← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 86

Sashe 38

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A.m ya na ganin ta shige ya bi ta tare da tura ƙofar a hankali ganin ya shigo ta tsaya dama tun da ta shigo ta rasa mai za ta gyara saboda ɗakin ya na tsaftace da kyan sa.

" Ki zo mu kwanta a gadon da baki taɓa hawa ba amma albarkacin aurena zai saka ki din ga moresa in matar so ba ta nan."

Hawaye suka wanke mata fuska ba ta ce mishi komai ba kuma ba ta motsa ba bare ya saka ran za ta hawo,asalima gaban ta ne ya faÉ—i ras!

Hannunta ya jawo ya na faɗin." Na lura kuka shi ne farin cikin ki to ki sani ba zan taɓa buɗe bakina rarrashe ki ba,ko na ɗauki hannuna na share miki hawaye da su.

Yanayin da suka shiga a ranar yanayi ne mara fasaltuwa da bayyanuwa a gare su musamman Juwairiya da ta sha kuka har ta gode ma Allah,domin kwana ta yi ta na kuka ko kaɗan ba ta bar shi ya rintsa ba,wanda in ta tuna dalilin kukan na ta biyu ne sai ta ƙara sakin wani kuka.

A.m da bacci ya fara ɗaukar sa a hankali bayan wata sabuwar duniya da ya shiga kuma ya kasa fahimtar wace duniya yake ciki,kukan da take yi ya na ɗaga masa hankali ya yi maganar duniya taƙi yin shiru,har ya gaji ya ƙyaleta ya rintse idanun sa da ƙarfi ya na son bacci ya ɗauke sa.
Ganin taƙi dai na kukan ya janye bargon da ya ƙudundune kan sa da shi ya kunna fitilar ɗakin."

Ke wai ke."

Sai kuma ya yi shiru daga ninyar faÉ—ar da yake ya yi mata ya É—an sausauta murya ganin dare ne ya ce." Ko fa wace mace da kika gan ta a gidan mijinta da haka ta fara.Kuma idan bakya son haka ba sai ki gaya min ki gode ma Allah auren kwangila muka yi so ba daÉ—e wa za ki yi da ni ba."

Hakan sai ya saka Juwairiya ta ƙara fashewa da kuka ganin ta ba ma mutumim da ya tsane ta rayuwarta,ga shi bai san mahimmancin ta ba bayan wahalar da ta sha yake gaya mata waɗannan kalamai.

Bakinta ta murguɗa a ranta ta ce." Mugu kawai azzalimi."sai kuma ta ci gaba da kukanta wanda A.m ya lura harda shagwaɓa don shi ya gama fahimtar ta shegen shagwaɓa ne da ita shi ya sa da an yi magana sai kuka.

Wani irin walƙiya a ka saki lokaci guda aka fara tsawa nan ne A.m ya fahimci garin hadari ne ya taso,da sauri ya sauka don ya duba ko windina a kulle ne kawai sai ya tsinci kan shi da jin daɗin ya na yin garin har ya buɗe labule ya na shaƙar iskar gurin.

Iskar ya ƙara ma Juwairiya zazzaɓin da ta ji ya saukar mata ganin haka sai ya rufe windon ya na addu'ar Allah ya sa ta yi shiru kenan,jin ta sassauta sautin kukan da take yi sai ya koma ya zauna.

Wayar sa ta fara ruri da sauri ya ɗauka don gabansa ya faɗi ya na tunanin waye da daddare zai kira shi,ganin numbar masoyiyar sa ya sa shi miƙewa da sauri take ɓacin rai ya bayyana a fuskar sa.

A wannan lokacin da yake duba wayar sa aka tsuge da ruwa sosai kamar da bakin ƙwarya.
Zubbur ya miƙe ganin numbar Zainab ce ya yi kamar ba zai ɗauka ba,saboda tun da ya gaya mata zai dawo ta de na ɗaukar wayar sa ashe mara mutuncin tafiya ta yi tabar ƙasar.Sai kuma ya kanga wayara a kunnin cikin tsanani ɓacin rai a ransa ya na tunanin Allah kawai zai raba ta da shi.

" Hello zauji don Allah gani a airport ka zo ka É—auke ni kuma na samu Æ´ar matsala da kayana har mutumim ya na min barazana.Ga kuma ruwa da ake yi kazo ka ji zauji."

Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi ya kalli Juwairiya da take cikin wani hali don shi kan sa ya san ya wuce gona da iri,kuma ba tare da sanin haka ba ya kuma kalli kansa da har yanzu ya kasa tantance duniyar da yake ci.

Tunani ya fara yi ko Zainab ta hauka ce ne da za ta dawo da tsakar dare sai ya ɗauki wayarsa da nufin ya duba lokaci, ai wallahi ba zai fita yanzu ba sai dai koma mene ne ya faru musamman da ta ɓata masa rai ta yi tafiya ba tare da izinin sa ba.

Tsananin mamaki ya kama sa da agogon wayar sa ya nuna mishi ƙarfe biyar da mintuna,ya na cikin kokwanton ko wayar sa ce saitin ta ya goce sai ya ji ladani ya kwaɗa kiran sallah.

Da sauri ya yaye labulen ɗakin don ya ƙara tabbatar ma kansa take kuwa ya ga har hasken alfijir ya keto gari ya fara wayewa..
Sai hankalin shi ya ƙara tashi musamamn da Zainab ta turo masa tsaƙon ba sai ya zo ba,don sun daidaita da mutumim yanzu haka ma suna hanyar gida,saboda mijin Anti Fati ya turo direba ya ɗauke su kuma duka za suzo gidan.

TO FA JUWAIRIYA GASKIYA NA TAUSAYA MIKI DA RANAR KI TA KASANCE A HAKA KOMAI DAI MENENE ALLAH YA BAKI HAƘURI DA JURIYA.KUCI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN SAKACINA KO HALIN MAZA

NAƘI YIN TYPING DA YAWA SABODA GASKIYA FANS BA KWA RUWAN COMMENT SAI DAI KU YI TA BIYO NI TA PC KUNA FAƊIN ALLAH YA ƘARA FASAHA INA GODIYA AMMA NI NA FI SON NA GA RUWAN COMMENT YA NA TASHI DON GAKA IN KUNA SON NAADIN GA TYPING DA TSAWO KU DIN GA COMMENT.

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO

ÆŠUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ÆŠIN KU YA NA SAKA NI NISHAÆŠI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha shidda.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 19*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

A.m ya shiga cikin tsananin tashin hankali ya juya ya kalli Juwairiya da take jin duk abin da yake faruwa,ga jikinta sai kyarma take yi har ta fara haɗa haƙori kar-kar!

Sai tashin hankalin sa ya nunku ya kuma rasa tunanin da zai yi.Hannunsa ya sa ya tallafe kan sa can kuma ya shiga shafa sumar kan sa ya na tunanin mafita,don shi babban tashin hankalin shi da Zainab ba ita kaÉ—an za ta dawo ba ya san ce wa ta ce su zo ne su rarrashe shi.

Wayarsa ya zaro ya yi kiranta ringing ɗaya ta ɗauka ta na kashe murya ta ce." Hello Habibina ai mun kusa ƙarasowa gidan..."

Wata uwar tsawa ya daka mata da ya firgita ta ya ce." Ni ko Zainab wallahi in kika shigo gidana na da waÉ—annan dabbobin sai na yi miki mugun rashin mutunci,don haka ki ce musu ko wace banziya ta kama gabanta tunna su mahaukata ne.Kuma zaki dawo zaki ga abin da zai faru! Allah ya sa su yi gangancin shigowa gidan."

Da fushi yake magana tamkar ta na gaban shi don iya abin da zai yi kenan ya hana su shigowa cikin gidan.

Zainab ta yi shiru da waya sororo a hannunta, ta rasa ya za ta yi ga shi ta gama koɗa kanta ta isa da shi,don sun nuna ƙin zuwa saboda sun san halinsa ba kamar mazajen su yake ba.
" Kai direba tsaya wallahi Zauji yau rashin mutunci yake ji kun ji abin da ya ce."
Ta faÉ—a a kunya ce ta na kallon su.
"Mai ya ce É—an rashin mutuncin?"
Anty Fati ta tamabaya don ta san za'a rina sanin hali."Gaskiya ko wace mace ta tafi gidan ta ku sauke ni anan kawai ina ga Æ´an iskan Æ´an uwansa sun zuga shi ne,amma da amincewar sa na tafi Dubai yanzu ya na faÉ—a min kar ku zo mishi gida ."

Ta faɗa a kunyace don ya ba ta kunya ga shi ta gama zuga musu ƙarya." Kar ki yadda Zey ya haɗa ki fita kin ga dai irin ribar da muka samu,ki nuna mishi turjewar ki."
Anty Fati ta faɗi cikin maganar zuga ta na son ta ƙara zuga ta don ta shirya duk abin da yake ji.
" Ke ma kin san halina kawai ba na son ya wulaƙanta ku ne ku je kawai ni wallahi akan sana'ta zan iya haƙura da aikin gwannati bare kuma ya ce zai kawo min cikas."

Anty Maryam da ba ta ce komai ba ita ma ta na tunanin abin da za ta tarar,in ta koma sai yanzu ta yi magana ta ce." To ki rabu da shi mana yadda kike da kyan nan ai kin san ki na fita za'a wawushe."
Wani mugun kallo ta yi mata tamkar za ta kai mata duka ta ce." Ka ji Anty Maryam da maganar banza ni da Hubbi ai mutu ka raba takalmin kaza! So kike na kashe aurena na je na auri mai mata ko wanda zai yi min kishiya nan gaba,hakan ma ba zai yiwu ba don ni da kishiya ko a lahira ba na fata kuma zan iya yin komai a kanta ni da ita yaƙi ne tsakaninmu."
"To ki tafi mana ga shi har yanzu ana yayyafi kuma kin buÉ—e mota kin tsaya ki na zuba,don kawai an miki maganar kishiya duk da family É—in mu ba'a mana kishiya, amma Zey ki rage kishin ki to ke da mijinki ba ya haihuwa wace mace za ta zauna da shi ai sai ke Æ´ar wahala."
Chapter 38 · 0% Book details