← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 86

Sashe 75

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

INA ƳAN MATA DA MATAN AUREN DA SUKA SHAYAR SUKE SON MARTAR ƘIRJIN SU YA DAWO?

INA MATAN DA SUKE FAMA DA RASHIN ƘIBA KO INA A ƘAME?

MAZA GARZAYO KI SIYA INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO DA ƘIBA,MAGANIN AN RIGA AN GWADA KUMA YA NA DA AKYAU ƘWARAI.BARI IN GAYA MIKI YAR'UWA DUK WADDA TA CE MIKI MARTABAR ƘIRJINKI,ZAI DAWO MATUƘAR JIKINKI BAI MURJE BA,TO GASKIYA KUƊIN KI KAWAI ZA TA CI.

IN HAR KINA SON MAGANIN YA YI AIKI A JIKIN KI SAI KIN DAURE,KIN SHA SAFE DA YAMMA.SANNAN MUNA AIKAWA KO INA SIYAN NAGARI MAIDA KUÆŠI GIDA.

MAGANIN AKAN FARASHI MAI TSAUƘI IN KINA SO MAZA GARZAYO KI KIRA WANAN NUMBAR ( 07088268243) KO (08144072423)

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 33*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"Hamdiya na roƙe ki kibar maganar nan don Allah,domin babu abin da zai saka ni sai tarin baƙin ciki.A halin yanzu wannan ba shi ne a gabana ba,ina son na koma gurin Mama ina jin ban kyauta ma ta ba,duba ga irin wahalar da na ke sha,wallahi ji na ke komai na duniyar ya yi mini zafi.

Sai ta saki kuka sosai tare da miƙewa tsaye, da nufin ta fice da da falon,amma wani irin jiri ne ya ibe ta,wanda ya saka ta koma da sauri ta zauna,tare da rintse idanunta.

" Haka ne ba ki yi mata adalci ba,amma ki gode ma Allah da iyayen A.m su ka karɓe ki,in da ace kin haihu ne ya karɓi ɗan sa,da wane irin ido za ki kalli Mama?"

"Duk da haka ban yi mata adalci ba alhalin yanzu,iya tsananin wahalar da na ke ciki,ya kamata na gane kuskuren da na aikata."

Sai ta ƙara sakin kuka." Ki yafe mini Mama ina nan dawowa gareki na nemi yafiyar ki."

"Ya kamata ko da za ki koma gurin Mama,ki nemi mutuncin kan ki a gurin Ya A.m,saboda abin da ya yi a gaban iyayenmu ya ƙona mini rai sasai,yana tare da ke amma ya dubi tsabar idanun ki ya ce baya sonki a gaban kowa."

Juwairiya ta kalle ta da kamar ba za ta ce ko komai ba,amma kuma ganin yadda ta mai da hankalinta da damuwarta gareta, amatsayin ta na yar'uwar sa,sai ta ce.

" Haka ne amma ni ban ga abin damuwa ba,tun kafin mu yi aure yake gaya mini ba ya sona,yana da matar so ni kuwa auren wucin gadi muka yi da shi,duk da ada ina masifar son sa, amma haka ya din ga wulaƙanta ni yana kirana da matar shige,a yanzu na yadda ni matar shige ce,kuma na ƙosa mu rabu na huta da warin da nake ji a jikin sa."

Hamdiya ta kwashe da dariya tana kallon ta." Yanzu babban Yaya ɗan gayu mai ji da ƙwalisa kike cewa yana wari?"
" Wallahi wari yake yi mini mai haɗe da ƙarni sam ba na so na ji muryar shi,sai na ji warin ya fara tunkaro ni."

Ta faÉ—a tana zuciyarta na tashi saboda maganarsa da ta yi.
" To Anty Juwai ba kya tunanin wannan wata dama ce da za ki yi,amfani da shi ki ƙwato ƴancinki a gurin sa?Kamar yadda yake nuna miki baya son ki ki nuna kin tsane shi fiye da wanda yake miki,ko da kuwa ba gaskiya ba ne a zuciyarki,sabada wani lokacin in ka nuna tsanar mutum ƙarara ko da shi ba ya ƙaunar ka,hakan ya kan sa ka ya ji abin ya dame shi matuƙa,sai ki ga da ga baya ƙauna ta zarge a tsakani"

Ta ce tana kallon ta amma ganin ba ta ce komai ba,sai ta ci gaba da magana tana cewa.
" Allah ki nuna mi shi sam ba kya son ganin sa,saboda cikin da ke jikinki a yanzu zai so ya din ga zama kusa dake yana ririta cikin,ke kuma sai ki yi amfani da damarki ki wahalar da shi,domin duk faÉ—in da yake ba ya son ki ni ina ganin yana yaudarar kan sa ne,saboda in da ba ya sonki,ba zai aure ki ba koda kuwa na kwana É—aya ne,duba ga matsayin sa da na iyayen sa."

" To a yanzu mai kike so na yi?Bayan kin san ni ko kallon sa ba na son yi."Ta ce da ƙosawa saboda ita ambatar sunan sa da take yi,ya ishe ta sai tana jin kamar za ta yi amai.

" Ki wahalar da rayuwar shi sam kar ki nuna tausayi,kuma kar ki bari ya matso kusa dake."Ta faÉ—a ba tare da shakku ba.

" In dai wannan ne kar ki damu fiye da haka zan yi mi shi."Ta ba ta amsa tare da mai da kanta ta kwanta,saboda wani irin bacci da take ji.

Tun Momi na ɗari-ɗari da ita da mutanen,gidan har suka saki suna nuna mata wani irin ƙauna,da abin da ke cikinta.A.m gabaki ɗaya sai ya ji hankalin sa ya tashi,don ya so ace masoyiyarsa ake nuna wa ƙauna ba ita.

A.m ya ba ma Zainab lokaci zuciyarta ta huce sannan ya je gareta,saboda ya san cewa a halin yanzu babu abin da zai ce mata ta kula shi,Daddy ya gaya masa kutu mahaifinta yake so ya kai a ba ta takaddarta,in har A.m ya ƙi sakar mi shi ƴa,yayin da shi kuma ya dage don bai ga abin da zai saka ya rabu da ita ba.

Juwairiya na zaune akan É—aya daga cikin kujerun falon Hajiya Binta,abokiyar zaman Umma,ita da Hamdiya da ba ta daÉ—e da dawowa daga makaranta ba.

Hajiya Binta ta fi kowa tarerayarta a cikin gidan,saboda ta ya ba da hankalinta sosai kuma mace ce mara damuwa da ɗora ma kai jiji da kai,ku san duk ta fi kowa sauƙin kai a gidan.

Fate ne ta yi mata da ga É—an manja sai magi da gishiri,in ban da kwatira ta ciki babu abin da zai saka ta sha.

Hira suke yi sosai da Hamdiya sai Hajiya Binta da take saka musu baki jefi-jefi,yayin da hankalinta yake kan tibi tana kallon shirin daÉ—in kowa.

A.m ya yi sallama ya shigo cikin shadda kalar bula mai kyau.
Daga É—akin mahaifiyarsa yake aka ce mi shi tana nan,ya taho da zumuÉ—insa ya ganta saboda tafiya da ya yi,zuwa cairo har tsawon sati É—aya.

Idanunsa akan cikin shi burinsa ya ga ya fara girma don har yanzu shakkun tana da ciki yake yi ya ƙosa ya ga cikin ya fito.

" A a lale barka da mutanen turai."Hajiya Binta ta faÉ—a tana kallonsa da ya yinsallama ya shigo.Gefenta ya zauna yana shafa kansa.

Bayan ya gaishe ta ya kalli Juwairiya da ta haɗe girar sama da ƙasa,ba tare da ta kalle shi ba ta kauda kanta gefe,tana shan faten duk da ta ji ya fitar mata a rai,saboda ƙamshinsa da ta shaƙa.

Hamdiya ta gaishe shi ta fita Hajiya Binta ta miƙe tana faɗin." Bari na kawo maka abinci Momi ba ta dawo daga gurin aiki ba."

Bai amsa ba ta shige kicin don haka ya ɗago kan sa ya watsa mata wani kallo da ƙyamar a faten da take ci.

" Matar shige ya babyna da fatan ki na kula min da shi?Ba ki bar shi ya yi kukan rashina ba."

Wata uwar harara ta sakin mata kullum a zaman su tana ƙara sanin A..m, baya ƙaunarata kamar yadda yake nuna mata,sam bai gaya mata ya yi tafiya ba.
Ganin taƙi tanka mishi sai ya tashi ya koma gefenta tare da rungumota gabaki ɗaya yan faɗin." Allah Sarki baby na yi missing ɗin ka bari na ji lafiyarka."

Juwairiya da ƙarfinta ture shi gefe tana toshe hancinta,yayin da ta fara kakarin amai.
" Don Allah ka rabu da ni kar ka ƙara matsowa kuda da ni! Ba na sonka kuma ba na son na ji ƙamshin turaren ka.Wallahi wani irin wari kake yi,wanda i don't want to say ga irin sa."

A.m ya zaburo cikin ɓacin rai ya kalle ta da ƙarfi ya ce." Ke kar ki raina mini wayo kin ce ba ƙya son ƙamshin turaren na canza kan dole, yanzu wannan daga Cairo na siyo shi,za ki raina mini wayo ki ce ina wari,bayan duk zuriyar ku babu ba wanda zai iya siyan turaren."Cikin ɗaga murya yake maganar,amma sai ta kalle shi ta saki ɗan ƙaramin tsaki,wanda ya ji ran sa ya ƙara ɓaci sosai.

" Ya akai yi Abdurrahman tana fama da kanta kake É—aga mata murya?"Hajiya Binta ta faÉ—a lokacin da ta kawo masa abinci ta ije a gaban sa.

Hararar Juwairiya ya yi ganin tana mi shi
wani kallo sama-sama yana mamakin rashin kunyar da take so ta fara yi masa.
" Ya zan yi da ita gabaki ɗaya tun da ta samu ciki take yi mini gani-gani,duk turaren da na sa sai ta ce bai yi mata ba,tana son ta nisanta ni da babyna."Da shagwaɓa ya yi maganar da kuma murya mai alamun ɓacin rai.

" Sai ka yi haƙuri ka san sha'anin mata in suna da ciki,wataƙila ba ya yi mata daɗi ne saboda ana fuskantar haka."

Kasa cewa komai ya yi saboda takaici sai hararata yake yi,yayin da ita hankalinta ba shi garesa goruba take ta gwawiya.
" Cinyau kawai daga samun ciki komai kika samu kici,kuma ni takaicina cimar talakawa da kike yi."Ya yi tsaki ya ƙara cewa."Dama duk abin da ka haɗa da talaka sai ya ba ka haushi,yanzu fisabilillahi mai za ki ci da waɗannan cimar wahalar da kike yi,to wallahi ba za ta saɓu ba dole ki canza ni zan tsara miki kalar abincin da za ki ci,kar yarona ya fito yana cin cimar talakawa."
Chapter 75 · 0% Book details