← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 86

Sashe 12

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma kina ganin tijarar da yake mana ko?Kin san halin shi ba shi da kirki,ni fa bana son tashin hankali ya dinga jibgar ki a banza."
Juwairiya shiru kawai ta yi a ranta ta saka komai zai faru sai dai ya faru,amma aikin Anty Naja yanzu ta fara.Hankalin Mama ya tashi da safen ranar da ta gama hutun ta bayan Juwairiya ta yi sallah ta tafi aikin ta,ba ta kula da kiran da Mama take ƙwala mata ba.

Da yamma da ta dawo Baba Sani ya shigo da bulalarsa ya yi mata duka,har bata iya tashi amma ba hana washegari ta koma aikin ta ba.Ganin irin dukan da yake mata Mama ta hana ta aikin,sai dai wannan karan ta bijire ma umurnin ta don ta rantse ko kashe ta zai yi ba za ta bar aikin ba.

Tsakanin ta da mijin Anty Naja ba ruwanta da shi tun da ta fara aikin so uku ta gan shi,duk sanda ya shigo ya ga yaran a kusa da ita sai ya fara musu faɗa ya kora su cikin ɗaki ya na harararta ya na mazurai,a yadda yake mata ta lura ya matuƙar tsorata da halin masu aiki.

Ganin haka ta ƙara kame kanta ta na mamakin yaran duk da suna zuwa islamiya amma ba su wani iya karatu ba,don ko babban dake da shekaru tara ko alhamdu bai iya cikakka bare ya damu da sallah ba,sai kallon catoon da suke yi kullum ba ƙauƙautawa,ganin haka ta dage da koya musu da saka su su yi salla,abin da ya ƙara saka Anty Naja son ta a cikin zuciyar ta.

Ganin Æ´an canjin da yaransa suke samu abin ya burge shi har yake amsa gaisuwar ta a sake,wani lokacin har kyauta yake mata na kuÉ—i yace ta kaiwa mahaifiyarta don Anty Naja ta gaya mishi mahaifinta ya mutu.

Kusan kullum Juwairiya ta dawo sai taci na jaki a gurin Baba Sani jikin ta duk shatin duka ne,amma hakan bai saka ta karaya ba ta ci gaba da aiki don yanzu suna ci ga Mama dake sana'ar ta rayuwar su ta na tafiya cikin rufin asirin Allah sai dai takurawar da Baba Sani yake mata,wanda hakan ya na damin Mama ga shi taƙi ta dai na aikin.
A haka rayuwa take gara musu yau fari gobe tsumma,yayin da kullum burin Baba Sani ya cika burinsa amma Allah bai ba shi damar ida mugun nufin sa a kanta ba.Ganin haka sai ya ɓullo mata da nuna mata kuɗi ya na jan ra'ayin ta akan ta amince mishi ko sau ɗaya ne,amma taƙi duk ta gan shi sai ta nemi tsari da sharrin sa don ganin sa take kamar wani sheɗani.

Ta ɗauki tsawon shekaru biyu ta na aiki a gidan Anty Naja,a lokacin ta girma ta ƙara wayewa ga hankali da natsuwa kullum cikin hijabi take bata cirewa sai in mutanen gidan ba sa nan,ko ita Anty Naja ba za ta ce ga yanayin jikin ta ba,don tun kafin takai haka da Baba Sani ya saka mata ido ta yi tunanin ko jikinta yake ruɗarsa,bare yaanzu da ta zama ƴan mata ta cika ta batse ga Anty Naja da take ba ta kaya masu kyau kuma ta ba cin me kyau,har mai na shafawa da na wanke kai take siyar mata.
Maza da dama sun sha bayyana soyaryarsu gurin ta wasu kuma suje gurin Baba Sani,amma sai ya taƙarƙare yace Juwairiya ƴar mace ce sannan ba ta da kamun kai har kwana take a waje.Ya faɗi mugun abu da ba ta mata suna ya gaya musu,wasu suna jin haka za su tafi wasu in suka nace ya yi musu korar kare don ya rantse,in har ba ta amince mishi ba to ita da aure sai dai ta ga ana yi ko kuma in ya mutu.

Juwariya yarinya mai kimanin shekaru sha tara.Ta na da haske amma ba can ba,fuskarta mai kyau irin zagayayen fuska gareta,da dogon hancin ta haƙoran ta masu kyau ga ƴar wushiryar ta a tsakiya,wanda in ta yi dariya yake ƙara ma kyau matuƙa!Da dimful ɗinta.Bata da jiki amma a kwai shafe sannan doguwa ce ba can ba,amma ta na da tsawo wanda yake ƙara mata kyau.

Ƙirar jikinta me kyau ne ko ita ta na alfahari da hakan wato irin jikin nan ne mai ɗaukar hankali waɗanda ko wane namiji yake burin samu mace mai irin sa.Wannan dalilin ya sa kullum take cikin hijabi do ko ƙawayenta suka shigo suka gan ta ba hijabi,sai su yi ta zuzuta ta su na yaba kyawun jikinta.

A wata ranar litinin da safe bayan mutanen gidan sun gama karyawa suka wuce gun aiki,kasancewar da garin a kwai zafi sannan Anty Naja ta tura mata da tsako a cikin wayarta me botira da ta siyar mata,don ta din ga kiran ta ko kuma in ta tafi aiki da wuri ta gaya mata abin da za ayi,don yanzu girkin su ya dawo hannunta saboda Baban Abnaj yafi son girkinta.
Waina da miyan karas za'a yi da farfesun rago,ganin ta na da aiki ya sa ta zage damtse ta na yi tun ta na cikin hijabi har ta cire ta na ta aikin ta,ta kunna wayarta ta na sauraron karatun kur'ani cikin suratul ma'ida.Ta shafa'a ta na ta aikin ta sai ƙanwar Abnaj mai suna Ibtihal ta danna remote ta ɓata saitin tibin,Abnaj ɗan shagwaba ya saka kuka ya zo ya na sanar da Juwairiya akan ta zo ta gyara musu.

Hannunsa ta kama suka nufi falon da nufin ta gyara mishi,ta na tsaye a gaban tibi ta na ta ƙoƙarin yadda za ta gyara amma ta kasa gashi ita ba ta san yadda ake yi ba,sannan gashi har sun fara kuka akan a gyara musu.
A hankali ya buɗe ƙofar ya shigo da sallama a bakinsa,Juwairiya da hankalin ta ke kan tibi ba ta san ya shigo ba,ko in ce dukan su sai bayan ya ɗauki tsawon lokaci ya na kallonta cikin mamaki a ransa ya na mamakin dama a kwai wannan halittar a gidan sa?Don shi zai rantse bai taɓa mata kallo ko na sakan bane ya san dai ta na da kyau a fuska.

"Oyoyo Daddy!"Abin da yaran suka ce kenan wanda ya ɗauki hankalinta ta miƙe a razane ta yi diri-diri,tamkar za ta shige cikin ƙasa yayin da wani irin kunya ya lulluɓeta.
Ganin yadda ta diririce sai ya shige ɗakin sa akan ya ɗauko abin da ya saka shi ya dawo saboda mantuwa da ya yi,wato wasu fayal da ya ije da nufin ya tafi dasu sai gashi ya manta da su kuma ana buƙatar su.Ashe da rabon ya yi gam da katar!Don shi ya ga matar aure dama tuni ya yaba da hankalinta.

Ko da ya shiga cikin ɗakin wani irin kasala ya ji y rufe shi ya faɗa kan gadon shi ya na jin wani irin shauki na ta ya na zagaye ilahirin jikin shi.Ko da ya shiga ɗakin faɗa kan gadon sa ya daɗe ya na jin wani girmar lamari har na tsawon lokaci,sannan daga bisani ya miƙe ya ɗauki fayal ɗin ya fito.

Kawai sai ya tsinci kansa da bin hanyar kicin ɗin ya ɗan tsaya nesa da kicin ɗin zuciyar sa na bugu da ƙarfi,take yake jin lamura suna sauya mishi har ya fara dana sanin dawowar sa gida gashi komai na son ya canza musamman akan yarinyar da take ba shi girma

"Abnaj fito na gyara muku tibin ku barta ta yi aikin ta,kun dame ta da surutu."Yace da yaransa da suke kicin É—in suna ta zuba da Anty Juwairiya kaza,ita kuma ta na ta yi musu dariya ba yan ta basu kwan da ta soya musu.

Yaran suka bi shi suna murnar zai gyara musu tibi,bayan tafiyar sa ziciyar Juwairiya ya buga dam!Da ta kalli ƙwayar idanunsa cikin rashin sani ganin yadda ya kafa mata idanu lokaci guda,abin da ta hango ya matuƙar tsorata ta wanda bai yi kama da so ba sai tsantsar sha'a warta da ta hango.In ko haka ne abincin ta ya ƙare a gidan.

Bayan fitar sa ta ɗaga labule ta na kallon farfajiyar harabar gidan,sai kawai ta ji hawaye ya na sauka a kan ƙuncinta bai yi kama da mutumim banza ba saboda ya na da dattako.To me ƙwayar idanunsa suke nuna mata?Ita kuma irin na ta jarrabawar kenan?

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na takwai.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA TAKWAS*

Tun daga wannan ranar Juwairiya ta ga canji a tattare da shi,ya sakin mata sosai kuma ya na matuƙar kyautata mata,ko hira yake da matar shi sai kiji ya tsoma ta ciki yace"Wai haka aka yi Juwairiya ita za ta faɗi gaskiya."

Ranar da ya fara mata hakan ta yi matuƙar razana ta kalli Anty Naja ta ga ko me za tace amma sai taga sai dariya take ta na jin daɗi har ta na ƙara tambayar Juwairiya,wani tsabar takaici kaɗa kanta kawai ta yi ta shige kicin ɗin wanda dama shi ya ƙwala mata kira don kawai ya tambaye ta.

Bayan sati É—aya sai gashi ya dawo gidan da wuri da yake a ranar matar sa na gurin akin ta na night duty acan za ta kwana.Bayan ya yi sallar magariba ya kulle ko ina na gidan ya shigo,tun da taga ya dawo da motar sa ya wuce masallacin kofar gidan sa gabanta ya faÉ—i hankalinta ya tashi,domin ita canjin da ta gani a gurin sa ya na tsorata.
Chapter 12 · 0% Book details