitowa ya tsaya kamar me tunanin wa ni abu da ya manta.

A hankali Zainab ta taso ta tsaya ta bayansa ta huging ɗinsa da sauri ya ture hannunta ya koma gado ya kwanta tare da rufe idanunsa ya janyo bargo ya lulluɓa da shi.

Ganin haka ita ma ta hau ta ɗaga bargon ta shige tare da rungume shi,ya sa ka hannunsa ya ture ta ta faɗi ƙasa don har yanzu haushinta yake ji,haka kawai ta ba ma wata mace damar shigowa rayuwarsa ga shi ya na jin wani abu da ba zai iya ce wa ga shi ba,don har yanzu jikinsa babu ƙarfi.

Da takaici ya isheta sai kawai ta fashe da kuka don ta bugu sosai ta miƙe ta na share hawaye ta ce." Bari na fita tunna baka buƙatar son ganina! Haba ko Allah muna yi mishi laifi ya yafe mana."

Ta saka takalmi ta kuma ce wa." Dama yunwa nake ji bari naje na ci abinci."
Haba da sauri ya diro a kan gadon da ya ƙudundune kansa da bargo ya janyo ta da ƙarfi ta faɗa kan gadon ya na zare ido.

" Ke ce kika ban haushi matuƙa amma na haƙura tunna kin ce ba zaki ƙara ba."
Ya ce da ita ya na murmushin dole ya saka hannun shi ya tallabeta ganin ta na murmushi ya ci gaba da ce wa." Baki san tashin hankalin da na shiga ba da baki nan kin san duk yawon ki ba ki taɓa bari mun raba shinfiɗa ba.Tun lokacin da na ce miki mun iso kika kashe waya na tsargu."
Ya ƙura mata ido ya na kallonta ya kai bakinsa kusa da kunninta ya na mamakin abin da zai ce mata." Ko dafa da na dawo na ga baƙya nan sai wancan wa take da suna ta bani abinci wurgi da shi na yi,a hotel na zauna saboda gidan ya yi min baƙi na kasa bacci ni kaɗai gabaki ɗaya kewanki ya dame ni,gaskiya ina son ki matuƙa."

Ya numfasa ya na mata wani tsadadden kallo da murmushi ya ci gaba da ce wa." Ina masallaci na ga kiranki duk da fushi nake dake har na fito cikin hotel É—in da nufin na É—auki mota na É—auko ki,sai ga shi kin kira ni in bar shi mijin Fati ya turo muku direba shi ya sa na karyo mota na dawo gidan tunna matar gidan ta dawo."

Ya faÉ—a ya na kaida kansa gefe shi kansa ya na mamakin kansa.
Zainab murmushinta ya ƙaru ta na jin wani irin girman kai da alfahari da mijinta da take yi,sai ta kama shi ta rungume ta na faɗin."Ina sonka Habibina ni na san ba za ka iya rabuwa da ni ba,ko ce wa da ka yi na bar maka gidan ka kana faɗi ne kawai amma ni da kai mutu ka raba."

" Tabbas Zainab maganarki dutse da sai dai ki taho asibiti jinya."Ya faÉ—a
Dariya suka yi duka ya rufe su da bargo ya kasheta da soyaryar shi sannan ya sa ta baccin dole,saboda ya sakin mata nauyin shi wai dole sai ta kwanta sun yi bacci,duk da ba shi take ji ba.

Kallonsa take yi yadda yake saukar da numfashinsa a hankali,daga gani baccin na kai mishi karo ita kuwa ta kasa baccin saboda wani irin yunwa dake ƙwaƙwularta,saboda rabonta da abinci tun daren jiya ta kasa ci ta na fargabar yadda za su kwashe da shi.

Shafa fuskarsa ta yi da yake ta sheƙi da kyau ta na mamakin mai ya hana shi bacci,sai kuma ta danganta hakan da ce mata da ya yi ba'a gida yake kwana ba ƙila ya kasa bacci ne.

A.m da fari baccin ƙarya yake yi ya saka mata nauyin jikinsa don kar ta ce za ta buƙaci abinci, ta je gurin Juwairiya don ya san a halin da take ciki ba yadda za'a yi ta iya wani aiki a gidan,amma kuma daga ba ya saboda rashin baccin da bai yi ma wannan mai kukan tsiyar da ta hana shi bacci sai bacci ya kwashe shi.

Da Zaina b ta gaji da juyi a gado ta bubbuga shi ya É—an buÉ—e ido ya na kallonta.
" Gaskiya ka tashi ni fa na gaji da baccin nan yunwa na son ta yi min lahani."

Ta faɗa ta na jan shi ya sauko shahada ya yi ya sauka tare da miƙa da salati,ya shige bayi ganin haka ita ma ta sai ta wuce ɗakinta ta shiga bayi wanka ta yi ta zira duguwar riga,suka fito falo suna taku a jere sai kace ba su suke ta faɗa ba.

************
Juwairiya kuwa bayan ta gama jin wayar da A.m yake yi da Zainab ta shiga tashin hankali matuƙa! A wannan lokaci ji take kamar ta buɗe ido ta ga ba ta a doron ƙasa kuka take yi sosai na rashin abu mafi girma a rayuwarta,wanda Baba Sani ya so ya yi galabar raba ta da shi dama mutane da dama amma ta yi yaƙi tukuru,ta ada na abin ta sai ga shi yau ta siyar da shi saboda kuɗi ta na shan wulaƙanci ba tare da an daraja ta ba.

Ta rintse idanunta ta na jin wani irin ciwo mai raÉ—aÉ—i a zuciyarta yayin da wasu tarin hawaye suka ci gaba da turereniya a fuskarta.
Cije bakinta ta yi lokacin da ta miƙe ta na jin wani irin azabar raɗaɗi ya na zagaye duk ilahirin jikinta.
Chapter 40 · 0% Book details