← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 86

Sashe 42

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana biyu Zainab ta takura kanta ta hana zuciyarta fita don ta faranta masa,saboda ta ga canji kwana biyu ya na wani shareta,da ta yi masa magana zai hayayyaƙo mata kamar zai cinye ta.

Sai ta danne zuciyarta ta ƙi fita ko ina daga aiki sai gida ta na ba shi kulawa,wanda da ƙyar ta samu ya sauko suka koma rayuwar su kamar da.

Juwairiya kullum za ta yi musu abinci mai rai da lafiya su ci suna yabawa a zuci,don girkinta ya na matuƙar ƙayatar da su duk da babu wanda ya taɓa yabawa,amma har ɗan ƙiba sai da suka ƙara kaɗan.
Sai dai fa mai hali ba ya fasa halin sa Zainab a daddafe ta yi Æ´an kwanaki a gidan, wadda take jin kamar ta na gidan yari duk da irin kayan alatun dake gidan amma saboda ta saba fita sam komai ba ya burgeta.

Zaune take a É—aki ta kulle kamar yadda ta saba duk lokacin da za ta yi rawa ta tura.
Tasha ado da wasu riga da wanda na ƴan kanti masu kyau kalar pink,wandon bai kai ƙasa ba.
Gyara gashinta ta yi ta fara rawa cike da ƙwarewa ta tura ta na murmushi don ta san yanzu za ta ga ruwan comment da like.

Ilai kuwa ta na turawa aka fara liking ta na kallo ta na murmushi,ta na shirin sauka wata numba da kullum take mata sallama a facebook,ta ƙara yi duk da ba amsa wa take ba amma ba ta gaji ba,ku san kullum sai ta yi mata sallama.

Tsaki ta yi ta sauka da ga online gabaki ɗaya ta na mamakin wannnan numba da take damunta,saboda ita in dai ba ta san mutum ba ba ta magana online,sanin cewar ita tauraruwa ce a yanar gizo so ba ta da lokacin da za ta tsaya ta na kula su,amma a ranta ta ji ta na son ta amsa sallamar don ta ji mai ke tafe da ita,saboda ta duba profile ɗinta ta ga ita ma ba ƙaramar mace ba ce,don da Barrister Mardiyya take bearing.

Murmushi ta saki tare da ije wayar da sauri daidai lokacin da A.m ya murɗa ƙofar ya shigo,sai ta kama hannunsa ta riƙe ta na dariya tare da kashe murya ta ce.
"Barka da dawowa yanzu na ji ƙarar shigowar ka, ina wanka ne shi ya sa ban fito ba."

Dafe kan sa ya yi ya janye jikin sa ya zauna akan gefen gadon ya na kallonta tare da ƙoƙarin rage kayan jikin shi.

"Babyna na gaji matuƙa kamar kai na ciwo yake son ya yi,yunwa nake ji kawo min abinci in ci anan bacci nake son na yi."

Ya faɗa tare da kwantawa ya miƙewa a kan gadon don jikin sa ko ina ciwo yake masa.

Zainab ta É—an canza fuska ta ce " Na É—auka za ka ci abincin a dinning ne fita nake son na yi,kuma Juwairiya ta riga ta shirya abinci meye sai ka wahalar da mutum gurin É—aukowa."

Ta ƙarashe maganar cikin yauƙi da yanga tare da ɗaukar wayarta,da take kusa da shi don ta tuna kamar ba ta sauka a online ba,sai dai kuma da ta tuna ba ta taɓa ganin ya ɗauki wayarta da sunan ya duba ba,ko kuma ya ce zai yi wani abu.

Gaban sa ya faÉ—i da ta ambaci sunan Juwairiya ba zai ce ya manta da ita ba,amma sam ba ya son ya ji sunan sai ya ji haka kawai gaban sa ya faÉ—i.

" Zainab ba na son rainin wayo ni da gidana da kuma matata ba ni da ikon na ce ga in da zan ci abinci?Kuma da kika ce wancan za ta kawo min,to ba ita nake so ba matata wacce nake da iko da ita nake son ta kawo min,kuma ki je ki dawo bacci nake son mu yi babu in da za ki."

A ɗan kausashe ya faɗa ya na harararta wanda ya zamar masa ƙa'ida,kamar wani mace in dai aka gaya mishi ba daidai ba, sai ya yi harara.

Yarfe hannunta ta yi ta ije wayarta tare da fara ƙorafi ta na ce wa." Haba Hubbi kai ma ka san na yi ƙoƙari ban je ko ina ba,na baka lokacina na tsawon kwanaki.

Ta ɗan matsa kusa da shi ta ce." Yau fa bikin ƙanwar ƙawar Anty Fati ake yi,ka ga ai ya zama dole na je ko?"Ta tambaye shi tare da tsare shi da ido.

Kallonta ya yi bai ce komai ba sai ya miƙe ya kunna tangamemen tibin da ke ɗakin ya riƙe remote ya ce.

" Dole ki je mana gayyar soÉ—i ni dai na gama magana ba in da zaki,ke ko kishina ba kya yi ki ta sa Æ´an aiki suna kawo min abinci,ko tunanin in canza miki ba kya yi."
Kusa da shi ta zauna ta na faɗin." Yarda da kai ne Hubbi Allah in za a ban kur'ani zan iya rantse wa a kan ka,sam ba ni da haufi ko da ba ka yi min alƙawarin ba za ka yi min kishiya ba,hankalina ba zai tashi ba saboda ban taɓa jin ka yaba wata mace ba."

Ta ɗan kalle shi da murmushin yadda a fuskarta ta ci gaba da ce wa." Kuma duk abin da nake yi ai ba na zuwa da ƙawayena waɗanda ba su da aure gidana saboda tsaro."

Dariya ya yi jin abin da ta ce ya miƙar da ita ya na faɗin." Ok Babyna ina godiya sosai da yardar da kika yi min,kuma ke ɗin zazzafa ce ta ko'ina ga kyau ga ilmi da da tarin baiwa kala-kala,ina gaya miki ba wata sai ke a nan."

Ya nuna mata ƙirjin shi da da babbar yatsar shi dariya suka yi ta yi huggin ɗin sa,sannan ta ba manna masa kis ta ruga da sauri don ta ɗauko masa abincin,duk da ranta bai so haka ba amma fitar ta ta rantse sai ta fita.

Don haka ko da ta dawo haka ta ci gaba da lallaɓar sa har ya amince saboda ta dame shi,kuma bacci yake son ya yi da sauri ta ɗauki ɗan gyalen ta ta fice daga gidan.

Bayan ya ci abinci ya ɗan miƙe tare da ba da tazara kafin ya kwanta,saboda abincin da ya ci sannan ya kwanta bacci.

Juwairiya ta warke sumul bayan ɗan ciwon kwana biyu da ta yi ta zage ta na ta aikinta,cikin ƙosawa a ranta ta na addu'ar Allah ya sa ta samu cikin ya ɗauke ta daga gidan,ganin yadda Zainab ta mai da ita baiwa,shi kuwa daga ranar bai ƙara neman ta ba.

Ta na falo aiki take yi goge su tibi da abin da ya kama ta a goge a falon take yi.

Sosai ta mai da hankalinta a kan aikin da take yi ta na son ta gama ta É—ora girkin abinci.

Ya fito daga ɗakin sa ya na sanye cikin doguwar riga na jallabiya mai ruwan madara,wayar sa riƙe a hannun sa sam fuskar sa babu fara'a.

Juwairiya ta saki ɗan ƙaramin tawul ɗin da take goge tibin da shi za ta ruga ganin ya fito, amma sai ya yi maza ya riƙe mata hannu tare da kiran sunan ta.

Tsayawa kan dole ta yi tare da juya masa baya cikin tsananin kunyar sa.

Juyo da ita ya yi da murya mai sanyi ya fara magana.
" Ban san tunanin ki in da ya tafi ba tun daga ranar kin ɗauke wuta kin mai da ni kamar wani dodo,bayan kin san wannan kamar sharan fage ne akan tsarinmu har zuwa randa zamu cimma haƙar mu,kowa ya huta da wahalar da kan sa mu samu maslaha a rayuwar mu."

Ta na son ta yi mishi magana irin ya faɗa ta amsa mishi ko da maganar da ya yi mata babu daɗi,amma kuma ta na matuƙar jin nauyin sa wanda ko haɗa ido a bisa kuskure take yi.

Sai ta kauda fuskarta a ranta ta na faɗin." Kai ne kake son ka cimma haƙar ka,amma ni ina son na kasance da kai har abada A.m ina sonka burina ka ɗauke ni daga gidan ka nima ka sama min ƴanci na rayu da kai duniya ta san mijina ne kai."

Amma a fili sai ta yi ƙasa da kanta ta na kallon ƙafafun sa suke da kyau da sha'awa.

" Ke ni fa ba na É—aukar rainin wayo na yi ta miki magana kina sharewa,ki buÉ—e baki ki yi min magana kuma ni ban ce ki yi min kuka ba."
Ya faÉ—a ganin ta yi rau-rau idanunta sun kawo ruwa.

Kamar umurni ya ba ta sai ta yi ƙoƙarin mayarwa ta na son kallon sa.

A.m ya saka hannun sa ya shammace ta kawai ya cire mata hijabin jikinta ya na faÉ—in.

"Ni fa yanzu ban ga abin ɓoye-ɓoye a tsakaninmu ba bayan kin san ke ɗin matata ce,wanda aure ya ba ni damar mallakarki a gurin makwaɗaicin ƙanin mahaifinki."

Ta kauda kanta ba ta ce komai ba sai kuma ta saka kuka.
Dunƙule hijabin ya yi ya jefar ya ci gaba da faɗin."Anyway yanzu dai ni maigida na ba da umurnin in dai daga ni sai ke ne a gidan,to amaryar wucin gadi ƙar ta ƙara saka hijabi ki bari sai in wanda kike jin kunya ta dawo sai ki saka abinki,amma ni da ke ai ba kunya tsakaninmu ko."

Ya gama maganar ya na tambayarta ya na wani irin murmushi mai kama da na mugunta ko ya na son shirya wani ƙeta.

Juwairiya ta ji wani irin sanyi a ranta karan farko haɗuwara da A.m yau ne rana ta farko da ya yi mata murmushi,duk da murmushin na sa da wata manufa ya yi amma hakan ya ba ta matuƙar citta a ranta.

Ta matsa daga kusa da shi ganin irin ƙare ma jikinta kallo da yake ta fara tafiya a hankali.
"Juwairaah."
Ta tsaya cak daga tafiyar da take yi amma ba ta jiyo ba,shi ya taho har in da take ya matsa kuda da kunninta ya ce " Ina zaki matar wucin gadi ai ban gama magana ba,kin san ya kamata a É—ora daga in da aka tsaya ko."
Chapter 42 · 0% Book details