← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 86

Sashe 58

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Haka ne Ibrahim zuciyata ta fara hasasomin haka,sai dai ina zargin duk abin da ya faru a kwai saka hannun Baba Sani a ciki.Zuciyata ta fara zargin in da ya tura Juwairiya ba alkhairi ba ne,sai dai ina É—an jin sanyi ne, in na tuna da Juwairiya yarinyar kirki ce,na yadda da tarbiyar da na ba ta sam ba na tunanin za ta aikata abin da nake zargi,duk da cewa ba'a shedar É—an yau."

Hannu ta É—ora a ka yayin da gabanta ya faÉ—i ras!Sa'ilin da wani tunani ya faÉ—o mata.

" Kar dai a ce Baba Sani ya yi mini ƙarya ne akan aiki zai kaita,ya saka ta a hanyar banza?"

Ta tambayi Ibrahim da take tunanin bai fahimci abin da take nufi ba.
Mama ta saki ƙara tare da zubewa a ƙasa tana faɗin." Ya Allah na kasa samun natsuwa zuciyata,na shiga ruɗanin halin da Juwairiya take ciki,kar a ce Baba Sani ya ɓata mini tarbiyar da na gina ta akai,ya saka ta a harkar banza.Kar a ce da kuɗin da take aikata alfasha muke ciki."

Sai ta girgiza kanta tana kuka da ƙarfi ta ci gaba da faɗin. " Iya tsawon yaushe zan zauna a wannan gidan ba tare da na san gaskiya ba,in har Juwairiya ta canza tarbiyar da na ba ta tabbas ba zan iya yafe mata ba,domin na ci burin na ga na aurar da ke Juwairiya kar ki yi mini haka."

Da sauri Ibrahim ya taso ya rungumeta yana rarrashi ganin tana son ta fita hayyacinta.

"Mama mu bi abin da sannu-sannu kar ki aibata ta,na san cewa sam Anty Juwairiya ba za ta aikata haka ba,tabbas a kwai abin da ke faruwa.Kuma duk wanda ya sa aka kawo mu cikin wannan daular,to a kwai saka hannun Baba Sani a ciki don zuciyata ba ta yadda da irin sanyin da ya yi ba,lokaci guda ya zubda duk wani makaman sa akanta."

Mama ta shiga cikin tsananin ruɗani ƙwarai ta yi ihu ta yi kuka,tana roƙon mutumin da ya taimaketa ya gaya mata abin da ke faruwa,amma ko kallon ta bai yi ba don ba'a ba shi izinin haka ba,bayan haka shi bai san komai game da lamarin da ya faru ba.

Ganin irin kukan da Mama take yi tana kiran sunan Juwairiya ta ƙi shiga cikin gidan,a farfajiya ta tsaye tana kuka sosai ya kalle ta ya ce.

" Hajiya ba ni da nufin na cutar da ke gara ki koma ciki,don wallahi ko kukan mutuwa za ki yi ba zan buÉ—e miki ki fita ba.

Jin haka Mama ta ƙara sakin wani kukan ta zauna a gurin ta ƙi motsiwa,sai kuka da take yi domin kanta ya kulle.

*****

A ranar da aka É—auke su Mama Juwairiya ta yi wani irin bacci mai nauyin gaske,ba ta tashi ba sai da ta É—auki tsawon lokaci tana bacci mai kama da na mutuwa.

BuÉ—e idanunta ta yi cikin tsananin mutuwar jiki don ji take ko É—an yatsa ba za ta iya É—agawa ba.

Sai da aka É—auki tsawon lokaci sannan ta samu ta iya tashi zaune.

Ɗaga idanunta da ta yi ta kalli agogon da ke manne a bangon ɗakin,da gudu ta miƙe tana salati saboda tunawa da ta yi ko sallah ba ta yi ba.

" Na shiga uku mai ya faru yanzu fa ƙarfe ɗaya har da kwata,wane irin bacci na yi ko dai mutuwa na yi na dawo?"

Ta tambayi kanta domin wannan bacci da ta yi bai yi kama da na lafiya ba.

Da sauri ta miƙe ta shige ba yi tana tunanin to wane sallah ya kamata ta fara.

Bayan ta idar da sallah sai ta yi sauri ta ruga zuwa falo,saboda kiran curoma da cikinta yake yi.A haka dai ta ƙarasa tana mamakin jin gidan ya yi shiru,kamar ba mutane a gidan.

Ta shiga cikin tsananin tashin hankali da ta duba lungu da tsaƙo ba ta gan su ba ,sai ta fara kuka da salati tana dubawa cikin tsoro.Ta ɗauki tsawon lokaci amma ba ta ji ɗuriyar kowa ba.

Tana tsaye a farfajiyar gidan motar Baba Sani ya sawo kai.Da sauri ta ƙarasa gurin shi cikin muryar kuka don tunaninta ya fara ba ta yana da saka hannu na rashin ganin su,ko kuma shine ya ɗauke su.

" Baba Sani ina Mama na duba ko ina ban ganta ba."

Wata irin tsawa ya daka mata ya ce."Ku ji min munafuka ban sani ba,duk abin da ke faruwa ba da saka hannunki ba za ki raina min wayo."

Zare idanunta ta yi ta ce."Wallahi ba ni da masaniya akan komai mai ya faru?"

Kallonta ya yi sai ya matso kusa da ita ya fara magana cikin É—aga murya." Jiya A.m ya sameni ya ce kun yi da shi zai kai Mama wani gari har zuwa lokacin da za ku rabu,saboda na gaya masa ta kawo min Æ´an sanda."

Ya faɗa ranta a ɓace da baƙin ciki ƙarara a fuskar sa." Wallahi sam ba haka na so ba na so a ce yabar mini komai a hannuna,saboda na yi baƙin cikin irin daular da ya kaita."

Juwairiya ta kaÉ—u da jin abin da ya faÉ—a sai ta saka kuka sosai,ganin yanzu Mama ta san abin da ta aikata.

A ƙasa ta zauna tare da ƙara sakin kuka." Na shiga uku ba zan iya ƙara gaɗa ido da Mama ba,wane irin kallo za ta yi min wallahi na yi dana sani ƙwarai,yanzu idanuwana ba za su ƙara ganin ta ba har saina haifa mi shi yaro."Sai ta ji hawaye na sintiri akan fuskarta.

Sosai ta shiga tashin hankali ta na jin ba za ta ƙara iya haɗa ido da Mama ba,don ta san daga ranar da ta ji abin da ke faruwa za ta tsaneta na har abada.

Ganin irin kukan da take yi sosai kamar ranta zai fita a ranta ta na jin baƙin ciki matuƙa.

Baba Sani bai duba halin da take ciki ba ya ce." Ki kwantar da hankalin ki ni kaina na yi alƙwarin saina raba auren ku,in har na buƙaci kuɗi bai ba ni ba,wallahi saina tona asiri komai ya wargatse saboda na tsani ganin ki a cikin wannan daular,in kuma baya haihuwa ne sai ya sake ki don ba za ki zauna da shi ba."

Ba ta ce masa uffan ba har ya gama magana ya fice.

Juwairiya sai ta ji ba za ta iya zama a cikin gidan ba,domin duhun da ya yi mata yafi duhun ƙabari.

Ta yi kuka har ta ba uku lada tana ji wani irin kunyar Mama matuƙa tun kafin ta haɗa ido da ita.Take nadama ta shige ta har ta fara tunanin ba za ta taɓa yadda ta ƙara haɗa ido da Mama ba,matuƙar A.m bai aminta da ita ba a matsayin matar sa,wacce zai yi rayuwa da ita na har a bada.

Duk kiran da yake mata ƙin ɗagawa ta yi tana cikin haɗa kayanta,sai ta ji hucin mutum a bayanta,wanda ta gane A.m ne domin in dai ya zo guri turaren sa yake fara bayyana kan sa.

Kuka ta saka masa sosai tana dukan sa aƙirjin sa,ba tare da ya hana ta ba ya ƙyaleta don ya san dole ta yi,ita da take da hawayen banza ba'a taɓa ta ba ta yi kuka ina ga an rabata da Mama.

Ganin tana ta dukan sa amma ya ƙi ko motsi sai ta ƙara fashewa da kuka tare da faɗawa jikin sa.

" Mai ya sa zaka rabani da Mama anya ka yi min adalci kuwa,da wane ido kake son na kalle ta?Bayan ta san cewa na yi aure ba tare da sanin ta ba! Ni na san Mama ba za ta taɓa yafe mini ba,domin ita ba irin Baba Sani ba ne."

Ƙara rungumeta ya yi tsam a jikinsa ya na jin gangar jikinsa ya yi kewarta matuƙa.

" Ki gane ba ni da nufin na cutar da ita sai dai na yi hakanne don kar ta hanani samun farin cikina.Ina cikin damuwa sosai aurenki da na yi na yi ne don na samu cikon burina,amma kullum damuwa yake ƙara min ga Baba Sani da ya maida ni bankin sa, ga Mama sannan Zainab ta fara zargina dake jiya na shiga tashin hankali domin a kwai wanda yake bibiyarmu.Anya Juwairiya ke alkhairi ce a gareni?"

Ya faÉ—a yayin da idanuwansa suka canza launi saboda tsananin damuwar da yake ciki.

Da sauri ta janye jikinta gare shi tana jin wani iri zafi sosai jin abin da ya faÉ—a.

" Wayyo Allah na! Na roƙe ka ka cire min son sa a cikin zuciyata mutumin da nake so fiye da rayuwata,yake ganin ni ba alkhairi ba ce a rayuwarsa."

Ta faÉ—a a fili sai hawaye suka ci gaba da turereniya a fuskarta.
Tasowa ya yi zai riƙe ta ya buɗe baki ya ce." Sam b......"

" Don Allah ka fita daga gidan nan ba na son ganin ka! Ka fita kafin kasa zuciyata ta buga."Ta katse shi tana nuna masa hanyar fita.

Cikin zafi ya kalle ta." Ok na ji zan fita amma ki gaggauta dawowa gidana domin ki haifa min babyna mu rabu tun kafin Zainab ta fahimci komai,sannan Zainab ta sha alwashin cusgunawa rayuwarki domin ta gano gaskiyar lamarin dake tsakaninmu,don haka ki shirya duk wani cin kashi da za ki gani a gidan,sannan ba zan yi koma baya ga lamarin ba domin mu samu mu fita daga zarginta."

Sai Juwairiya ta fara kallon sa kamar wani mahaukaci yayin da take ji tabbas A.m ba ya sonta kamar yadda ya sha faÉ—a mata.

Wani irin baƙin ciki ya tokareta wanda y saka ta ji a ranta za ta iya bijire musu duka tare da tona asirin komai,don a yadda take jin zuciyarta ba za ta iya ɗaukar cin kashin da Zainab za ta yi mata ba.

Tabbas za ta tona komai ta fito ta nuna ma duniya ita ma matar shi ce,in yaso sai sama da ƙasa ta haɗe,haka kawai ya din ga ƙwallo da rayuwarta don kawai ya ga tana son sa.
Chapter 58 · 0% Book details