← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 86

Sashe 2

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

*******
Juwairiya zaune a gefen ƙanin ta Ibrahim ta zuba mishi idanu, ya yin da hawaye suke gasar turarreniya a fuskarta,ji ta ke kamar ta yi hauka tsabar damuwa ta na jin wani irin baƙin cikin halin da suka tsinci kansu. Zura hannunta ta yi a cikin kofin ruwa ta shafi fuskar Ibrahim da yake kwance rai kwakwai mutu kwakwai,sai kuma ta kama shi ganin yadda ya zaburat amkar zai shiɗe.
Mama da ke tsaye a bakin ƙofa fuskarta ɗauke da tsananin damuwa da ƙunci ta janye tagumin da ta yi tare da ajiyan zuciya mai ƙarfi."Anty Juwairiya mutuwa zan yi ga shi Baba ya ƙi dawowa."
Ya faɗa da wata irin murya da yake ƙoƙarin haɗa kalmomin da su."Baza ka mutu ba Ibrahim ciwo ba ya kisa."Mama ta ce cikin tausayin sa.
Juwairiya kuwa ta kasa magana sai kuka ganin gudan jinin na ta ƙanin ta tilo na cikin wani mawuyacin hali, ji take da ma ace ciwon a jikinta yake.Sun jima suna tsaye a kansa da numfashin sa yake baraxanar ɗauke wa,hankalin su a tashe sai shafa masa ruwa suke yi suna kuka gunun ban tausayi.
Juwairiya ce ta miƙe ta na faɗin"Mama bai kama ta mu zuba mishi ido mu na kallon sa a cikin wannan halin ba,tunna Baba bai dawo ba zan fita na samo abin da za'a kaishi asibiti.Ta ce cikin kuka Mama ta kasa ce mata komai duk da ta na tunanin in da za ta samo kuɗin,amma har ta na shirin fita ba ce komai ba."Juwairiya na shiga uku!Ya sume."Ta ji muryar Mama cikin ƙaraji dai-dai lokacin da ta fice da ga gidan.

*Follow,read,comment,share.*

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA BIYU*
Chapter 2 · 0% Book details