← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 86

Sashe 65

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin da tsaƙon ya shigo Hauwa na tsaye ta riƙe Juwairiya ƙam da take son ta fice daga gidan.

" Ina tausaya miki Juwairiya ko wani namijin kika aura ba A.m ba za ki sha wahala sosai,na lura baki iya ɓoye so ba in dai kina son mutum su maza ba'a musu haka yayin da suka fahimci mace ma son su wulaƙanci yake biyo wa baya."

Hawaye ta share ta kalle ta ta ce." Wataƙila ba ki taɓa soyayya ba ne shi ya sa kike daɗin haka amma son da nake ma A.m irin na in ban same shi ba sai rijiya."
" Ina na taɓa so ai kin san auren ƙiyayya na yi da mijina.Ta yi mata gatse sannan ta ɗora da cewa "Ai ko kina ruwa wallahi don ina tausaya miki."

Kama hannun Hauwa ta yi ta riƙe sai hawaye shar!"Ki bar ni don Allah na tafi."

Kallon ta ta yi tana dariya ta ƙara cewa." To mara aji matar mahaukaci, ya ce na tura masa da adireshin gidan, sai ki kwantar da hankali don na fiki murnar tafiyar ki ko banza yau zan yi bacci lafiya, ba tare da na yi rarrashin kukan da ake min duk dare ba.In kun so sai ku kashe kanku munafukai kawai."Wani irin daɗi ya lulluɓe jin zai zo duk da tana tsoron haɗuwar su amma idanuwanta suna ƙaiƙayin son ganin sa.Yana isowa hon ya shiga yi ba ƙaƙƙautawa.

Da gudu ta ruga har tana bige ƙafa da ƙofa amma bata kula ba,ko sallama ba ta yi mata ba sai hannun da ta ɗaga mata.

Duk da bugun da zuciyarta take mata amma gaka nan ta yi shahada ta shiga suka zuba ma junan su ido.
A.m da yazo da fushi duk sai ya nemi fushin ya rasa musamman da ya ga ta rame kamar wacce ta yi ciwon shekara.

Kau da kan sa ya yi ga barin kallon ta ya ɗauki biro ya saka a tsakanin yan yatsun ta ya matse da ƙarfi har sai da ta yi ƴar ƙara saboda zaba.

" Kin san irin girman laifin da kima yi mini?Kin ɓata mini rai ƙwarai kuma saina miki horo mai tsanani,na rantse kika ƙara gigin ƙara zubar min da ciki saina illata ki sannan jikina ba zai yi wahala ba sai kin mayar da abinnda kika zubar.
Ƙaryar iskanci kike ba ki san waye ni ba muje gidan za ki ga abin da zai faru dake."

Tsananin tsoro ya cika mata zuciya ganin irin muguntar da ya yi masa,sai ta ji tsoron kar yazo ba kowa a gidan ya kashe ta a banza,saboda har yau tana tuna irin shaƙar da ya yi mata.

Ganin fuskar sa babu fara'a hankalinta ya ƙara tashi.
" Ka yi haƙuri na gane kuskure na insha Allahu ba zan ƙara ba kuma na yi hakan ne..."

" Ban tambaye ki dogon surutu ba in har kina son na yi haƙuri to ki ƙoƙarta ki mayar da abin da kika yi mini asarar shi a yau."

Ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba hankalin sa na kan tuƙin da yake yi.

Yanayin yadda ya ya nuna mata hankalinta ya É—an kwanta,domin ta yi tunanin fuskantar haka daga gare sa,ta É—auka dukan mutuwa zai yi mata kuma ya kore ta.

Tun da ya faɗi wannan maganar bai ƙara cewa uffan fa har suka iso gida lokacin a na kiran sallar isha'i,don haka parking kawai ya yi ya fice masallaci.
Ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi tana ƙare ma gidan kallo wanda rabon ta da wata biyu kenan

Da ta tuna Zainab sai da gabanta ya faÉ—i ras! Duk da ta san ba ta gidan shi ya sa ya je ya É—auko ta,a ranta take tunanin ko ta yi tafiya zuwa waje.

Bayan ya shigo tana zaune a falon gidan sai ƙare wa falon kallo take saboda ganin ya canza,kallonta ya yi sai kuma ya ɗauke kan sa zai haye sama.

Da sauri ta riƙe hannun shi." Don Allah ka yi haƙuri ka yafe min wallahi na tuba kuma na yi nadama."

Hararar ta ya yi tare da galla mata tsaki ya janye hannun sa sai kawai ta faÉ—a jikinsa tana kuka sosai.

" Ke fa matsala ce ta ko ina bayan asarar da kika yi min kukan banza za ki rarrashe ni da shi ko?Kawai zan haƙura ne in har kin yi alƙawarin yau za ki mayar min da asarar da kika yi min."Ya faɗa cikin wata irin murya.

ÆŠago kanta ta yi tana share hawaye ta kalle shi sai kuma kunyar abin da ya faÉ—i ya sa ta sunne kanta tana murmushi.

" Yunwa nake ji ƙwarai kin korar min matar so,sai ki maye makwafin ta kafin ta gama hutun ta dawo,sai ki yi ƙoƙarin mai da asarar da kika yi mini don ba zan wahalar da kaina ba.

Da sauri ta tashi ta ƙwalalo masa ido tana dariya sai kuma ta nufi kicin,wanda dama kafin ta yi alwala sai da ta ɗora masa abu mai sauƙi wanda zai ci,don ita yau murna ba zai barta ta ci komai ba.

Mamaki ta yi da ta ga ya biyota kicin ɗin duk da ƙorafin abin da ta yi masa yake yi,da kuma yi mata gargaɗin kar ta ƙara sai ta ji sanyi sosai a ranta ,saboda yana da saurin fushi zai kuma iya yanke komai ba tare da tunani ba,amma kuma yana da saurin sauka.

Ba ƙaramin mamaki ta yi ba da ya nuna mata shifa da gaske ita za ta mai da asarar da ta yi masa

Hakan ya sa ta dage sosai don ta faranta masa saboda ya manta komai.Daga ƙarshe da kan sa ya karɓi jagoranci komai,saboda bai san ya yi missing ɗinta alot haka,a haka bacci ya yi ya kasheta da ƙaunar sa da take sakata hauka a kan sa,sai ya fake da duk a cikin horo yake mata wanda so yake ya maida asarar da ta yi masa.

Sai da suka makara sallar asuba ita ce ta farka ta zare jikinta sannan ta tashe ki,kan dole a gida ya yi sallah,ya kuma sawa suka koma bacci.

Ba su tashi ba sai misalin sha biyu na rana kiran wayar da A.k yake yi ya tashe shi.

Tsaki ya saki zai kashe wayar sai dai da sauri ya miƙe ganin kira rututu a wayarsa,da ya kalli agogo salati ya fara yana ɗan buga bayanta ganin sha biyu har ta gota.

Miƙe wa ta yi ita dama tuni ta farka ba ta so ta farkar da shi ne,ya sa ta ci gaba da kwanciya amma yunwa take ji matuƙa.

" Hello hala yau mutuwa ka yi ne ana ta kiran waya ka san muna da baƙi sai ka zo ka buɗe mini falon ka ina waje baƙi na ta jira.

Da sauri A.m ya sauka ƙasa shaf ya manta da client din sa da za su zo yau yana faɗin." Ki sauko ki bani abinci mai sauƙi fita zan yi."

A.k ya dogare a bakin ƙofa yana kallon sa ganin sa da kayan bacci." Wai hala rashin matan na ka ya sa ka fara shaye-shaye ne? Haba bacci har sha biyu da ƴan mintina sai ka ce wanda ya yi sabon aure.

Shafa kansa ya yi ya ce." Kai fa banza ne bari na watsa ruwa mu tafi."

Yana ƙoƙarin hawa Juwairiya ta fito da nufin ta shiga kicin ta ɗora girki kanta a sunkuye ta gaishe da A.k da ya yi tsaye yana kallon Am da yake shafa kansa.

" Kai amma ka ci uwar É—an rainin wayo ka bar ni ina can ina ta neman ta,Baba Sani ya tasa ni a gaba ashe kana nan ka na cin amarci har da makara."
Tsaki ya yi ya harare shi daidai lokacin da ta shige kicin ya sausauta murya ya ce."Nima ganinta na yi ta dawo."

Ya na taɓe baki ya yi maganar ya ɗauki remote ya kunna tv bari na yi sauri na watsa ruwa ka rage zama.
" Allah ya yi munafuki anan ka yi sauri ka fito kai ka sani da gulmarka."
Dariya ya yi ya bugi bayansa." Da babu ai gara ba daÉ—i."Ya ce tare da haye wa sama.

Kusan sati biyu tun da Zainab ta tafi Lantana ba ta zoba,sakamakon yarta da take aure ta haihu an yi mata aiki ta tafi jinya.Hakan ya ba su damar sakewa suna jutawar su.
Kullum ranar duniya sai A.m ya kira Zainab amma ba za ta ɗaga ba, kuma yana ta biko gurin iyayenta,sai wulaƙanci suke masa daga ƙarshe mahaifinta da kan sa ya kira Daddy A.m a kan ya daina zuwa gidan shi Zainab sai ta huta za ta dawo.Da zarar ta dawo za ta dawo ɗakinta don haka ya daina damunsa.

A.m ya yi fushi sosai sai ya yi zuciya ya ƙyaleta musamman da ga matar wucin gadi,ta dage tana faranta masa ko ba komai zai yi maleji kafin ta dawo.

Juwairiya ta yi amfani da wannan damar ta saka rayuwarta a cikin ta A.m duk da irin gwasaleta da yake yi, yana yabon Zainab amma da ya fita zai kira ta yana gaya mata ya yi missing hawayenta na banza don Allah ta yi mishi kukan zai siya.

In ya faɗi haka dariya take mishi ta ce ashe kukan banza ya ƙara matsayi tun da har siye ake son ayi.Haka dai suke zaman su cikin girmama juna da kulawa.

Washegari Zainab ta kira lantana aka ta je ta gyara mata gidan ta,saboda tun da ta tafi kewar sa ya dame ta ko bacci kasa yi take yi,duk kiran da yake mata rungume wayar take yi tana kuka,amma shegen girman kai ya hana ta ɗaukar wayar in ta tuna kuma da abin da ya yi mata sai ta ji duniyar ya yi mata zafi.Ita tunanin ta A.m zai biyo ta ƙasar ne.
Chapter 65 · 0% Book details