Sashe 85
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk yadda likitan ya so ya raba hannun su, amma ina ya ƙasa saboda sun riƙe junansu ƙaƙam,sun ƙi saki daga ƙarshe kan dole ya ƙyale shi.
Duk iya ƙoƙarin su jaririn ya ƙi fitowa,amma kuma in suka saka hannun suna taɓa kan sa.
Hankalin su ya tashi matuƙa gashi a lokacin ƙarfinta ya ƙare,ko motsi ba ta iya wa balle ta yi nishi,sai idanunta da take wulƙita su cikin raɗaɗin azaba.
" Ina gani ya kamata a kira doctor Garkuwa don shi kawai zai iya maganin wannan matsalar,ƙila ya ce a shirya mata aiki fa,domin ba ta da ƙarfin da za ta iya nishi yaron ya fito."Doctor Bilal ya ce da doctor Marwan.
" Ba ya ƙasar ka san ya yi tafiya zuwa ƙasar America akan ƙwallon gasar ƙafa da zai buga."
" Kai wai me ya saka doctor Garkuwa yake yin haka! Sai ka buɗe asibiti amma ba za ka rinƙa kulawa da patient ba,kullum ba shi da aiki sai zuwa ƙasashen waje akan ƙwallon banza,wanda iyayensa ba sa son yana yi Yanzu ya yake son mu yi da wannan baiwar Allah da take cikin wani hali?"Ya faɗa cikin tashin hankali.
" Waye wannan Garkuwa mahaukaci ne shi zai fifita ƙwallon ƙafa akan mutane?Na rantse in ya kashe mini mata sai na kashe shi ko kuma kotu za ta raba mu."A.m ya ce cikin hargowa bayan ya shaƙe likitan.
Da ƙyar ya ƙwace kan sa ya ce." To sakar mini riga shi ma ɗan zafin rai ne kamar kai sai ka bi shi can ku ƙarata."Ya ce tare da ƙwace rigarsa.
" A nemo amininsa doctor Isa abin takaici jiya ya gama duting dar."
" Ashe asibitin mahaukata na kawo matata ba ku da hankali,asibintin ya zama ƙyalƙyali banza,ba ku damu da halin da take ciki ba,to bari na gaya muku in har Juwairiya ta mutu kuma duk sai na kashe ku."
Likitan ya buɗe baki zai yi magana da fushi ganin ya raina ƙoƙarin su,sai suka ji kukan jariri da ya kusan faɗowa ƙasa,wanda taimakon Allah kawai ya fito da shi daga cikin.
" Wayyo Allah na! Ƴaƴa biyu! Wallahi ƴaƴa biyu kika haifa mini gaskiya aurenmu mai albarka ne." A.m ya faɗa yana kallon jaririn da ya daina kuka saboda wahalar da ya sha.
" Na yi mata allurar tsaida jini amma ya ƙi tsaya fa."Nurse ɗin ta ce cikin tausayin wahalar da take sha.
Shiru kawai ya yi ya tsaya yana tunanin wace alllura zai ƙara yi mata,kafin wannan mahaukacin mijin na ta ya farga.
Hankalin su ya tashi ƙwarai duk yadda suke ɓoye-ɓoye sai da ya fahimta,ya riƙe hannunta ƙam yana hawaye." Juwairaaah na ga tashin hankalin dama haka mata suke wahala in za su haihu? Allah Sarki Momi zan kasance mai yi miki biyayya har ƙarshen rayuwa,zan miki duk abin da kike so duk da na san ko mai na yi miki ba zan taɓa biyan ki ba.Bazan raba ki da yaran ki ba Juwairaah domin in na yi haka Allah sai ya hukunta ni,wallahi kin biya ni komai da kika haifa mini yara har biyu duka maza."
Ba ƙaramin wahala su ka yi ba kafin su tsaida jinin,don har idanunta sun fara ƙaƙƙafewa.
Ya tsura mata idanu yana kallon fuskarta da idanunta ke rufe tana saukar da numfashi a hankali.
Kiran sallar asuba na farko ya sa shi ya miƙe sai kuma ya kalli jikinsa,ba tare da ya shirya ba dariya ta kama shi ganin duk wannan diramar da ake kayan bacci ne a jikin sa.
Wayarsa ya É—auka yana kiran mutane yana gaya musu,don a ranar har wanda bai kamata ya gaya wa Juwairiya ta haihu ba,sai da ya gaya musu,saboda in dai zai ga numba a wayarsa sai ya kira ya faÉ—a musu.
A.k ya fara isowa cikin asibitin kafin ya shigo sai ga motar su Daddy kowa yana rige rigen shiga,don ko gaisawa ba su yi da junan su ba.
" Wallahi ta haihu ka gan su ni ma na zama Baba Allah Daddy za su rinƙa kirana suna gudu suna bina,kuma fa kama da ni suke yi har da tabon fuskata."Ya ce da A.k da ya sawo kai cikin ɗakin yana nuna masa yaran da suke cikin shawul,duk da ba su taho da kaya ba,amma tsarin asibitin ne komai na buƙata a kwai.
" Ikon Allah ka ga sabon shiga yara biyu a lokaci ɗaya! Gaskiya Juwairiya ta iya haihuwa.Amma na kasa gane tsakanin kai da ita wanda ya yi naƙudar duba ga yadda jikinka ya ɓace da jini."Ya faɗa yana dariya bayan ya karɓi yaran a ran sa yana ta ya amininsa murna.
A.m ya ji kunya sosai saboda iyayensa da suka shigo shafa kan sa ya yi ya ce." Bari kawai ƴar albarka ta ci baƙar wahala,amma duk da haka bayan shekara za ta rinƙa kawo mini kyawawan yara irin waɗannan."
Momi kuwa rungume yaran ta yi ta saka kuka sosai." Ikon Allah ashe a kwai ranar da zan ga yaranka Abdul,sam ba ka kyauta mini ba da ka ɓoye mini wannan lamari,don kawai ka birge wata mace can wacce ta cuci kanta da kanta,wai kai ɗan soyayya haka kawai ka hana ni ganin sanyin idanuwana jikokina."Momi ta ce tana goge hawaye.
" Sha kuruminki Momi duk da cewa ana shan wahala amma duk shekara za ta rinƙa kawo miki irin waɗannan."Sai ya haɗa hannunsa ya kama mahaifiyarsa ya rungume yana hawaye.
" Momi tabbas na ƙara girmama lamarin uwa a raina ashe haka mata suke shan wuya kafin su haihu!Mutuwa ce kawai ba ta yi ba.Momi zan miki biyayya har ƙarshen rayuwa,ko da wuta kika tura ni zan shiga."
Kama hannunsa ta yi ta haɗa." Kana yi mini biyayya Allah ya yi maka albarka ya shirya maka zuriya." Sai kawai ya saki ƴar ƙara yana dukan A.k ya ce." Yes ni ma na kai lokacin da za a yi ma yarana addu'a."
" Ya A.m ina Anty Juwai É—in?"Hamdiya ta tambaye sa don burinta ta gan ta.
" Kull karki ƙara ce mata Anty ai daga yau ta girma Maman ƴan biyu za ki ce,saboda kin rage mata matsayi."Dariya suka kwashe da shi.
Bayyana irin farin cikin da suka shiga abu ne mai wuya musamman A.m, da yake ji a ran sa dole sai ya yi sadaka don bai taɓa tunanin haihuwa ta farko,za ta haifa mi shi zuƙa-zuƙan yara har guda biyu kuma duka maza.
Gida ya dawo don ya yi wanka sannan ya yi wa Zainab albishiri,saboda ya bar ta cikin jimamin halin da ake ciki.
A lokacin gari ya waye ko da ya dawo tana ɗakinta ga mamakinsa sai yaga tana bacci,don haka bai tashe ta ba ya wuce bayi ya yi wanka,sannan ya saka turaren da yake so don ya san daga yau ba za ta ƙara yi masa ƙorafi ba.
Wani irin gayu ya yi cikin murna da annashuwa bai taɓa tunani yana sonta haka ba,da ya duba halinta da haƙuri ga kula da ibada sai ya ga tabbas ta ya kamata a so ta,uwa uba kuma girkin da take mi shi.
Ya auna tsaƙanin son Zainab da ita wa ya fi so sai dai shi kan sa ya rasa ganewa,domin har yanzu yana son Zainab saboda soyayyarta daga Allah ne,bayan nan ga tausayinta da ya cika mi shi rai,ya san cewa za su kai ruwa rana in ya gaya mata abin da ke zuciyarsa,amma ya zai yi ita zuciya ba ta da ƙashi,shi kan sa ba yin kan sa ba ne Allah ne ya saka mi shi sonta a cikin zuciyarsa,domin zuciya an halicce da son mai kyaukyata mata.
Ya sauko zuwa falo har ya É—auki makullin mota zai fita, sai kuma ya tuna bai yi magana da Zainab ba,da sauri ya juya zai haye saman,a ran sa yana ma kan sa faÉ—a dole ya yi adalci a tsakanin su.
Matuƙar kunya ta kama shi ganin ta a saman bene tsaye da kayan bacci tana kallon sa,sosai ya ji kunya don fa har ya murɗa kofa zai fita ba tare da ya yi mata magana ba.
" Inna lillahi! Tabbas zuciyata ta gaya mini yau A.m ya yi sabon abu, wanda ya saka har ya manta da ni Zainab wacce yake iƙirarin ba zai taɓa rayuwa babu ita ba."Ta faɗa yayin da idanunta suka kawo ruwa don ko bai gaya mata ba,farin cikin da ke ɗauke a fuskarsa ya bayyana hakan.
Dawowa ya yi da sauri ya hayo in da take." Tabbas ta haihu Zainab na ci ƙwallon Juwairiya ta haifa mini yara kyawawa har guda biyu."
" Wayyo Allah na!."
Ta faɗa tare da zubewa ƙasa ta dafe kanta tana jin wani irin tashin hankali."
Kamata ya yi ya rungume ta kalle shi da hawaye a fuskarata." Na shiga uku da gaske yau ka samu abin da za ka raba mana soyayya da su?Kuma ba yarana ba?"Ta ce cikin kuka.
" Haba Zainab ke da za ki yi murna Allah ya albarkance mu da yara har biyu,bai kamata ki nuna tashin hankali a rana irin ta yau ba.Na gaya miki babu abin da zai saka na raba son da na ke miki har yanzu son ki na nan a cikin zuciyata sa..."
Tura shi ta yi ta miƙe ta ce " Ka barni na yi kuka domin ya zama dole a rayuwata,haihuwa fa ka yi da wata mace yau ko mutuwa ka yi Allah ya cika maka burinka ka samu magaji,ni fa A.m ba zan taɓa haihuwa ba duk da tarin dukiyar da na mallaka.Kaga ya zama dole in yi kuka ko abin da ya fi kuka."Kawai sai ta rushe da kuka ta kama ƙarfen benen ta riƙe bayan ta miƙe tsaye.
" Haba Zainab yarana ai naki ne na har abada bai kamata ki ce haka ba,kuma na yi miki alƙawarin ba zan taɓa nuna miki wani abu akan yaran ba,sannnan zan kasance dake har ƙarshen rayuwata in har ina numfashi a duniya."
Tun Zainab na kuka yana rarrashinta har ya gaji ya miƙe ya ce." Bari na kai kaya ana ta jirana." Ya fice daga gidan.