Sashe 17
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani ƙarin haushi ya turniƙe shi ita sam ba ta kishin jikinta ganin shigar da ta yi,sannan ta na cire kayanta amma take kiran me aiki tazo kai Zainab lamarinta a kwai gyara.
Bayan ta cire rigar ta umurci Mero ta É—auko mata wani wani kayan ta saka,sannan ta nufi gurin sa da yake zaune saboda tsaban takaici be kalleta ba bare ya tanka mata,sai kallon agogon hannunsa yake.
Ba tare da nuna damuwa ba taja tiren abincin da ya saka Mero ta kwashe wan can ta kawo mishi,saboda tsabar yunwa da yake ji amma ya kasa cin abincin sam babu tes jira yake a gama ruwan ya ya yi take away.
Fara ci ta yi ta kalle shi tace."Habibi ba ka ci abinci ba lafiya."Banza ya yi da ita yaci gaba da kallon wayarsa ya na danne-danne a cikinta.
Kai hannu ta yi ta taɓa wuyan shi ko ta ji da zafi a tunaninta ba shi da lafiya,amma sai ta ji jikinsa normal.Taɓe bakinta ta yi ta ci gaba da cin abincin a ranta ta na faɗin."Miskilancinne ya motsa bari na kama kaina."
Kusan minti talatin ya na kwance be tanka mata ba har ta gaji da zama yaƙi kunna kallo ta san ta na kunnawa, ze taso mata tunna dama a yadda ta gan shi jira yake ta taɓo mishi,sai ta miƙe sif za ta shige ɗakinta ta hau charting.
Idanunsa a lumshe ba tare da ya buÉ—e ba yace."Da ga ina kike?"Yace a cikin wata irin murya me kama da da baya son maganar.
Dawowa ta yi ta zauna ta duburbuce ta fara in ina.Ya ƙara jeho mata wasu tambayoyin da cewa."Sai yanzu kika dawo ba na hana ki dawo min gida da daddare ba?Me yasa baki wuce gidan kuba.Kuma da izinin uban wa kika fita?"
Gabaki É—aya ta tsorata ta kuma ruÉ—e ganin yadda yake jeho mata tambayoyin da ta kasa amsa koda É—aya ne.
Miƙewa ya yi ya matso kusa da ita ya na kallon kayan da tasa ya ɗauka ya na kallonta a wulaƙance."Ba na hanaki saka irin kayan nan ba wai ke me yasa bakya kishin kanki yanzu fa a gaban ƴar aiki kika canza kaya,sam bakya kishin sirrina Zainab hauka kike son na yi a kanki na fara gajiya da halinki."
Duk cikin maganganunsa ba wanda ta ji haushi sai tambayar ta daga ina take da ɗan yi jim ta kuma dake ta ba shi amsa da cewa."Ina tunanin mun gama magana akan fita ba sai na tambaye ka ba saboda gaskiya ban ga a na wannan takurar a gidan mu ba.Kuma fa gidan ƙawar Anty Usaina muka je yau ake birthday ɗin ɗanta."Ta ƙarashe maganar ta na son ta ja hankalin shi ya sausauta fushin da ya ɗauka.
Ya ƙara jan tsaki me ƙarfi dama ya san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi.
Tsawa ya daka mata yace "Malama karki raina min wayo na gaji da waɗannan banzan bidi'oin da kika saka a ranki.Kin raina ni matuƙa Zainab baki ɗauke ni da daraja ba a matsayina na mijinki,watakila haka kika ga ana yi a aure a matsayinki na matar aure ba zaki shigo gidana ba sai tara da mintina."
Kaɗa kansa ya yi ya miƙe yaci gaba da cewa."Kin san nace miki in har kika fita ba da izinina ba,ban yafe miki ba kuma mala'ikun rahama suna tsine miki harki dawo sai ki kiyaye."
Hararan shi ta yi tace cikin gunaguni."Taɓ ni ai na gaya maka ba zan amince a takurawa rayuwata ba.Haka kawai to meye amfanin ilmina na lura so kake ka mai dani irin gidahuman matan nan marasa ilmi,waɗanda suke bari namiji na raina su wai duk in da zani saina tambayeka Allah ya kyauta."
Da takaicin yadda ta raina shi bata shakkar shi yace."Ba ma fita ba na hanaki driving sai dai duk in da zaki a yi driving É—in ki."Ya na faÉ—in haka ya fara taka matakalan bene ze haye.
A sukwane ta jawo rigar shi ta baya cikin fushi tace."Wallahi ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa Ka mata ni zan yadda wani shashashan direba ya tuƙa ni,karka manta kusan motocina daga gidanmu na zo da shi bare ka yi min iko,in ma akan wace ka siya min ne ba zan ƙara hawa ba amma ba wanda ya isa ya kafa min dokoki."
Nu na ta da yatsa ya yi ya na cewa."Ba na hana ki kuma na yi miki warning akan riƙe min riga da kike yi ba,to wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara wannan gangancin.Kuma kika kuskura kika zage ni sai kin raina kanki,don jikin ki ze gaya miki."
Dariya ta yi me sauti ta ba shi amsa da faɗin."A lai-lai da ka tabbata ɗan ƙwaya kamar ni zaka buga aiko ruwan sama se inna so bare wani gardi can.Duk mutanen gidan ku kuwa sai an koya musu hankali ai ban yi kalar matar duka ba.Ko ka manta matsayin uba na."Ta numfasa sanann ta ɗora ta na kallon shi da tsananin ɓacin rai ya sa shi tsaye ya na kallonta.
" Kuma da kake faɗin karna zage ka inna zage ka me za ka yi?"Tace mishi cikin zallar rashin kunya ta na karkaɗa ƙugunta.A.m ya yi ƙuta yace.
" To ki kwatanta ki gani fitsararriya kawai."
Baki ta turo mishi tare da murguÉ—awa." Ni ba fitsararriya ba ce banza mara m....".
Wani irin mari ya gaura mata wanda yasa ta É—auke lokaci guda ta yi taga-taga za ta faÉ—i amma ta dake tare da kwarma wani uban ihu,abin ka da farar fata lokaci guda fuskarta ta sunduma domin marin ya gigitata sosai.
Amma saboda taurin zuciyarta ta cakume shi ta na ihu ta na zagin sa shi kansa ya yi mamakin kafiyarta,ture ta ya yi ya shige ɗakinsa tare da bugo ƙofar kai tsaye bayi ya wuce ya sakar ma kan shi ruwa,domin ta haɗa mishi zafi kwanyar shi har wani tafasa take yi.
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na goma.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*SHAFI NA GOMA*
Bayan ya fito da ga wankan ya na jin yadda sautin kukanta yake tashi ya na mishi kuwwa a kunninsa,sai ya ji be kyauta ba da ya mari rabin ransa take ya zira doguwar riga ya fita don ya rarrasheta.
Ɗakin ta ya shiga ya ganta ta na ta kuka ta na haɗa kayanta tare da ƙoƙarin kira a wayarta,sai dai da alamu ba ta samu wanda take kira ba.Wayar ya fisge tare da rungumeta cikin tsigar rarrashi.
Dukan sa ta fara a ƙirjinsa ta na ƙoƙarin raba jikinta da na sa,da kyar ya samu ta sausauta kukan ta ɗan yi shiru ta na sheshsheƙar kuka cike da shagwaɓa.
Da ƙyar ta ya samu ta yi shiru amma ta rantse mishi duk ranar da ya ƙara kai hannunsa jikinta sai ta haɗa shi da Daddy ɗin ta,shi dai aikin lallashi yake ya na gaya mata maganganu masu daɗi har da kama kunninsa ya na faɗin ya tuba.
Bayan sun shirya suka kwanta cikin ƙaunar junan su kamar babu abin da ya shiga tsakanin su.Yanayin garin sai ya basu damar yin bacci cikin shauki suna maƙale da junan su.
Washegari suka tashi kamar babu wani abin da ya shiga tsakanin su na saɓani.Bayan ya yi wanka ya fice gidan amininsa ita ma ta gallah wanka ta fice aiki.
Parking ɗin motarsa ya fito ya caɓe Anwar ɗan gidan A.k da ake goyo don yanzu ya iya tafiya.
Juya shi ya yi ya na dariya tare da É—auko tsarabar sa ya ba shi wanda duk ze zo sai ya kawo musu,sannan suka shiga cikin gidan sai ga Æ´ayarsa ita ma ta rugo da gudu ya É—auketa haka dai ya shiririce ya na musu wasa har ya É—auki tsawon lokaci.
" Yau kai ne a gari in ji maƙi baƙo ka ga angon Zainab to sannu da zuwa."Matar A.k tace ta na dariya bayan ta kawo mishi ruwa.
Shafa kansa ya yi ya na dariya yace."Gaskiya kince wani abu irin wannan kirari haka,kin san ƙawar taki bata da dama ba ta bari na naje ko ina gaskiya kin cancanci tukwici."
Dariya ta yi tace."Gaskiya makka da madina nake so a kai ni."Tace da shi."Duk kin je sai sai in kina buƙatar zuwa sai na saka sunan ki a cikin jerin masu zuwa."Dariya suka yi duka.
Sannan ta wuce ta na gyara dinning domin cin abincin rana.Bayan A.k ya fito daga É—akin baccin sa ya ba shi hannu suka tafa tare da tsokanar junan su A.k yace."Ina madam Zey."Ya shafa gemun sa ya É—an canza murya yace Æ´ar rigima za ka ce min na san yanzu ta wuce gurin aiki."
Dariya ya yi shima ya na kallon shi."Ai hali ne ya zo ɗaya an haɗu ne da an dace."Su kai dariya tare da ƙara tafawa."Madam ta gama shirya abinci ka zo muci."A.k yace da shi yamutsa fuskarsa ya yi ya na kallon shi, nan take sai hankalin A.k ya tashi musamman da ya ga ya maida kan shi a jikin kujera ya na kallon shi.Nan take ya fahimci amininna sa ya na cikin damuwa.