← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 86

Sashe 76

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juwairiya da takaici ya ishe ta tun da yake gaya mata magana bai taɓa damunta kamar na yau ba,ta buɗe baki za ta mayar masa magana,amma idanun Hajiya Binta ya saka ta kasa,sai kawai ta shige ɗakin ta yi kwanciyarta.
" Dole fa sai ka jure dama haka mata suke yi in suna da ciki,in ka yi haƙuri laulayi ne yana fara girma za ta daina." Ta ce masa tana kallon sa da murmushin abin da ya ce." Haba ji fa don Allah wannan abin mai kama da icce take ciki,salon ya karce yarona."Ya faɗa bayan ya ɗauki goribar yana juyata a hannunsa.

Miƙewa ya yi lokacin da take dariyar abin da ya ce." Bari na gaisa da baby na dawo ko hutawa ban yi ba."Ya wuce ɗakin da ta shiga.

Juwairiya na kwance sai ji ta yi mutum ya kwanta gefenta tare da É—ora hannunsa a cikinta.

Kafin ya yi magana wani irin amai ya turnuƙo ta shiga kyara shi a jikin sa.Am hankalinsa ya tashi sosai ran sa kuma ya ɓace,ganin yadda ta ɓata mi shi jiki da amai.
" Wannan wane irin rainin wayo ne?Amai za ki yi mini a jiki."Ya faÉ—a yana wani yatsina fuska tamkar shi ma zai yi amai

ÆŠaga idanunta ta kalle shi a wahalce ta tabbata A.m ba shi da tausayi a zuciyar sa.

Miƙewa ta yi za ta shige bayi ta ce." Na ce ba na son ganin ka balle na ji warin jikinka,ba ciki kake da buƙata ba?Meye na ka da sai ka addabi rayuwata,in na haihu sai ka yi yadda kake so da babyn, amma kar ka ƙara kusa toni,saboda babu wanda na tsana fiye dakai a duniya sa..."

" To tun da ba kya sona sai ki zo ki kashe ni!An gaya miki ni ɗin son ki nake yi,kawai saboda na ji ɗumin yarona nake matsowa garaki.Aikin banza kawai."Ya ce da ƙarfi saboda ya ji zafin tsanar shi da take faɗin tana yi,a tunanin sa ba wannan lokacin ya kamata ta nuna masa ba ta son ya matso gareta ba,saboda yanzu yana buƙatar ya din ga jin girman babynsa.

Ƙoƙarin cire rigar da ta ɓata ya yi ya ije mata a gefenta." Kin san Allah sai kin wanke rigar nan,kuma in mutuwa za ki din ga yi ba amai ba sai na din ga jin motsin babyna saboda babu uban da ya isa ya hanani kuɗi na biya."Ya fice cikin ɓacin rai.Tsaki ta yi ta gyara jikinta ta koma ta kwanta

Bacci ya soma ɗaukarta ta ji ƙarar waya da sauri ta miƙe ganin numbarsa ne ya sa ta datse kiran ta koma ta kwanta,sai dai yawan kiran da yake yi ya sa ta ɗauka ba tare da ta ce komai ba.

" Hello ki na ji na?"Ya tambayeta cikin ƙosawa.
" Umh."
Kawai ta ce mi shi ba tare da ta ƙara cewa komai ba." Na kasa tafiya gida ina falon momi don Allah ki zo ki gaya mini kalar turaren da kike so na din ga sawa,amma ki bar ni na din ga jin lafiyar babyna don Allah."

Ta yi shiru tana tunanin mai za ta ce mi shi sai ta ji ya ƙara cewa." In dai a kwai kalar ƙamshin da ya yi miki,ki faɗa mini zan siye shi ko nawa ne."

" Ni babu ƙamshin da nake so sai humrar da Hamdiya take shafawa."Ta ce da shi.

Kamar tana ganin sa ya ware idanun sa da ƙarfi ya ce." Amma ba ki da hankali ni ne zan shafa turaren humra mata fa suke sawa."A ƙufule kuma cikin muryar tsawa ya gaya mata duk da ya san A.k ya gaya mi shi,ba a yi ma mai ciki tsawa,amma abin da ta ɗauko na rainin da ta ɗauko ba zai ɗauka ba.

" In ba za ka shafa ba dole ne dama ban ce dole sai ka shafa ba,na san ta mata ce, ita take birgeni kuma nake son ƙamshinta,don haka ka sha zaman ka,ba dole sai ka zo in da nake ba ko ka taɓa jikina,don yanzu kamar yadda ka tsane ni baka son wallahi na fi ka tsanar ka."

ÆŠif ta kashe wayar har wani huci take ita kanta ta san ta koyi tsiwa,wanda ta rasa gane dalilin haka kowa ma haushin sa take ji.

A.m da ya yi sagalo da waya a hannunsa tsananin mamakinsa ya kamata,tunaninsa yaushe ta canza.

Hamdiya ya ƙwala ma kira sai ga ta ta fito da sauri." Don Allah sis turaren da na shafa ba shi da daɗi?"Dariya tambayar ta ba ta don ta san kanun,amma sai ta ƙunshe dariyar ta kalle sa yadda ya ci magani ran sa a ɓace ta ce."A a yana da daɗi Ya A.m duk turaren a kwai daɗi da fatan ka yi mana tsarabar sa?"

Tsaki ya saki." A a wancan ƴar rainin wayon ta ce wari nake turaren bai da ƙamshi,tun da ba ta son turaren zan kawo miki sai na canza wani,yauwa ta ce turaren da kike shafawa take so humra ina son ki ba ni."Ya faɗa ba don yana so ba ran sa na suya saboda ta ce yana wari,kamar shi duk wanka da gayu da yake yi.

Duk yadda ta so ta ɓoye dariyar sai da ta dara ganin yadda ya yi." Mai za ka yi da humra ta mata ne f.."
" Ya kike so na yi kwata-kwata ta hanani in ji É—umin babyna ni kuma ba zan iya zama ba tare da jin É—umin shi ba."Ya faÉ—a ba tare da ya ji kunyar ta ba.

Ganin yadda ya yi maganar ba wasa sai ta shige É—aki tana dariya ta kawo masa.

" Bari na shafa sai na je."

Ya faÉ—a yana sinsinar kwalbar turaren amma bai ji wani daÉ—in da take da shi ba.

" Da ka yi haƙuri sai ka canza kaya ka shafa ka dawo kar ta ƙara wani amai,tun da a kwai ƙamshin wancan turaren da ba ta so a jikinka."Ta ce da shi.

Ficewa ya yi ya nufi motarsa ba tare da ya tanka mata ba,shi a ganin sa Juwairiya raina mi shi wayo ta yi,shi ya sa take faÉ—in yana wari.

Bai zo gidan ba sai washegari gabaki ɗaya kunya ta kama shinda ya fara shafa humrar sai ya ji sam ƙamshinta ba ta yi masa ba,amma kan dole ya shafa ya ɗauki wayarsa da ya gama tura ma Zainab tsaƙon text na ban haƙuri da gaya mata dalilin da ya saka ya aure ta,ya sauko ƙasa.

A.k ya gani zaune a falon wanda tun ranar da bin ya faru bai ƙara ganin shi ba,har ya yi tafiya ya dawo sai yau.

Kamar yaro ya duƙa lamun yana ba shi haƙuri tare da ƙama kunninsa duka.

A.m da ke saukowa yana ganin sa ya ɗaure ya kauda kan sa don ya ba shi matuƙar haushi,wato da kashe shi za a yi sai dai a kashe shi kenan,shi ya gudu don haka ko kallon in da yake bai yi ba ya kama hanyar fita

Da gudu A.k ya ruga ya kama hannunsa yana roƙonsa tare da yi masa dariyar ƙeta.

Da takaici ya ishe shi bin shi ya yi da gudu suka kama tsere-tsere kamar wasu yara,har A.m ya riƙe hannunsa tare da ɗaukar filon kujera,ya din ga maka masa a jiki shi kuma yana dariya.

Da ya gaji sai ya faÉ—a jikinsa suna haki can kuma suka saki dariya suka tafa.
" Wato ka gudu ka barni duk abin da zai faru ya faru ko?Wallahi ban san ba ka da mutunci ba sai a lokacin sam ba ka cika aboki ba."

Dariya ya yi." Ah to ya kake son na yi kaga laifina haka kawai yadda Abba ya harzuƙa so kake na ja ma kaina?Ai tsunttsun da ya ja ruwa...."

" Aiko na sha mari sosai kumatuna har sai da suka yi."Ya faÉ—a masa jin abin da ya ce.

Dariya suka ƙara yi sannan A.m ya miƙe." Well zan je na ga babyna ka san mun shiga da ga ciki,yanzu ina da wanda zan kula da shi so yanzu lokacin sa ne."

" To sabon shiga ofis nake son na je saboda tsoron kar mu haÉ—e na fara zuwa gidan ka sabon shiga."

" Ni fa ƙamjin turaren humra nake ji na mata ko Zainab ta dawo ne?"A.k ya ce yana wani shinshine-shinshine.
Bugu ya kai masa a baya." Gulma babu kyau ban sani ba."Dariya ya yi ." Allah da gaske nake yi kamar irin na Maman Najwa da take shafawa,na sani ko lallaɓo abin ka ta dawo."Ya ce da shi lokacin da ya buɗe mota zai shiga.

" Ba ita ba ne wancan Æ´ar rainin wayon ce,wai ba ta son ko wane irin turare sai wannan turaren,har yanzu cewa take ina wari ka san Allah bacin cikina da ke jikinta da sai ta gane ba ta da wayo da take faÉ—in ina wari."

Dariya sosai ya yi." Ikon Allah sai haƙuri haka yawancin masu ciki suke yi,amma mafi yawancin mazaje ba sa ganewa sai suna ganin kamar ƙarya suke yi,bayan da gaske iya gaskiyar su suke faɗa.".
Rufe motar ya yi." Ok bari na je mu gaisa sai na shigo."Ya ta da motar sannan A.k ya wuce gurin motarsa.

A.m ya yi sallama a cikin falon mahaifiyarsa wacce ya tabbata tana gurin aiki a wannan lokacin,kamar yadda ya yi tunani haka ne kuwa don babu kowa sai yan aiki da suke ta hidimar su.

Kai tsaye ɗakin da ya san take ya nufa a ƙofa suka kusan karo, da Hamdiya ta ta fito da gudu da kofin tea a hannunta tana kurɓa.

Matsawa ya yi gefe ganin yadda take sauri kamar za ta tashi sama." Barka da zuwa Ya A.m na yi latti sosai so by."

Ta fice ba tare da ta bari ya amsa gaisuwan ba."Shirmanmun yara kawai mutum ya san yana da lecture amma ya tsaya yana ɓata lokacin sa."Ya ce tare da tura ƙofar ɗakin.

A.m da ya yi turus a tsaye gani tana bacci ya yi kamar ya juya,saboda abin da Hamdiya ta rubuto masa har da ba a tashin mai ciki da ga bacci.

Sai kuma ya fasa ya yanke shawarar ya gaisa da shi kawai a hakan.
Chapter 76 · 0% Book details