← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 86

Sashe 59

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Riƙe rigar A.m da ya juya zai fita ganin ta ƙi cewa komai da nufin ta gaya masa baƙaƙen maganganu,amma yayin da ya zuba mata idanun sa masu kama da an zuba zaiba a ciki,sai ta ji wata irin narkakkiyar dalma na son sa ya zagaye duk ilahirin jikinta,kuma ba ta taɓa ganin Mama ta yi sa in sa da mahaifinta ba.

Juwa ta yi da sauri ta yi ta shige ɗaki tare da sakin kuka mai ƙarfi.

A.m ya daɗe a ƙofar gidan ya duƙar da kansa a kan sitiyarin motar sa,sosai ya jima a gurin ya na jin damuwa a ran sa.

Wayar sa ya zaro ya nemo numbar ta da ya yi saving da suna damuwata,domin haka yake kiran ta tun da ta shigo cikin rayuwar sa ta saka mi shi damuwa.

Da ya yi nufin ya kirata akan su tafi sai kuma ya tuna bai san wanda yake musu shishshigi ba,da sauri ya figi motar sa a guje ya bar ƙofar gidan,a ran sa ya na addu'ar Allah ya sa ta dawo yau saboda ya yi missing ɗin girta.

A ranar ta shirya ta koma gidan A.m saboda gidan ya yi mata babu daÉ—i.

Suna zaune a falo Zainab ta kwanta gaba ki ɗaya a jikin shi tana zuba mishi shagwaba,yayin da shi kuma sai biye mata yake yana ƙara saka ta cikin lambun son sa.

Hankalin sa na kan ƙofa ganin yamma ta yi ba ta shigo ba,wayar sa ya zaro ya ƙara tura mata da tsaƙon da ya tura yafi sau ba adadi kamar haka.

"Aslm mai kike yi har yanzu ba ki dawo ba,na gaya miki kar ki ƙara mintuna a gidan na maza ki dawo.Da fatan za ki bi umurnina a matsayina na mijin ki n wucin gadi."

Tun da ta ƙaranta sau ɗaya ba ta ƙara gigin ƙara karanta wa ba,duk da tsaƙon yana shigowa duk bayan mintuna.

Da siririyar sallama ta shigo wanda idanun A.m yana kallon ƙofar shigowa.Karab suka haɗa ido ya yi sauri ya ɗauke kan sa,sai ya ɗan ture jikin Zainab ya miƙe da sauri zai haye sama.

Zainab da sauri ta kalli bakin ƙofa ta kuma mai da idanunta kan A.m da ya miƙe yana danna waya zai haye sama.

" Honey ina za ka je."

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce." Ba shopping kika ce zan kai ki ba?Ina son na watsa ruwa zafi nake ji."Ya faÉ—a ba tare da ya kalle ya ba.

Hannun sa ta kama ta riƙe tana sakin mi shi lallausar murmushi. Tare nake son mu yi jirani just one minute."

Ta juya kan Juwairiya dake tsaye kamar sanda tana kallon su."Sannu mara mutunci Mamar ta ki mutuwa ta yi da kika je kika zauna?"

Juwairiya da take jin gabaki ɗaya ranta babu daɗi ,ba ta tanka mata ba sai ajiyar zuciya da ta sauke,na alamun wacce ta ci kuka ta ƙoshi.

" Ke ni za ki kawo wa rashin mutunci banza yar matsiyata ki kula in kika ce hauka za ki yi mini,wallahi sai in kashe ki in kashe banza,na ga uban da zai tsaya miki.Ai ni duk wanda ya shiga gonata saina raba sa da rayuwarsa,kuma mu zuba mu gani shege ka fasa."

Ka sa ce mata komai ta yi ta saci kallon A.m da ya jingina jikinsa da kujerar dinning har yanzu,danne-danne yake a wayarsa ba tare ya tanka ko kallon É—aya daga cikin su ba.

" Ni fa zafi nake ji so zan shiga ciki sai kin shigo."Ya faÉ—a babu ko É—igon damuwa a ran sa.

" Yarinyar nan ta ba ni haushi fa tana sane da kuÉ—i nake biyan ta,amma ta je gida ta zauna Allah saina cire kuÉ—ina don ba zan yi asara ba."Ta ce tana kallon A.m ko zai ce wani abu.

Watsa mata mugun kallo ya yi tare da jan tsuka." Duk abin da za ki yi mata ki ba Æ´ar aikin ki ba ce,ina ruwana wannan ya rage naki."
Yana gama faÉ—in haka ya haye matakalan bene ba tare da ya kalle ta ba.

" Ki yi haƙuri jikin ta ne ya yi tsanani har sai da muka kwanta asibiti k..."

"Rufe min baki shashasha." Ta katse ta cikin tsawa.

" Da ga yau duk wani aikin gida ya koma kan ki Lantana ba za ta ƙara komai a gidan nan ba,maza ki wuce underwears ɗina sun yi datti ki haɗa da na A.m ki wanke.Ta faɗa tare da kama kunninta sai kuma ta saki ta haye sama.

Tun daga wannan ranar take wahalar da ita duk wani aikin gidan ita take yi,dalilin haka ko makaranta ba ta zuwa wani lokaci,domin ƙawayen ta take kwasowa ta saka ta girki,har in za su tafi ta ba su abincin ba sai sun yi girki ba.

Wani lokacin sai ta kira ƙawarta ta ce ga za ta turo Juwairiya ta yi kwana biyu ta taya ta aiki.Ga zagi da cin mutunci komai aka yi ita ce.

Juwairiya ta yi shiru ne sakamakon tsorata ta da A.m ya yi kan in ta yi gigin tona asiri,zai cutar da Mama sannan ba zai gaya mata in da take ba.Hakan ya sa take jure duk wani cin kashi da take mata.

Kusan tsawon lokaci ta yi tana saka ido a tsakanin su haka Lantana ko tari ta yi idanunta na kanta.

A.m ya kauda duk wani abu da na zargi da shiga tsakanin su,har faÉ—a yake ma Juwairiya kamar bai santa ba,kuma kullum cikin sata aiki yake in dai yana gida.

Duk wani saka ido ta yi ta gaji daga bisani ta ci gaba da harkokinta dama ta san A.m ba zai taɓa iya kalon ta ba,balle yanzu da duk ta zube ta lalace saboda wahalar aiki da ƙuncin son maso wani da take yi,sai hanci da ta yi gashi kullum sai ta yi mafarkin Mama da Ibrahim.

Tafiya ta kama Zainab ba tare da wani shakku ba ta bar ƙasar bayan ta saka Lantana,ta din ga kwana a gidan har ta dawo hakan bai wani ɗaɗa A.m da ƙasa ba ya amince.

Cikin dare bayan sun yi bacci A.m yake shaƙa mata Lantana maganin bacci,wanda in ta kwanta sai safiya take farkawa.
Sai safiya ta yi ta din ga ƙorafi tana mamakin baccin da take yi ita dai Juwairiya dariya take mata sosai.
Juwairiya ta gasganta A.m ƙarshe ne gurin wayo da basira,ita kanta mamakin sa take ga wayo da iya kalami ga mace wanda hakn yake sa ta mutu ƙaunar sa.

Zaune suke a cikin makaranta ita da Hauwa Juwairiya ce ta siyo su agwaluma da yalon Bello,tana ta ci tana lumshe idanun ta domin su take son ta ci.

Hauwa ta kalle ta ganin yadda take ci kamar wata mayunwaciya.
Ganin yadda ta kafe ta da ido sai ta ɓalli agwalumar ta cige baki,saboda tsami amma haka take son sha.

" Humh ke ma ka yi mamaki kamar wata mayya haka na tashi ina son na sha agwaluma,bayan ni ba mutuniyata bace saboda tsaminta."Ta ƙara ɓalla tare da lumshe idanunta saboda daɗi.

Dariya Hauwa ta saki ta ce."Anya lafiyarki ƙalau kuwa ko dai ciki kika samu?Ni fa ina ganin kamar ciki ne da ke?"

Da sauri ta miƙe tare da yar da agwalumar cikin tashin hankali ta zare ido ta ce."Na shiga uku ciki fa da kika ce gaske ne?"

" Ina zan sani tunanin haka nake gani a jikinki yau kuma kin zo da baƙon lamari abin da ban taɓa ganin kin sha ba kike sha.To ke ya kamata ki gane yaushe rabon ki da yin ɓatan wata?"

Ta tambaye ta ganin yadda ta diririce har hawaye sun fara sintiri a fuskarta.

" Umh umh wallahi na manta tashin hankali ba zai barni na tuna ba,amma ina ganin kamar tun ina gidan Mama wayyo Allah na bani!"

"Mene ne na banuwa Juwairiya fata za ki yi Allah ya sa wannan cikin ya dasa so tsakanin ki da mahaifinsa."
" Tab!Ai wallahi in Zainab za ta iya haihuwa to ni ma zan bar wannan cikin a jikina zubar da shi zan yi ko da zan rasa rayuwata ne,nufin ki na fara irga watannin rabuwa da A.m na koma gurin Mama? Ba zan iya ba domin ban san da wani idon zan iya kallon ta ba."Ta ce cikin kuka.

" Haba wai ke mai yasa ba ƙya fahimtar magana da ɗaukar shawara ne! Ki bar cikin jikin ki na tabbata shine makamin da zai jawo kusanci tsakanin sa da mahaifin sa."

Hauwa ta faÉ—a cikin zafi domin zuwa yanzu ta fara ba ta haushi ganin ta cika kafiya da taurin kai.

" Na lura ba kya sona so kawai kike na rabu da farin cikina.To sai na zubar da cikin nan kuma babu wanda ya isa ya hana."

A zafafe ta furta cikin ɓacin rai tana gani n kamar ba ta son zaman ta da A.m.

" Ni ban ce ba ina baƙin cikin yadda kika ɗauki so kika ba ma namiji wai shin shine kaɗai namiji a duniya,na tabbata ko rabuwa kuka yi za ki samu namiji mai kyau ki aura,ke ma ki na da kyau."

Miƙewa ta yi tare da ɗaukar takaddun ta."In har za ki taimakamin na zubar ki zo ki raka ni asibiti,in kuma ba za ki ba ai na san hanya."

Ta nufi hanyar fita da sauri Hauwa ta biyo bayan ta duk da ba ta farin ciki da zubda cikin amma babu yadda za ta yi.

Likita ya kalle ta cikin mamaki sam ba ta yi kama da mutuniyar banza ba,amma mai ya sa take son ta zubda ciki? Da kuma ya tuna mugu ba shi da kama.

" Don Allah likita ka taimaka ka zubda cikin nan ko nawa ne za mu baka."

Juwairiya ta faÉ—a jikinta na rawa ta kwaso duk kuÉ—in da ke jakanta ta ije a teburin sa.

Duk tsoron da take ji na allura haka ta bari ya zumbuÉ—a mata tana cige baki,sannan ya É—auko wani magani ya ba ta kan in ta ji ciwo ta sha guda biyu.
Chapter 59 · 0% Book details