← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 86

Sashe 63

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai tsananin mamaki ya kamata ta shiga kaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa zuwa can ta nisa ta ce." Har yanzu wannan ba hujja ba ce Zainab saboda wataƙila A.m ya na shan ƙwayoyin ne don yana tunanin ƙila ƙwayoyin Zai taimaka miki."

"Haba akan me za ki ce haka bayan na gaya miki cewar mahaifata aka yi min aiki aka cire.Kuma idan haka ne mai yasa ka bai gaya min ba"Ta faɗa cikin ƙosawa jin bin da ta ce.

" Wannan ma ba hujja ba ce har yanzu ba ki da hujja Zainab.Kina abu kamar ba likita ba bayan kin manta mahaifa takan tiƙo a jikin mace ko da an cire ta,mata nawa ne suka haihu bayan a n cire musu mahaifa?.Musamman ke da baki taɓa haihuwa ba."

" Wayyo Allah kin sani a ruÉ—u in kin ce duk wannan ba hujja ba ce,to numbar A.m da na gani a wayarta shi kuma mene ne?"Ta ce da ita tana kuka sosai.
" Ba zan ɓata bakina gurin faɗa miki irin son da nake masa ba.Na roƙe ki kamar yadda kika yi min alƙawarin za ki watsa mata acid ki taimake ni ki yi yadda muka shirya,ga bayanin in da take gidan kawunta wanda na samu labarin mahaifiyarta ta ɓata."

"Ok tun da haka kike so zan yi amma na so a ce mun ɗan ƙara lokaci,mu samu ƙwararan sheda, yau ɗin nan zan cika aikin ki na koma Abuja bari na gama cin abincin.Niƙabi zan saka na watsa ma shegiya ki huta.

BARI NA YI NAN DON YAU BANI DA TACE WA LAMARIN YAFI ƘARFINA.

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 28*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Zainab dake shatatan hawaye ta karɓi acid ɗin da ta miƙa mata,tana jin wani irin tsanar Juwairiya a ranta kamar ta je ta watsa mata da kanta.

Ganin Momy suka yi ta shigo tana murmushi a fuskarata ta zauna a gefen su.

" Humh ta yaro kyau take yi ba ta ƙarko."

Ta ce tare da dafa kafaɗar Zainab da har yanzu take ɗigar hawaye,saboda gani take kamar a mafarki yake faruwa,ba ta taɓa tunanin fuskantar haka da ga gare shi ba.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta saka tare da rungume Momy sai ta ƙara fashewa da kuka.

" Momy har yau na kasa yadda cewa A.m zai iya kula wata mace bayan ni,mace mara aji wanda ba ta da daraja a duniya duk cewar zargi nake yi amma in na tuna,sai na ji kamar na shaƙe kaina na mutu."

Cikin kuka ta faÉ—a da shagwaba gaba ki É—aya ta haye jikin Momy tana shagwaba,sannan ta É—ora da cewa.
" Ke sheda ce irin wahalar da na sha kafin ya amince da soyayyata! Yanzu sai wata aba wacce ban ɗauke ta da ƙima ba ta shiga tsakanimu.Abin da ya yi min na ji na haƙura da shi amma fa babu macen da za ta raɓe shi,face na zama ajalin ta."

"Na sani ba sai kin ɓata bakinki ba amm ni bana goyon baya akan acid ɗin da zaku watsa mata,saboda in har da gaske yake son ta zai iya yin komai don ta samu lafiya daga ƙarshe kin ga ke kika rasa,amma da za ki bar komai a hannuna da sannu za ta gane kuskuren shigowa rayuwarki da ta yi sa..."

" Momy yanzu kina nufin na fasa watsa mata acid É—in?"
Ta katse ta da tambaya tana magana da muryar kuka.

" Abin da nake so kenan in har zai yiwu kar ki manta ke ce ƴata ɗaya tilo da na mallaka, ta ya ya za ai na bar rayuwarki ta ƙuntata ki bar min komai a hannuna,mijinki kuwa sai ya gane bashi da hankali don wahalar da shi za muyi ki ƙyale shi,zai gane ba irin ki ake wulaƙanta wa ba."

" Ai ni da nace ba zan kona gidan sa ba kawai ya sakeni na haƙura da shi."Ta ce cikin shagwaba tare da riƙe hannunta.

" Ba ki da hankali mijinki za ki bar ma wata banza Æ´ar aiki? Ashe kishinki na banza ne tun da har za ki hau dokin zuciya ki kyale ma wata mijinki."

" Wannan karon Nabila ce ta karɓe maganar da cewa." Momy ya kamata ta fahimci waye mijinta sannan kin san Zainab da baƙin kishi,ni har yanzu na kasa gane gaskiyar lamarin dake faruwa,amma ya kamata ta gwara A.m ta nisan ta kanta da shi har sai ya gane kuransa.

Zainab cikin zumɓura baki ta ce." Ki bar shi da ni yake yi ba Anty Safna za ta tafi ingila ita da mijinta ba,bin ta zan yi na huta acan ba zan dawo ba sai na huta."

Nabila da mamaki ta kalle ta ta ce." Ki bar shi da Æ´ar aikin na ki Zey?"

" A''a na san cewa tun ranar da abin ya faru zai kore ta, so nake na gwara shi kin san yana masifar sona dole hankalin sa ya tashi."

Dariya ta yi ta ce." Haka ne ai bai kyauta ba amma yanzu Momy zuwana bai da amfani an fasa watsa mata acid É—in?"

" Ƙwarai kuwa Nabila ku bar min komai a hannuna ita Zainab ta fita waje ta huta kafin muga abin da zai faru."

Haka kuwa aka yi washegari Nabila ta koma Abuja.

A ranar da su A.m suka yi nasara Zainab ta fito musu sun ga rashin mutunci,don tun A k na saka baki yana ba ta haƙuri ta dawo,har ya gaji ya koma gefe yana kallon A.m da ya yi kalar tausayi,kamar zai yi kuka yana roƙonta.

Cikin muryar sanyi ya ce." Ki fahimce ni tun lokacin da muka je ƙasar waje aka yi miki aiki,na tambayi likita ya ba ni wannan maganin tunanina ko za ki iya haihuwa."

Kallon mayaudari ta yi masa ba tare da ta tanka masa ba,domin gani take ya ci uwar rainin wayo.

" Allah ki yadda da ni don Allah ki dawo É—akina zuciya da gangar jiki sun yi kewarki."
Ya faÉ—a a raunane kamar zai yi kuka tare da kama hannunta.

Fisge hannunta ta yi ta harare shi tare da yatsina fuska." Ai ka gama tsarani wallahi gara ma ka fita harkata,domin zuwa gobe in sha Allahu na bar ƙasar nan ba zan dawo ba saina huta iya son raina."Ta ce da shi tana kallon sa a yatsine

Wannan karon murya a ɗage ya fara magana." Kar ki sake ki fita wata ƙasa don ba da izinina ba,kuma in kika sake kika je Allah saina ɓata miki rai"

" Ai kin banza kawai a suwa ai ni yanzu duk abin da ka zaɓa a aurenmu daidai ne in ba rabuwa za mu yi na fi son haka,da na zauna da fasiƙi wanda ba shi da aji ya rasa macen da zai kula sai ƴar aiki.."

" Ya ishe ki Zainab sau nawa zan gaya miki babu wani abu da ya shiga tsaƙaninmu da ita kin ƙi bani dama na yi miki bayani,ban taɓa kallonta da nufin wani abu ba don ni ban ga abin da zan nema ajikinta ba,kar ki manta yawo take a cikin hijabi kamar wata ƙonanniya.Yarinyar da ba ta da waye wa mai zan yi da ita...."

Zainab tsaki ta yi ta wuce kawai gani zai tsarata ya bita kamar zai shige cikin ɗakin ya na faɗin." Na gaya miki kar ki bar ƙasar nan ba tare da izinina ba."

Garam ta kulle ƙofar saura kaɗan ta haɗa da hannun shi da ya kai da nufin ya kamo ta ganin za ta shige.

Bango ya kaima duka tare da kama kan sa ya riƙe.
A.k da ke zaune hankalin sa na kan waya amma a zahirin gaskiya yana jin badaƙalar da suke yi ne,mamakin aminin na sa yake yi saboda ya saki da yawa Zainab ta raina shi sama ba ta ganin darajar shi balle ta girmama auren su.

Ganin ya nufi hanyar fita ya miƙe cikin ƙosawa shi kansa ya gaji da zuwa biko,yana ji a ran sa ba zai ƙara rako shi ba don ya gaji da ruwan rashin mutuncin da yake kwankwaɗa daga gurin Zainab da iyayenta.

A mota suna tafiya shiru A.m ya yi ƙuta ya kalli A.k da hankalin sa ya na kan tuƙi ya ce." Ka na jin wannan yar rainin wayon ko,wai wata ƙasa za ta!Zainab ta raina ni matuƙa ban san yadda zan yi da ita ba,amma in dai ta yi gigin fita waje Allah sai na hukuntata."

Shiru A.k ya yi ba tare da ya tanka mishi ba yana tuƙin sa a ran sa cewa ya yi." Kamar da gaske zai iya."

Ƙaramin tsaki ya yi ganin haka sai A.m ya kama bakin sa ya yi shiru bai ƙara cewa komai ba,don maganar da yake masa kame-kame ne lamarin Zainab yana ba shi haushi sosai.

" Har yanzu ban ji kayi maganar Juwairiya ba."A.k ya faÉ—a ba tare da ya kalle shi ba.

" Shiru ya yi ba tare da ya tanka ba duk da ya É—an daina jin zafin ta amma har yanzu yana jin haushin asarar da ta yi mishi.

" Ka rabu da ni da wannan shiriritacciyar ina maganar matar so wake ta matar shige,sai ka bari na gama da wanda zuciyata take muradi ba wata can ba."

Tuki A.k ya ci gaba da yi ba tare da ya tanka a bin da ya ce ba a ran sa shika É—ai ya san me yake tunani.
Chapter 63 · 0% Book details