← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 86

Sashe 81

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusa da ita ya zo ya tsaya yana ƙare mata kallo." Ba na hana ki kiran sunana gatsai babu girmama wa ba,ko banza yanzu kya karrama sunana da Baban baby."

Kallon shi ta yi a yatsine ta ce." Ba wani Baban da zan kira ka, sai ka bari wadda za ka ba wa yaron in ta dawo ta rinƙa ce maka.Kuma ni ba wannan ba ciyo ya ƙare shi nake son ka siyo mini."

Gefen ta ya zauna tare da lakuce mata hanci ya shafa cikin wa da da sauri ta ture hannunsa tana hararar sa.Hannunsa ya ware ya ce.

" Allah ina roƙon ka ka fito da baby lafiya na huta da wannan yarinyar da ta addabi rayuwata."

Taɓe bakinta ta yi ta ce." Oho koma me za ka ce ka ce amma ni buƙata ta ka siyo mini ciwo."

" Amma na gaya miki ba lokacin sa ba ne Juwairiya,Allah ko waɗanan da kika ga na samo miki wani ƙauye can aka yi mana kwatance ki tausaya wa rayuwata ki kalli yadda na koma."

Ya faÉ—a da muryar sanyi da yake bayyana tausayi don kawai ta tausaya mi shi.

" Ashe ma a kwai in da ake siyar wa ai na É—auka babu shi ne Allah ko bangon duniya sai ka samo mini."Ta yi maganar cike da shagwaba tana game a wayarta.

"To ba in da za ni don na lura abin naki rainin wayo ne."Ya ce tare da miƙewa zai fita.

Juwairiya sai ta kama rigarsa ta riƙe za ta fara kuka." Allah sai ka siyo ko da yake ba zan damu ba,ai na ji an ce in mai ciki ta ga abu tana so ba a siya mata ba, yaron da tabon rowa yake fitowa kuma jikinsa baƙi-baƙi yake yi,sannan ka ji abin da Hamdiya ta ce cikin kuma na iya zubewa,gara ni zan iya ƙara wasu da yawa kai kuwa fa ƙila ni in na yi aure ƴan biyu zan fara haihuwa masu kyau ba irin ka ba babu kyau sai koɗaɗɗiyar fuska..."

Buge bakinta da sauri ya yi kuma ta ji zafi ta sa kuka.

" Mara mutunci kawai da aurena kike faÉ—in za ki auri wani ki haihu."

Ya ɗaga kafaɗarsa yana mata murmushin ƙeta ganin yadda take hawaye saboda ta ji zafin buge mata bakin da ya yi.

" Ji be ta mai hawayen banza har sallar dare zan rinƙa yi kar yarona ya gado ki,saboda in zai rinƙa irin kukanki ƙila na rinƙa tunaki in mun rabu."

Taɓe bakinta ta yi tare da sakin rigar shi ta koma ta zauna ta ɗauki yalon Bello ta ci sannan ta ce." Kai har a kwai abin da zai saka ka tuna da ni in mun rabu,ni kam na ƙosa mu rabu na huta da addabar rayuwata da kake yi."

A.m da ya tuna Zainab za ta dawo sai ya matsa ya zauna kusa da ita tare da É—aure fuskar shi.

" A kwai maganar da zan yi dake kuma mai mahimmanci ba na wasa ba,don na lura yanzu na sakin miki fuska gabaki ɗaya kin raina ni.Matar gidan za ta dawo duk wannan iskancin ki ije shi a gefe,saboda kin san ba za ta ɗauka ba yadda kike gara ni kamar wani ƙwallo,sannan maaganar turare ya tsaya iya ɗakinki dole zan canza wanda na ke shafawa domin na faranta ranta."

" To ni dama na yi maka dole ne in dai ka shafa wani ba wannan ba kar ka sake kazo kusa da ni."Ta ba shi amsa kai tsaye jin abin da ya ce.

Bai ba ta amsa ba ya ɗora da cewa." Maganar tashina da daddare da kike yi na yi miki girki zan daina ke ko da safe ne,saboda kin san Zainab ba za ta ɗauka ba,don tun da na ke da ita ban taɓa shiga kicin ba na yi girki,da tashina da kike yi na zauna zaman jiran ki a falo ƙarshe sai dai na kwana anan.Kin san Allah kika yi wannan gigin sai na ɓata miki rai."Ya ƙarashe maganar da nufin gargaɗi.

" Wannan kuma bai shafe ni ba abin da na sa ni in har baby ya ce zai ci abinci Allah sai na zo na tashe k.."

" Juwairiya ranki zai ɓace fa ki kiyaye ni."

Da kaukausar murya ya katse ta jin abin da ta ce sai kuma ya duƙa a gabanta duk da bai so yin haka ba." Don Allah ki tausaya mini kamar yadda na ke son yaron jikin ki haka na ke son Zainab."

Wani iri ta ji babu daɗi a ranta abu mai kama da kishi wanda ba ta gane hakan ba ya tsaya mata a maƙogaro sai ta miƙe da sauri ta shige cikin ɗakinta.

" Momi ki barni Allah yau a gidan Mijina zan kwana,saboda na lura ba zan iya rayuwa in babu shi ba,kuma ya sanar da ni duk abin da ya yi saboda ni ne yana tsoron kar watarana a tilasta mi shi, ya yi aure ya sa ya auri yar talakako in ce ya siye ta don ta haifa mana baby."

Zainab ce take gaya wa mahaifiyarta maganar saboda ƙwace wayarta da ta yi jin suna hira da shi.

" A she ke banza ce ke anya nonona kika sha lallai na yadda ba ki da hankali."

Ta numfasa saboda takaici da ya rufe mata ido ta ci gaba da cewa." Don ya gaya miki wannan ƙanzon guregen kika yadda da shi,karki manta namiji ne fa shi,yau na yadda ba ki da hankali karki bari a ƙwato miki ƴanci ki koma gidan na sa da kanki za ki dawo kina kuka,don wallahi zaman gidan sai ya so ya fi ƙarfinki."

Momi ta ce cike da takaicinta saboda ta yi-ta yi da ita su je gurin Malami,amma ta bijire mata.

" Ko ma me za ki ce ki ce amma ni ba zan je na ɓata aurena ba,na san A.m na sona kuma da zarar ta haihu za ta bani ɗan ta koma in da ta fito,kuma yanzu a gidansu ya ije ta."

Momi da ta harzuƙa kamar ta kwasa mata mari take ji." Au haka kika ce ni da na so a zubar da cikin ne,saboda barin a haife shi kamar wani babban kuskure ne za ki yi."Ta ce mata tana son ta shawo kanta.

" No Momi barin sa ya ga ƙwansa shi zai saka ya samu natsuwa, kin san in son sa ba zan so na ga yana cikin damuwa ba,kawai ya haihun hakan zai fi mana samun kwanciyar hankli."

" To ai ke kika sani duk abin da ya ƙara faruwa karki ƙara nema na ki je ciwon so ya kaiki ya baro."

Ranar da A.m ya je É—aukota ya sha faÉ—a sosai a gurin Daddy.
Daddy ya yi masa faÉ—a sosai kamar zai kai mi shi duka har ya É—ora da cewa." Ka ji na rantse maka don kawai Zainab ta aikata kuskure a rayuwarta,wanda mun yi mata faÉ—a sosai da kuama kunyar mahaifinka da na ke ji,da albarkacin son ka da take yi maka,amma wallahi kulle ka zan yi sai igiya ta yi rarara.
Sakaran banza kawai ka rinƙa dukan mace goto-goto da kai ba ka jin kunya,tun da nake da ita ban taɓa saka hannu na buge ta ba sai kai,an ce maka jaka na haifar maka."

Ya numfasa tare da ɗorawa cikin zafi sa ƙunar zuciya na saboda ƙara dukan shalele da ya yi.

" Na so ka sakin mini yarinya na tura ta in ingila ta yi rayuwarta a can,ai ka san kai kai ke da asara,saboda duk wanda ya yi rashin Zainab ya tafka babbar asara wallahi,ga kyau ga kuÉ—i da ilmi."

A.m shiru ya yi don haka A.k ya ƙi rako shi don ya san dama zai ga rashin mutunci.

Haka suka shanya shi kusan rabin awa yana jiran ta har ya yi fushi ya raya a zuciyarsa in har ba ta fito ba,minti biyu ya yi zai tafi,sai ga ta ta fito tana cika tana batsewa da tiren kayan lambu a hannunsa.

Ware hannunsa ya yi har ta taho za ta faɗa sai kuam ta duƙa tare da sakin kuka sosai.

A hankali ya ƙaraso ya ɗaga ta ya rungume." Is ok babyna na riga na gaya miki duk abin da ya fa.."Katse sa ta yi cikin kuka.
" Dole na yi kuka sosai kamar yadda kake rungume ni a faffaɗar ƙirjinka haka kake mata gaski.."

" Wa ya gaya miki? ai irin wannan yana faruwa ne don kana son mace,ni kuwa kin ga sam ba na sonta,kawai na tsaya na zaɓo mai kyau don kar a haifa mana baby mummuna."Ya ce da tsigar rarrashi."

Tsarata ya ci gaba da yi yana gaya mata kalamai masu kwantar da zuciya,har ta manta komai ta miƙe akan za ta ɗauko kayanta su tafi.

Momi kuwa ko kallonta ba ta yi saboda ta yi fushi da ita sosai,sai haÉ—a kayanta take yi cikin sauri kamar wacce za ta tashi sama,ko da ta yi mata sallama tsaki ta yi ta juya mata baya.
A.m dake tuƙi idan ya juyo ya kalle ta sai ta balla masa harara ta saki tsaki tare da kauda kanta.

Wani irin fargaba yake damun sa in ya tuna Juwairiya na gidan,kuma ya san Zainab ba za ta yadda ba,sannan a halin yanzu ba zai yadda ta yi nisa da shi ba,saboda in ya ga É—an cikin da ya fara fitowa sai yaga kamar É—ansa yake gani,uwa uba ga É—umin jikinta da yake masifar so ya ji sa a kusa da ita,duk da yaki ce sa da take yi.

" Zainab ina son za mu yi magana don Allah ki natsu ki fahimce n ."
" To mai kake so ka gaya mini yanzu kuma?Don Allah ka ƙyale ni na gaji da yaudara ta da kake yi kana gaya mini kalaman bakinka na yaudara."

Ta katse shi da murya mai ƙarfi saboda haushi ya ke ba ta sosai ji take kamar ta shaƙe shi,domin ya ha'ince ta ya ije mace a gidanta ba tare da ta sani ba.

Kawai sai hawaye suka fara turereniya a fuskarta daga ƙarshe fashe mi shi da kuka ta yi sosai.
Chapter 81 · 0% Book details