← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 86

Sashe 66

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai tana tunanin yadda za ta iya danne zuciyarta,ta zauna da Juwairiya bayan ta gane amanarta suke ci,duk da A.m ya yi mata rantsuwar yana shan magani ne saboda ita, amma kuma bai ƙaryata numbarsa a wayar Juwairiya ba,sai dai ya nuna sam bai san zancen ba wataƙila son sa take don kwanaki ana kiran sa da baƙuwar numba,bai dai taɓa ɗagawa ba ne shi yasa bai fahimci komai ba.

Zainab ta gane sam ba za ta iya rayuwa babu shi ba,amma dole ta canza zaman su domin sai ya gane kuran sa,ita kuwa Juwairiya Momi ta ce ta bar lamarinta a hannunta don sai ta yaba wa aya zaƙinta.

Lantana ta shigo gidan da mamakin ƙofar a buɗe duk da ta ga motar A.m a gidan,amma ta san ba' abarin ƙofar falon a buɗe.

Tura ƙofar ta yi ta shigo tana ƙarema gidan kallo yadda yake tashi da ƙamshi da gyara komai tsaf,jikinta ya bata a kwai mace a gidan.

Tsaye ta yi tana É—an tunani sai kawai taga Juwairiya ta rugo da gudu daga sama tana dariya,jikinta daga ita sai yar bes fara da wando fari tirikwata wa da A.m ya siyo mata da suka fita,saboda shi yana koyi da hadisin ma'aiki wanda yake mana koyi da saka fararen kaya.

Da gudu take saukowa tana dariya shi kuma ya biyo ta cakulkuli yake mata wai kan dole sai ta yi mishi kuka yaga hawayen banza.

Kamar yadda Lantana ta yi tsuman tsaye tana kallon su haka suma suka zuba mata ido cikin firgici.

TO FA NIMA IDANU NA ZUBA MUSU TARE DA BASU LOKACI DOMIN NA GA REACTION ÆŠIN SU

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 29*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Juwairiya kunya ta kama ta matuƙar gaske ji ta yi kamar ta nutse a ƙasa,juwaya ta yi za ta koma ciki,amma sai A.m ya janyo ta tare da haɗa ta da ƙirjin shi.

" Ke! Wace irin mahaukaciya ce da za ki shigo gidan ma'aurata kai tsaye sai ka ce É—akin gidan ku."

"Lantana jikinta ya kama rawa kamar mazari saboda tsawar da ya daka mata,ta yi mugun firgita ba ta gane abin da ya ce ba.

" Ka yi haƙuri yallaɓai wallahi ban san ka na ciki ba,kuma Hajiya Zainab ta ce na zo na gyara gidan za ta dawo."

Ta faÉ—a jikinta na rawa kanta na asa ta na mamakin abin da ta gani don ta firgita.

A.m ya yi farin ciki sosai jin abin da ta ce sai ya ɗan ture ta daga jikinsa,ya kalli Lantana da har yanzu idanunta a ƙasa suke,ba ta son ta ƙara ganin abin da ta gani,domin ƙila ƙarya suke mata.

" Ok sai ki je ki yi aikin ki munafuka na sha mamaki da Zainab ta tunume ni akan ina tare da Juwairiya,a she ke ce munafukar da take son raba aure.
Wallahi kin ji na rantse miki in har kika yi gigin faÉ—a mata abin da idanun ki suka gani,kaf Æ´an gidan ku ni ne ajalin su don bom zan siya na tashi gidan."

Ware idanunta ta yi tsananin tsoron sa ya kamata saboda idanun sa sun tabbatar mata da zai yi fiye da haka.

" Ba ke kin iya munafunci ba to bari na ƙara miki da abin da zai kashe ki,don ba za ki iya faɗa mata ba duk munafuncin ki saboda in ban kashe ki ba,to ita za ta yi ajalin ki kin ga gulma ta yi riba kenan."

Ya ce da ita ya na zare mata ido domin haushi take ba shi,tun da ya ji ita ta faÉ—a mata komai,ga shi yanzu ta korar masa da matar so.

"Juwairiya matata ce wanda na aura a bisa wasu dalilai da ba zan gaya miki ba,saboda bai shafe ki ba."

Ya ƙara matse ta sosai a jikin sa kiss ya sakin mata a kumatunta,ya na mata wani irin kallo da ya saka ta kauda idanunta saboda kunyar Lantana.

" Kin ga in ta dawo sai ki gaya ba mata yau ƙin ƙara gani ba kuma iyakan runguma ba,ki sanar mata duk abin da kika gani kar ki rage."

Lantana da sauri ta shige kicin tare da rufe ƙofar.

" Innalillahi na shiga uku!"

Ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yayin da kanta ya kulle ta rasa in da za ta fara tunani.

" Wallahi wannan mutumin ya rikita ni na rasa mai zan fara tunanin,a halin yanzu zuciyata ba za ta iya fahimtar komai ba,domin ya saka ni a cikin ruÉ—u."Ta ce yayin da ta É—ora hannu akanta.

" Da gaske ya ke faÉ—in matar sa ce ita?A 'a lamarin nan a kwai rikitarwa! Ji fa yadda ta koma tamkar wata gilas,saboda tsabar kyau kai Zainab shashashar mace ce,wai ta je hutu ai kuwa ki dawo za ki ga sakamakon hutu."

" Wa ni ai komai na ga kuna yi ba zan iya gigin gaya mata ba,haka kawai ku da holewa ni da shan bugu.Kai amma fa A.m ƙarshe ne gurin rashin mutunci don ko kaɗan Zainab ba ta yi tunanin ta na gidan ba."

Irin maganar da take yi a zuciyarta kenan ta buɗe ƙofar a hankali ta na leƙen su,sai ta ga sun ƙara rugawa da gudu sun yi ciki.

" Allah ya kai mu ki dawo gidan nan za mu
sha kallo!Allah ya sa kar ki yi shigowar dare in ba ma idanuna abinci,sai ki gane sakaci kika yi ko halin maza A.m yake nuna miki."Ta faÉ—a sannan ta kama aikinta zuciyarta cinkushe da tunani kala-kala.

Bini-bini za ta leƙa ta na kallon sama amma sai ta ji shuru kamar bacci suka yi.

" Ha ina tausayin ki yarinya ba ri Zainab ta dawo."Ta ce ta na aiki cikin mamakin lamari da al'ajabi.

" Humh namiji bunun ƙaya."

Abin da take ta nanatawa kenan a cikin zuciyarta.

A.m ya rungume hannun shi ya na kallonta da ta kwanta akan cinyar shi,ta ɗora filo a ƙirjinta idanunta lumshe kamar ta na bacci,sai dai a zahirin gaskiya ba bacci take yi ba.

Zuciyarta cinkushe da kishi da tunani jin Zainab za ta dawo,domin a yadda take jin son sa da kishin ta ba za ta iya ɓoye kanta ba,kamar yadda ta yi a farko ta na jin ko sama da ƙasa za su haɗe za ta nuna kanta a wannan karon.

Kamar yadda take tunani shi ma haka zuciyar sa take cinkushe da tunani,ga shi ya gagara samo mafita.

Duk da cewa zuciya da gangar jiki sun yi kewar Zainab,amma in ya tuna za ta dawo gaban sa yake wani irin yankewa ya faÉ—i.

Ya sani a yanzu babu wanda zai kalle ta yabce ita yar aiki ce,duba ga yadda ta koma tamkar wata tarwaÉ—a.

Ya na ta tunanin ko ya É—auke ta daga gidan sai dai ya na jin ba zai iya jure rashin abincinta ba,saboda har yanzu ya kasa iya cin abincin Lantana.

Wayarsa ya zaro ya gwada wayar Zainab da ya daina kira,saboda ƙin ɗauka da take yi.

Sai dai ringing É—aya ya ji ta amsa tare da sakin kuka.
" Ka daina sona A.m ban taɓa tunanin a kwai ranar da zan yi fushi da kai ka ƙyale ni ba."

Ta amsa daga ɓangarenta ta na wani irin kuka da yake tafarfasa masa zuciya.

Tsam Juwairiya tamiƙe daga jikin sa ta fice daga ɗakin ba tare da ta kalle shi ba,yayin da zuciyarta ke mata luguden bugu na kishin sa.

Binta da kallo ya yi ganin ta canza kalar fuskarta kamar ba wacce ya sani ba.

Sai da ta fice daga É—akin ya saukar da nauyayyar ajiyar zuciya.

" Ya kike son na yi kin mai da ni kamar wani ƙwallo don kawai kin ga Allah ya jarabce ni da son ki?Kawai na ba ki dama kije duk abin da kika yi ninya ki yi,ni dai har yanzu ba zan fasa gaya miki ina sonki ba."

Ya ce da ita ya na jin tsananin haushinta da kuma fargabar abin da zai faru,domin ya na ji a jikin sa kamar lokaci ya yi da zai gaya mata zaman Juwairiya a gidan su,don su daina samun saɓani,duk da ya san zai sha wahala kafin ta amince.

" In har ka na sona da gaske A.m ka daina kawo rigima a cikin aurenmu,sannan ka tuna da alƙawarin da ka yi min don Allah karka canza."

Shiru ya yi bai ce komai ba ya rufe bakin sa da hannun sa ya na jin saukar kukan da take yi.

" Ka yi shiru ba ka ce min komai."Ta faÉ—a cikin muryar kuka.

" Mai kike son na ce miki Zainab wane irin halacci ne ban yi miki ba! Ki dawo a kwai wata magana mahimmanciya wace za mu tautauna,kuma in kika fahimce ni in sha Allahu ba za mu ƙara samun tarnaƙi a aurenmu b."

" A.m a kwai matsala ne don Allah ka faÉ—a min?"

Ta tambaye shi da zaƙuwa jin muryar sa ta canza." Babu kuma kar maganar da na ce miki za mu yi ya ɗaga hankalinki domin alkhairi ce."
" Ok to shikenan baby ba matsala,amma fa ka canza gabaki É—aya,domin da ace babu wata matsala cewa za ka yi in jira ka mu taho tare."Ta ce da shi da wata kalar murya.

" Wataƙila da izinana kika tafi?"

Ya ce da ita a ƙufule kawai sai ta ji ya datse wayar, a lokacin da take faɗin.
Chapter 66 · 0% Book details