Sashe 68
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shaƙeta ta yi sosai kamar za ta kaita lahira ta na faɗin." Wallahi yau sai kin raina wayon ki saina nuna miki kuskuren shiga gonata da kika yi,duk cin mutuncin da kika yi mini ashe ki na nan a gidan kuna cin amanata bari ya dawo haɗaku zan yi na ƙona."
A.m dake tafe a mota da sauri har baya ganin gaban sa ya so ace ya na gida uwar haka,sai dai ciwon ya tashi sosai don aiki a ka shiga da shi afendis ke damun sa.
Ya na tuƙi amma hannun shi rawa yake yi saboda ya san a wannan lokacin,Zainab ta farka kuma komai zai iya faruwa.
Ko da ya iso gida bai yi parking ba ya ije motar tare da rugawa zuwa cikin gidan.
Zargin sa ya tabbata daidai saboda tun kafin ya shigo cikin falon,yake jin ƙarar Zainab da hargowa.
" Zainab ki bar abin da kike yi ki tsaya zan yi miki bayani."Ya ce da ita don yau ta faru ta ƙare.
Wani irin banzan kallo ta yi mishi tare da sakin ƙara." Uban me take mini a gida kalle ta fa A.m sam ba ta yi kama da mai aiki ba,duk tunani na tabar gidan na..."
"Wannan dalilin ya sa nake ta son ki ba ni dama na yi miki bayani "Ya katseta ya na faÉ—in haka.
" Bayanin me za ka yi mini buƙata ta kawai ta bar gidan nan."
Janye rigarta ta yi da ƙarfi ta ture Zainab daga jikinta cikin tsawa.
" Ya ishe ku gabaki ɗayan ku na gaji kuma kar ki ƙara riƙe ni ki na tuhuma ta,saboda matsa..."
Wani irin saukar mari ta ji ƙuncinta mai zafi wanda ya saka ta ji jiri ya kwashe ta,ta yi taga-taga za ta faɗi amma ta riƙe drower na kicin ɗin.
" Ki iya bakinki kuma ki tsaya a matsayin ki."A.m ya faÉ—a bayan ya kwasa mata mari.
" Ka ƙyale ta ta faɗi abin da za ta faɗa yau sai na wulaƙanta rayuwarki."
Juwairiya da ta ji saukar marin har ƙwaƙwalwarta ta rintse idanunta cikin kuka sosai,don yau ta tabbatar A.m ba ya sonta! Munafiki ne mayaudari ne kawai ya na more jikinta ne da mugayan kalamansa da yake yaudarar ta.
Ta buɗe baki za ta yi magana sai ƙamshin turaren A.m da ya canza ya daki hancinta,wani irin amai ya taso mata duk yadda ta so ta mai da shi ina ta makara!
Da sauri ta ruga zuwa bayi amma tun kafin ta kai ta fara amai tamkar za ta amayar da Æ´an hanjinta.
Sai Zainab ta din ga kallon A.m da ya tsaya tamkar gunki ta buÉ—e baki za ta yi magana,ta kasa sai ta ji kamar babu harshen ta a cikin bakinta,yayin da kanta ya É—aure iya É—aurewa kuma ya yi mata nauyi,jin kanta take ya yi nauyi, tamkar an yi mata gammo an É—aura mata duniya da abin da ke cikinta.
Matsawa ta yi gurin A.m sai kuma kamar an tsikare ta,ta ruga da gudu cikin ɗakin Juwairiya da take ta sheƙa amai tamkar ba za ta yi rai ba.
Allah sarki tsayawa ta yi ta kasa komai kamar jira take ta gama ta fito ta yi mata sannun a yadda ta nuna,amma iya tashin hankali da take ciki ya sa ta yi mutuwar tsaye,har ta kasa banbance wace rayuwa take ciki tsaƙanin ta duniya da lahira.
A.m da ya ƙaraso da sauri don bai fahimci wainar da ake toya wa ba,ya yi tunanin ko Zainab ta biyo ta ne da dake ta.
Abin tausayi amai take yi tamkar ba za ta daina ba,kuma A.m ya yi mamaki har ta gama amai ta fito bayan ta wanke bakinta,Zainab ba ta tanka ba,sakamakon suman tsaye da ta yi.
Wani irin ajiyar zuciya ta saki tare da firgita kamar wacce ta dawo daga doguwar suma.
Duk da cewa ita ba likitar mata ba ce,amma a iya zaman ta cikin asibiti ta san yadda ake gane mace mai ciki.
Hannu Juwairiya ta kama tare da duba tsakiyar hannun,sannan ta ɗaga ƙwayar idanunta.
Gabanta ya buga da sauri sabo da fahimci abin da Zainab take dubawa,lokacin da ta je asibiti ita da Hauwa abin da likitan ya duba kenan ya ce mata ta na da ciki.
Sam ba ta yi tunanin ciki ne da ita ba saboda wancan ba ta yi amai ba sai kwaÉ—ayi.
" Na shiga uku ya Allah karka saka mafarkin da nake yi ya zama gaskiya!Ka sa na buÉ—e idanuna tun kafin na aikata abin da duniya za ta yi tur da ni a cikin mafarkin.
Juwairiya take da ciki wa ya yi mata?"
Ta faɗa cikin ƙaraji tamkar wata zararriya ta na ihu gabaki ɗaya kamanninta ya canza
Juwairiya da A.m har ma da Lantana da ta yi laɓe a bakin ƙofa ta na jin mai ke faruwa!Suka haɗa baki gurin faɗin
" Cikiiii."
Sai kawai na ga Lantana ta hantsila ta yi waje cikin tashin hankali,ba tare da na yi wani tunani ba na bita a guje,saboda ba zan iya ganin wannan badaƙalar ba.
KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.
BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 30*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Zainab ji ta yi ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba,ta yi kukan kura sai ta faɗa kan Juwairiya ta ƙara shaƙe mata maƙogaro.
" Uban wa ya yi miki ciki da ma ke Æ´ar iska ce."
A.m da sauri ya yi kanta tare da ƙoƙarin ɗaga ta kanta ganin ta na son ta yi mishi illa."Ba ki da hankali ƴar mutane za ki kashe?"Ya ce lokacin da ya ɗaga ta daga jikinta.
" Barni da ita wallahi in a kwai abin da yafi kisa zan yi mata! Ta ya ya za ayi tayo ciki ta shigo mini da shi gida."
Sai kuma ta ce." A.m don Allah karka sa na haukace ahalin yanzu ji nake kamar numfashi na zai É—auke!Ka da zargina ya zama gaskiya ka barni na koreta a gidan ta je can ta nemi uban cikinta."
" Zainab ki tsaya ki fahimce ni na yi miki bayan..."
"Wai mai za ka gaya mini?In dai ba ka na son ka faɗa mini yau ne ranar da fitan numfashina zai yi bankwana da gangar jikina"!To na roƙe ka don Allah ka ƙyale ni.Juwairiya ta fita daga gidan nan shine kawai zai saka na fitar da zargi a cikin zuciyata."Ta ce tana kuka sosai.
" Sam ba za ta bar gidan nan ba samun sauƙin ki shine ki fahimci abin da zan gaya miki,domin ba ni da nufin na cutar da ke duk abin da yake faruwa na yi ne don ke."
Ja da baya ta fara yi tana mishi wani irin kallo,sai ta kalli ta ta kuma ƙara kallon sa kawai sai ta shaƙe shi.
" Na shiga ukuna ni Zainab zuciyata ,za ta buga A.m zai kashe ni,ka da son yara da kake yi don kawai ba na haihuwa ya sa ka naimi Juwairiya ka haihu ta zina! Tur mai za ka yi da É—an zina kuma ya fito ta jinin matsiyata."
Sai kuma ta sake shi ta nufi kanta tana faɗin."Wallahi saina kashe ku iyaye sun danƙaramin dukiya,shine za ku din ga zina akan gadona har ku samu ciki h."
" Ya ishe ki Zainab! Kar ki ƙara ai banta min yaro,kin san halina ba zan taɓa aikata zina."
Ya buɗe baki zai gaya mata matsayinta sai ya kasa ya sunkuyar da kan shi ƙasa,yayin da tsananin tausayi ya kamasa ganin yadda ta koma kalar tausayi tana kallonsa.
" Ki fahimce ni Zey ke san ba zan taɓa haɗa ki da..."
" Ba na son ji! Ba na son ji!! Mayaudari munafiki mai alƙawarin banza.Tur da na aureka na yi nadamar ranar da na ce ina sonka,kar ka matso kusa da ni in ba haka ba kashe ka zan yi!"
Ta faɗa tana girgiza kanta tare da toshe kunninta ganin ya nufi ta zai riƙe ta.
" Wannan dalilin ya sa na yi duk iyakan ƙoƙarina na fahimtar dake."
Ya ce da ƙarfi ya na kallonta sannan ya ci gaba da cewa." To tun da ba ki bani dama ba,bari na gaya miki gaskiya..."
Katse shi ta yi da ƙarfi tare da ƙara cakume shi ta ce." Mai za ku gaya mini mai kake son kace?Abu ɗaya na sani cewar mijina A.m ya na kwana tare da ƴar aikina,wallahi kaf duniya sai sun ji don a jarida zan buga,A.m ya yi ma ƴar aikina ciki za su haifi ɗan shege ɗan zin."
Wani irin shaƙa ya kaima wa da ya sa ta ji numfashinta zai ɗauke.
" Kar ki ƙara aibata min ciki ɗan dake cikinta halastacce ne kuma ta aure muka same shi,don ban san ta ba a matsayin ƴa mace ba,sai da aka karɓar min aurenta."
Ya zaro idanun sa ganin ba ta fahimci abin da ya faɗa ba." A taƙaice Juwairiya matata ce ta sunna wanda Daddy ya karɓar min aurenta! Don haka karki ƙara aibanta min yaro don wallahi sai kin gane baki da wayo."
Kawai gani ya yi ta sulale a ƙasa ta faɗi sumammiya.Da sauri ya yi kanta ya na kiran sunan ta.
Gabaki É—aya ya ruÉ—e ya rasa ta in da zai fara rungumeta ya yi cikin tashin hankali sunanta kawai yake kira.
Da gudu Juwairiya ta shiga kicin ta ibo ruwa ta watsa mata,amma sam ba ta farfaÉ—o ba jikinta ya yi É—ip kamar babu rai a jikin.