← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 86

Sashe 78

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tare da ta kalle shi ba ta ƙara sautin ƙarar wayarta da tsaƙwanni ke ta shigowa rututu,sai da ta nisa ta ce." Ni ma ba na buƙatar ya canza kuma ba zan zauna da mutum yana mini warin jaɓa ba,gara na ƙarashe sauran watannin da zan yi ba tare da na kusanta kaina da kai ba,don haka kar ka damu na zaɓi in da na saba zama."

" Hakan ya yi ai sai ki ci gaba da zama kayan É—akin kawai zan canza don É—ana ba zai kwanta in da talawa suke rayuwa ba."Ya ce tare da É—aukar wayarsa ya fara hawa sama.

" Aiko sai ya kwana don ba shi da mara ba da talakawan a jikin Æ´ar talaka ya fito ka ga shima dangin matsiyata ne."

Da sauri ya sauko ƙasa kamar zai isa gareta amma sai ya fasa ya yi mata wani mugun kallo.
" Ƙarya kike yi ko da ya a fito a jikinki sai da na saka kuɗina na siye ki da maƙudan kuɗi,kuma kar ki manta wacce zan ba ma wa gaba da bayanta arziki suka gada ba tsaya ba."

" To dangin ƙaruna ai dai ba a canza ma tuwo suna."Ta ce tare da ɗaukar goruba ta fara ci don ta san ya tsani ya ganta tana ci.

Tsaki ya yi ya haye sama ba tare da ya ƙara ko kallonta ba.

Juwairiya na zaune a cikin falon ta ga ana shigowa da kayan É—aki masu kyau,har aka gama jerawa suka tafi sannan na shiga ya yi kyau sosai.

Kwanciya ta yi ba ta tashi ba sai gabda magariba,wani irin ƙulululu ta ji cikinta ya yi na yunwa,sai ta far hawaye da ta tuna irin gatan da suke mata.

Kicin ta shiga ta don ta yi faten da ya zama kamar al'ada ku san shi ne abinta a kullum.

Sai dai ko da ta shiga kicin É—in warin gas ya hana ta yin komai,duk da toshe hancinta da ta yi ta kasa zama a kicin É—in.

Kayan ciye-ciyenta ta kwaso ta dawo falo tare da kunna kallo ta zauna tana ci.Gidan ta ji ya yi mata faÉ—i saboda babu kowa a gidan sai maigadi,A.m kuma tun da ya fita bai dawo ba.

Bayan ta yi sallar magariba da ƙyar ta jira isha'i tana gyangyaɗi,akan daddumar ta kwanta sai bacci.

Sai misalin tara ya shigo ganin bai ganta a falon ba sai ya yi mamaki saboda da sai ta kai ƙarfe sha ɗaya tana kallo.

Ɗakinsa ya shiga ya yi wanka kafin ya zo ya yi sallama da ita,don haka ko turare bai shafa duk da yana jin wani iri,amma gudun rigimarta ya haƙura.

Dariya ya yi ganin yadda ta dunƙule kanta tana bacci a dadduma sai ya shafa mata addu'a ya ɗaga ta cak ya kwantar akan gado tare da rufo mata ƙofa ya fita.

A.m dake ta juye-juye a É—akinsa shi kaÉ—ai yana jin kewa na damunsa musamman na Zeey É—in sa shida yake hutawa da matansa biyu,amma É—aya ta gagare shi,don haka ba tare da wani tunani ba ya fice daga É—akin,bayan ya fesa turaren da take so a É—akin.

Cak ya ɗaga ta don ya san ba za ta amince ta biyo sa ba,sai dai kafin ya isa da ita ta farka tana mi shi bore amma bai kula ta ba,har sai da ya dangana ta da ɗakin ya kwantar dare da rufe ƙofar.

" Ki kwanta har na fara bacci Momi ta kira ni ta ce kar na sake ki kwana ke kaÉ—ai a É—aki,saboda gudun matsala."
Bakin sa ya taɓe yake magana ba tare da ya dube ta ba,ganin yadda ta ci magani tana mi shi bore.

" Amma ka san ba na son ƙamshin jikinka ba zan iya kwana da kai ɗaki ɗaya ba,sannan na yi alƙawarin babu abin da zai ƙara kawo ni ɗakin nan,saboda na gama aikin da aka biya ni."

" Na sani ni ma ba wannan ya sa na kawo ki ba ko da haƙuri nake yi nake kula ki don na samu baby,amma kin san ai na wuce ajin da zan kula ki.Fatana matar so ta dawo mu ci gaba da zamanmu lafiya." Ya ce tare da kwanciya can gefen ta.

" Oho ko ma me za ka ce ba ni da matsala Allah ya sa matar ladan gona nake a gareka bai shafe ni ba."Ta ce sannan ta fara mi shi bore tana yatsina fuska kan za ta bar É—akin.

" Kin san Allah ko aman me za ki yi ba zan raba kwana da ke ba,sai matar so ta dawo gara ki kwantar da hankalin ki ki kwanta ya fi mi ki."

Juwairiya da ta gaji da ta kwanta bayan ta É—aure bakinta don ta lura komai zai ta yi mi shi ba zai mai da ta É—akinta ba,sai ta kwanta don babu yadda za ta yi.

A.m da ya kasa bacci yana ta mutsu-mutsu yana jin tana ƙorafi har ta gaji ta yi bacci,amma shi ya kasa bacci.

Wani irin juyi ya yi sai ga shi ya rungumota ya matseta a jikin sa.
Da sauri ta ture jikinsa cikin ɓacin rai." Don Allah matsa za ka takura mini ina bacci,ka san ba na son na ji na raɓe ka."

Ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya ƙara matseta a jikinsa yana jin zafin jikinta ya yi masa daidai da sanyin jikinsa.

" Ki kiyayeni har yanzu a matsayin matata kike don haka ina da ikon da zan taɓa ko ina a jikinki."Ya raɗa mata a kunninta.

" Ai ba ka isa ba in ba haka ba amai kake son ka yi wanka da shi do.."

" Allah ya sa abin da ya fi mai za ki yi amma saina matso kusa da ke,ko ranar da kika yi mini ba kashe ni ya yi ba,in ma da gayya kika yi,sannan ki korar mini matar so sannan ki barni maraya,ai ba ki isa ba,yanzu É—in maneji zan yi kin san ba kamar ta kike ba."

Ba tare da ta ji baƙin cikin abin da ya ce ba sai ta saka mi shi kuka sosai,jin abin da yake mata sannan tana jin duk in da ya taɓa na jikinta kamar yana ɗora mata garwashin wuta.
" Ai in har ka taɓa ni ba zan yi wanka ba don ba na son na saka ruwa a kaina."

" Wannan kuma ke ya shafa matsalar ki ne ke da Allah."Ya ce mata ba tare da ya fasa abin da ya yi ninya ba.

Ganin da gaske yake ta ture jikinsa da ƙarfi za ta miƙe,amma sai ya saka ƙarfin tuwonsa ya riƙe ta ƙam.
" Ka rabu da ni sadda ka je neman aurena cewa ka yi in samu ciki in haihu ai baka nuna bayan cikin a kwai abin da zai shiga tsaƙaninmu ba."

Dariya ya yi jin abin da ta ce sannan ta ƙanƙame jikinta sosai,sai ya tsaya cak ya kalle ta ransa ya fara ɓaci.

" Har yanzu matata kike so ki kiyaye ni karki kai ni bango in yi miki dole gara ki saki jikinki."

"Mugu azzalimi wallahi gobe gidan Momi zan koma ko na ɗauko Hamdiya mu rin ƙa zama tare."Ta ce da shi jin ya kai mata wani wawan kis.

" Allah ya ba ki sa a dama ki na da hali mai kyau da za ta karɓe ki,na san mugun halinki na ƙazanta ya saka Momi ta kore ki,ita Hamdiyar ba mahaukaciya ba ce kamar ki."

Ganin abin da take mi shi ya tashi zaune da ɓacin rai ya ce." Juwairiya ki fita idona ina tausayinki ne don babyna na rantse da yanzu jikin ki ya gaya miki."Ya ce mata ran shi a ɓace.

" To meye sabo a gareni ka duki matar so balle ni ai halinka ne."Da ɓacin rai ya kalleta ganin ta ƙi yadda sai ya sausauta murya.

" Kar kiji ina roƙon ki gaisawa da babyna zan yi kuma maneji zan yi da zarar Zainab ta dawo ko kallonki ba zan ƙara yi ba."

Ganin ba za ta kula sa bai saurara mata ba sai da ya samu natsuwa ya matsa gefe.Juwairiya da sauri ta miƙe tana kwara amai da fari biriss ya yi da ita amma gani yadda ta ke ƙaƙari sai ta ba shi tausayi ya isa gareta tare da kama jikinta.

" Karka taɓa ni dama na san ka tsane ba ka sona duk abin da zai cutar da ni shi kake so."

Tsaki ya yi ya koma ya kwanta kuma ya ƙi buɗe mata kofa da ta gaji ta kwanta ita ma.

A.m da ya jima bai yi bacci ba yana ta tunanin canjin da ya ji a jikinta domin ta canza kamar ba ita ba,komai na jikinta ya zama wani iri wanda shi kan sa ya kasa tantance komai.

Hunnunsa ya tura cikin gashin kanta yana murmushi mai É—auke da ma'anoni wanda shi kaÉ—ai ya san me yake nufi.

Haska fuskarta ya yi da wayarsa sai yaga ta yi bacci tana saukar da numfashi a hankali,yayin da fuskarsa take wani irin haske mai walwali.

Murmushi ya yi kamar ya rungumota su kwanta amma ya san mai zai faru sai ya kwanta cikin annashuwa,tare da tofa mata addu'a ya kwanta da tunani barkatai a zuciyarsa.

" A.m ka tashi don Allah."

Juwairiya ta ke bubbuga shi a hankalinda wata irin murya,amma sai bai ji ta ba kasancewar bai ya daÉ—e bai yi bacci ba.

Ganin haka kawai sai ta saka mi shi kuka da ƙarfin ta.Da sauri ya buɗe ido tare da kunna fitila,ya kalli agogo ƙarfe biyu da kwata.

"Lafiya mai ya same ki?"

Ta riƙe cikinta tana hawaye ganin haka ya ruɗe ya kamo ta jikinsa.

Ture shi ta yi ta ce." Cikina ke ciwo kuma na kasa bacci."

" Mai ya faru take ciwo ko baƙin ciye-ciyen ki za ki ja mini asara."Ya ce da ita cikin ɓacin rai da ta tashe shi da tsakar dare,saboda bacci ne a idanunsa.

" Yunwa nake ji kuma É—anwake zan ci."Ta ce tana fargabar abin da zai ce mata.
Chapter 78 · 0% Book details