← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 86

Sashe 67

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Tun da ba za ka zo ba sai ƙarshen za mu dawo,saboda zamu tsaya mu yi siyayya."

Miƙewa akan gadon ya yi tare da shafa gemun sa da ya ƙawata masa fuska.

Wani irin damuwa ya ji ya lulluɓe shi sosai.

" Gaskiya na canza shawara ina ganin kawai zan ɓoye Juwairiya duk san da ta samu ciki,sai na saka Zainab ta yi cikin ƙarya a zuwan ita take da ciki in ta haihu ɗan ya zama Zainab a zuwan ita ce ta haihu."

Take ya amince da shawarar sai ya miƙe da sauri ya saka takalmin sa ya fice zuwa ɗakinta.

Ta na tsaye a gaban mirrow ta juya bayanta tare da É—an jingina kanta da gefen mirrow,a ranta ita kaÉ—ai ta san mai take tunani,domin iya tsananin damuwar dake kan fuskarta na hango.Ba tare da ta san ya shigo ba ya fara magana.
Kallon sa take yi da wani irin canji a fuskarta har ya gama mata bayani,ba ta tanka ba illa kallon sa da take kamar baƙo a gare ta.

Ganin ba ta da ninyar magana sai ya saki tsaki ya juya ya na faÉ—in." Ina fatan kin ji mai na ce."

Ko kaÉ—an A.m bai canza mata ba wai don Zainab za ta dawo,haushin da take ba shi duk ya yi mata maganar abin da ya tsara sai ta yi shiru ta zamar masa kamar wata kurma.

Zaune suke a falo sun dawo daga siyayya A.m ya ce ta raka shi a kwai turaren da yake son ya siya.

Sun zaune a falon ƙasa sun baje kayan ciye-ciye suna ci

Turaren da ya siyo ya na son ya yi haÉ—a da wanda yake shafawa,saboda turaren ya tafi da imanin sa gashi ba zai iya canza wanda yake fesawa ba.

A hannunta ya kama ya fesa mata a hannun ya ce." Matar shige ki ji ƙamshin sa ya yi daɗi ko?"

Juwairiya har ga Allah ƙamshin bai yi mata ba,kallon sa ta yi ta ɓata fuska tare da toshe hanci." Humh ni ban ji wani ƙamshin daɗi ba don ni warin almiski ya yi mini,kuma ni ba na son almiski."

" Allah ko ka ji gulma wannan turaren ko shugwaban ƙasa ya shaƙi ƙamshin sa ba zai kushe ba,balle ke ni na san gulma ce irin ta ki don ko wanda na ke shafawa ba ki taɓa cewa ya na daɗi ba."

Dariya ta yi lokacin da ta toshe baki ganin haka sai ya ji haushi sosai ya biyota ya na faÉ—in." Allah sai na fesa shi a jikin ki duka."
Zagaye falon suke yi har ya kamata zai fara fesa mata turaren,yayin da take roƙonsa don har ga Allah bai yi mara ba.

Wayar sa da take aljihun wandon sa ta fara ƙara da sauri ya ciro,jin kiɗan da ya saka ma Zainab ce.

" Hello gani a airport ka zo ka É—auke ni."

Ya kalli Juwairiya da ta ji abin da Zainab É—in ta ce saboda ta na jikin sa ya É—aga wayar.

Da ido ya yi mata magana sannan ya É—auki key É—in motar sa ya fice.

Ta na ganin sa ta faÉ—a jikin sa tare da sakin kuka sosai." I miss you honey."
Da so ya yi ya ture ta ganin irin shigar da ta yi duk da cewar a da in ta yi shiga wani lokacin ya na ƙorafi,amma yau ganin ta da gyale ta yi roling ɗin sa,sai ran sa ya ɓace sosai,domin shi da za ta fara shigar Juwairiya ya na so,saboda ya gane hijabi wani sirri ne da Allah ya bawa mata duba ga jikin Juwairiya da yake mamakin ƙirar sa.

Ga mamakin ta sai ta ga ya yi shiru, bai cika magana ba sai kallon hanya da yake yi,hakan bai saka ta damu ba saboda ta yi tunanin ko har yanzu fushi yake yi da ita,duk da cewa ita ya kamata ta ƙi masa magana,amma sanin hali sai ta kama bakinta ta yi shiru.

Wayarta ta É—auko ta yi kiran Momy ta gaya mata jirgin su ya sauka lafiya.

Ko da suka isa gida wanka ta shige saboda ta gaji matuƙar gaske,kanta har wani sarawa yake yi saboda ciwo,in da Allah ya taimake ta ta ci abinci a jirgi,so babu abin da za ta nema illa ta yi sallah ta bi lafiyar gado.

Ya shigo da dubuwar farar rigar bacci wanda ya É—aure igiyar ta bayansa,ganin ta kashe fitilar É—akin ya kunna fitila mara haske.

"Zainab ki tashi magana za mu yi kuma mai mahimmanci."

Ya ce da ita don yau yake son ya gaya mata komai,gudun kar ta ganta a gidan lamari ya jagule,saboda ya tabbata gobe in ta yi ido biyu da ita,zarginta zai zama gaskiya don ta wuce a kalle ta ace mata Æ´ar aiki.

" Wash Allah na!Haba A.m na gaji fa wallahi kaina ciwo yake yi,komai za ka gaya min ba zan fahimta ba, ka bari zuwa gobe sai ka gaya mini duka fa yanzu na dawo."

Ta ce mishi cikin ƙorafi saboda ta san bai wuce ƙorafin abin da ya faru a tsaƙanin su zai yi mata magana ba.

Miƙewa ya yi ya koma ɗakinsa ya san tun da ta ambaci sunan sa ba za ta saurare shi ba,dama in dai ta kira sunan shi yayin da suke sa'in sa ba,ba za ta yi abin da yake so ba.

Washegari da safe A.m tun da ya yi sallah bai dawo ba,sakamakon ƙanin sa da aka kira shi bashi da lafiya ya na asibiti.

Zainab ba ta tashi ba sai kusan ƙarfe da rabi saura minti biyu,wanka ta yi sannan ta yi salla,saboda duk tashin da A.m ya yi mata ba ta tashi ba,gajiya ce sosai a jikinta har zuwa sadda ta tashi ba ta daina jin bacci ba.

Wani irin yunwa take ji a daddafe ta yi sallah,sannan ta zira doguwar riga ko hoda ba ta shafa ba ta fito don ta karya,ta san cewa zuwa wannan lokacin Lantana ta kammala abinci.

Da ga wanka ta fito bayan ta ɗauki tsawon lokaci ta na dirje jikinta, da yake wani irin haske tamkar zara cikin wata,ita kanta mamakin hasken da ta yi take yi ta san cewa ta na da haske,amma ita ba fara ba ce sai dai yanzu wani irin haske ta ƙara har kusan kashe ido take yi.

Duk da ta ɓata lokaci gurin yin kwalliya amma fa ba wata kwalliya ta yi ba,kasancewar ta ba mai irin sha'awar kwalliya irin waɗan da ƴan mata suke yi,su zama tamkar aljanu.

Wata doguwar riga ta saka kalar milk amma jikinta an yi mata ado da farin duwatsu,masu kyau don yanayin rigar ya fi kama da na indiyawa.

Turaren da ta ɗauka wanda A.m yake shafawa tun da shi ta feshe jikinta da shi,ta na son ƙamshin sa sosai saboda in ta shaƙi ƙamshin sa ji take kamar A.m na kusa da ita,amma wanda ya siyo sam ƙamshin sa bai yi mata ba,har cikin zuciyar ta ta tsani turaren, amma shi gani yake kamar watsa take masa.

Juwairiya a yadda ta tsara ma kanta hak za ta fita Zainab ta ganta,don ta na ji a ranta kuma ta rantse ba za taci gaba da ɓoye kanta ga a gurin ba,za ta bayyana na komai kuma duk ta shirya da abin da zai faru.

Sai dai kuma yadda ta ga surarta ya fito ba za ta iya fita a haka ba,kasancewar ta mai alkunya da yakana.

Ƙaramin hijabi ta ɗauka ta rufe jikinta da shi sannan ta ɗauki sabuwar wayar da A.m ya canza mata mai kyau da tsada,bayan ya gargaɗe ta da kar ta bari kowa ya ga wayar saboda tsadar ta.

A lokacin da ta kama murfin ƙofar fita ɗakin sai abin ya mata mamaki,domin ita kanta mamakin kanta take na yadda ta shirya hakan,duk da ta san dala za ta ɗauko ma kanta babu gammo.

"Sannu da shigowa Hajiya Zainab barka da dawowa Allah ya ja zamanin ki a gidan A.m."

Lantana ta ce mata kamar ta na mata gatsali kamar kirari,amma a zuciyarta dariyar ƙeta take yi don ta san za'a kwashi ƴan kallo.

"Lantana ya kai ban ga abinci a dinnig ba ke wace irin shashasha ce,kin san na dawio ko dama haka kike barin mijina da yunwa?"

" Allah ya huci zuciyarki Hajiya!Amma ba ni nake girki a gidan nan ba tun da kika tafi"Ta ce cikin sauri saboda ita ta ƙosa ayi ta ta ƙare.
" Ban gane ba shi yake yi ko fita yake ya siyo bayan son na ki."Ta tambaye ta da mamaki duk da ta san A.m ya tsani abincinta kamar yadda yake mata ƙorafi.

" Ba' a waje yake siyo ba Juwairiya ce take girkawa,amma yau ban san mai ya hana ta fitowa ta girka ba."Tsabar gulma da yake cinta har saurin baki da take yi ta faÉ—a in ina ta fara.

" Juwairiya?"

Ta faÉ—a cikin zare ido don ita ko kaÉ—an ba ta tunanin ta na gidan ba.
" Wayyo Allah na! Uban me yar iskan yarinyar nan take min a gida?Da ma ta na gidan nan ba ta bar gidan ba."

Lantana ta matsa daga gefe tare da kare wuyanta ganin ta nufe ta,a ranta addu'a take yi.

BuÉ—e kofar kicin É—in ta yi ba tare da ta nuna ko É—ar a ranta ba,duk da ta ji hargoguwar Zainab sai dai hakan bai razanata ba.

Lokaci guda Zainab ta yi shiru lokacin da ta yi ido biyu da ita.

Gabanta ne ya yanke ya faÉ—i dam!Ganin ta canza mata kamar ba ita ba.

Wani irn tashin hankali ya ziyarce ta ba tare da wani tunani ba ,shaƙeta ta yi tare da sakin wani irin kuka.

"Ke dan ubanki mai kike yi a gidana?"

Juwairiya ta fisge gabar rigarta da ta riƙe ba tare da ta ce mata komai ba, ta nufi gurin gas za ta ɗora abinci,da ba tare da ta ji tsoron ta ba.

Lantana kuwa tsalle ta yi gefe jikinta har rawa yake ganin yadda hankalin Zainab ya tashi,duk ta ƙosa a fara ta ga yadda za'a ƙare, a zuciyarta ta so ace munafukin ya na nan,sai ta ga ƙarya da nuna isa ya na faɗa mata matarsa ce.
Chapter 67 · 0% Book details