← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 86

Sashe 29

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 15*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

A karo na biyu ta ƙara gwalalo idanunta." Ina hakan ba zai taɓa yuwu ba!Gara na rayu a cikin talauci na kuma mutu a cikin sa.Anya ya san me yake faɗi kuwa.
Sai kawai ta nufi hanyar fita ba tare da tace mishi komai ba.
Juwairaah!"

Ya kira sunan ta da sauri tare ƙofar ya kama hannunta wani irin hajijiya ya kama ta wani abu mai kama da shokin,ya na zagaye jikinta yayin da yake fitowa daga gurin da ya riƙe ta ya na ƙara wutar sonsa a cikin zuciyar ta.

" Don Allah ka cika ni ba zan iya abin da kake faÉ—i ba,hakan ya tabbatar min da ka tsane ni ba ka son ganin farin cikina dama na san ni ba'a sa'ar auren ka ba ne, to amma kaje ka auri mata masu aji irin matarka ta yadda za ka samu Æ´ara daga gidan kuÉ—i,ba irina wanda mahaifina ya mutu bai bar min komai ba.

Ta faɗa tare da fisge hannunta da sauri ya sha gabanta ya toƙare kofar da take son ta fice, jikinsa ya yi sanyi ganin kamar ba za ta yarda ba,amma kuma ya zama dole ya san yadda zai yi ya shawo kanta,saboda amincewar ta ne kawai zai sa ka ta jure duk wani abu da za ta gani a gidan.

" Nima na so haka na sami mace mai aji kama ta, amma kin san babu wata mace mai aji wanda zan nema ta yadda da hakan.Kasancewa ta ɗa namiji da kowa ce mace za ta yi burin samu shi ya sa naƙi nai mar me aji iri na, don na san ba za a kwashe dai-dai da ita ba,kuma kema fa so nake na ceci rayuwarki daga ƙangin talaucin da kike ciki.

Ya ƙarashe maganar da murya na salon yaudarar shi ya na son ta amince.
Hawaye suka ƙara turereniya a fuskarta ta kalleshi da nufin ta saka wani mugun tsanar shi a cikin ranta,amma sai ta ji wani madarar son sa ya na ƙara shiga cikin bargon jikinta a duk sanda ta yi kuskuren haɗa ido da shi.

" Sai ni talaka ko?Ni da Allah bai saka min zuciya na so ba.Ko naƙasun talauci ya na yin tasiri a zuciya duk lokacin da ta ke son wani?Shi ya sa za ka zo ka cuci rayuwata ta ɗa na kake son na haifa na ba wata mace na har abada?Don Allah ka fita daga cikin rayuwata na roƙe ka na san ba za ka samu matsala da ƙanin mahaifina ba,amma ni ba zan amince da mugun nufin ka a kaina ba.A yau na yi burin dama ban taɓa sanin ka a cikin rayuwata ba."

" Ke ya ishe ki Æ´ar talaka kawai zaki zo ki na jera min wasu maganganu kamar wani É—an ki!Dama ban yi miki dole ba."

Ya faÉ—a tare da kaucewa ya ba ta hanya ganin hakan ya sa ta zura da gudu za ta fita,dai-dai lokacin da Baba Sani ya yi gyaran murya."Ya kamata ka wuce abokin ka ya na jira,kawai ka nemo waliyin ka a duk sanda kake son a É—aura auren kar ka damu da ita ko amincewar ta"
Da ido ya kalleta ya na gasgata abin da yake faɗi." Kin ji da kunninki abin da kwaɗayayyen ƙanin mahaifin ki yake cewa?Don haka ina tambayar ki ne don kar ayi ba tare da yaddar ki ba kizo ki ɓata komai."

Ya zaro waya mai kyau da tsada ya ije mata." Ga shi zan wuce na gaji da wannan kukan nan naki da kika tasa ni da shi.Fisabilillahi sai kace na zo gidan ta'aziya,duk abin da kika yanke zan kira sai ko gaya min." Ya miƙa mata kuɗi masu yawa." Ga shi ki je ki yi ma marasa lafiya siyayya.Ina ƙara gaya miki ɗa ɗaya kawai nake son ki siyar min bayan nan zaki iya auren namiji wanda ya fini,domin zan ƴanta rayuwarki zan gina ma mahaifiyarki gida na ba su duk wani jin daɗi na rayuwa.

Shekara É—aya ne fa kawai za ki yi kina ma masoyiyata aiki in ma kin sami ciki, da wuri zan É—auke ki daga gidan kin ga kin huta kenan,sannan ki iya takun ki ba da sani ta zan yi komai ba."

Ya numfasa ya na kallon ta yadda ta yi zuru ta na kallon shi,yayin da zuciyarta ta ci gaba da bugu cikin tashin hankali.
"kamar yadda na gaya miki haka za ki yi don haka ko kallona kar ki yi in dai ta na kusa da ni.Kasancewarta ba mai zaman gida ba ne kinga haka zai bamu damar aurenmu ya tafi cikin sirri."

Ya ce da ita sannan ya fice ya barta a tsaye tamkar gunki sai da ta ɗauki tsawon lokaci sannan ta yi zaman ƴan bori a ƙasa tare da fashewa da kuka.
" Don Allah karfa ku yi min ƙarya ku dawo fa in ba haka ba wallahi sai na nemo ku duk in da kuke don ba zan ga samu na ga rashi ba.

Motar su na ɓacewa ya ruga da gudu ya shige ɗakinsa alokacin Juwairiya har ta miƙe ta share hawayenta za ta fice." Ƴar albarka Juwairiya zo mai ya baki."

Sai kuma ya hangi damin kuɗin da ko ta kan shi ba ta bi ba, ai da sauri ya dafe ya na washe baki sannan ya miƙa mata dubu biyar ya ce." Gashi maza ki tafi Juwairiya ya gaya miki komai ko?Ai Allah ya tarfa ma garin ki nono kin huta da auren wannan mutumin,dama ɗan iskan tun da ya ga na ba shi auren ki ya dai na bani komai,duk da na yi baƙin ciki amma ko ba komai ai na samu ta sanadin ki rayuwata za ta shiga cikin jerin masu da shi."

Juwairiya ba ta ce komai ba har ta kai ƙofa za ta fita, sai kuma ta dawo ta ce." Ni fa ba zan aure shi ba haba Baba ka ji tausayina mana!Wallahi in..."

"Rufe min baki banza shashasha!Don ma kin samu zai aure ki wallahi da bai zuba uban kuɗin nan ba, to ko megadin gidansa yake son ki yi masa ba zan bari ba,ai ke gaba ta kai ki ko banza a shekara ɗaya zaki rayu cikin daula,ko banza za'a sha zaƙi da maiƙo a rabu da tuwo wanda shima ba kullum ake samu ba."

Da sauri ta fice jin maganar da yake mata wanda duk cin fuska ce.

Juwairiya ta shiga cikin tsananin hankali tun lokacin da ta fito da ga É—akin Baba Sani ta kife kanta ta na wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare.

Yayin da tausayin kanta ya rufe ta ganin mutumin da take matuƙar so ya zo neman ta akan auren kwangila."Yanzu inna auresa shekara ɗaya za mu yi? Shima tsakanin mu tamkar mage da ɓera tunna matarsa ta yi katanga a tsakanin."

Abin da take ta faɗi a ranta kenan sai kuma ta share hawayen da damuwa cike a zuciyarta,don ta rasa yadda za ta kwatanta wannan auren da yake son su yi,amma a ranta ta ƙudira koma me zai faru sai dai ya faru don ba za ta aure shi ba,ai gara ya barta a cikin tsananin talauci saboda in talaucin bai kashe ta ba,tsananin son da take mishi da kishin matarsa zai kai ta lahira!

Ko da ta isa asibiti ba yan ta gama girki abin mamaki sai ta ga Baba Sani zaune a can,ya dage sai zuba ruwan surutu yake yi tamkar wani aku.

Sai Juwairiya ta kasa shiga ta tsaya ta na kallon shi da mamaki ganin yadda yake ta magana har da dariya ga uban leda da ya siyo musu abu.

Mama shiru ta yi ta na kallon shi da mamaki."Oh ikon Allah duniya juyi-juyi!" Abin da ta ce kenan cikin tsananin mamakin sa.

"Ƙaraso mana Juwairiya kin ga har na riga ki ai daga gurin aiki sai na taho,ban san kina gida ba."

A sanyaye ta shigo tare da ije abincin dai-dai lokacin da Baba Sani ya tashi tare da yi musu sallama ya tafi.

Da sauri Juwairiya ta bi bayan sa ya na ƙoƙarin shiga motar sa ta riƙe murfin motar idanunta na zubar hawaye " Ba zan aure shi ba gara ya barni a halin da muke ciki,amma ba zan yi aure ba wanda mahaifiyata ma ba'a son ta sani!Tun wuri ka mai da masa da kuɗin sa ni zuciyata ba irin naka ba ne!Na san mutuncina ai talauci ba hauka ba ne "

Kau ya gaura mata mari " Baki da hankali kina wasa da ni ke baki san halina,ni murucin kan dutse ne! In har kika ce ba za ki yi wannan auren ba,kin ji na rantse miki Juwairiya zan iya kashe ki har da mahaifiyar ki.Don haka in baki bi umurnina ba ki kuka da kanki."

Ya ja motar sa ya barta a nan tsaye cikin tashin hankali sai kawai ta rushe da kuka,sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shuru ta wanke fuskarta ta shiga cikin É—akin da Mama suke.

" Ikon Allah abin duniya ba ya ƙarewa kin ga abin mamaki ko.Ai addu'a takobin mumuni ne."
Juwairiya ta ce."Umh Mama."Sannan ta É—auki filet ta zuba mata abinci.
"Juwairiya bayan fitar ki likita ya zo ya ce in dawo ki je ki same shi,sannan ya ba da takadda kamar na magani ne."

Ta ce cikin damuwa da murya ƙasa-ƙasa kai da ga ji ka san ta na cikin jinya mai tsanani.
" To Mama bari na je na same shi."
Ta miƙa mata abincin sannan ta fita zuwa ofishin likitan.
"Ok zauna"

Ya ce da ita bayan ta ƙwanƙwasa ta shigo a hankali ta zauna cikin tsoro-tsoro don ba ta san dalilin da likitan ya kira ta ba.
Chapter 29 · 0% Book details