← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 86

Sashe 82

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Allah ka na gani A.m ya cuce ni na yi dana sani son ka da nake yi,ga shi na kasa iya cire shi a raina.In kana son ka samu baby mai zai saka sai ka kawota cikin gidana,har yanzu in na tuna akan gadona kake kwana da yarinyar nan,ina ji kamar na sha guba na mutu."

Shiru ya yi ya riƙe sitiyarin motarsa yana kallonta yayin da yake ta tsaƙe-tsaƙe a zuciyarsa.

" Duk ya riga ya wuce wannan meye amfanin dawo da hannu agogo baya,sannan na gaya miki dalilin aure k.."
" Don Allah kar ka taɓa ni baka san ƙyamar ka nake yi ba,mu tafi kawai ka tada motar duk abin da za ka ce mini in mun je gida ka gaya mini."Ta ce mi shi yayin da ta ga ya yi nufin kamata.

Kifa kan sa ya yi akan sitiyarin yana jin kukan da take na damun sa,amma ya san za ta yi fiye da wannan in ta ganta a gidan,da yadda ta sake abin ta don shi kan sa tsoron rigimarta yake yi,shi ya sa ya so ya yi mata bayani amma ta ƙi sauraran sa,kawai sai ya tada motar komai ta fanjama fanjamjam.

TO MASU KARATU KU DAI BIYO NI KU JI YADDA ZA TA KAYA A TSAKANIN SU YAU BAN YI TYPIND DA YAWA BA,SABODA BA NA JIN DAƊI KU YI HAƘURI DA WANNAN ANA TARE.

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY

TALLAH!TALLAH!!TALLAH!!!

INA ƳAN MATA DA MATAN AUREN DA SUKA SHAYAR SUKE SON MARTAR ƘIRJIN SU YA DAWO?

INA MATAN DA SUKE FAMA DA RASHIN ƘIBA KO INA A ƘAME?

MAZA GARZAYO KI SIYA INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO DA ƘIBA,MAGANIN AN RIGA AN GWADA KUMA YA NA DA AKYAU ƘWARAI.BARI IN GAYA MIKI YAR'UWA DUK WADDA TA CE MIKI MARTABAR ƘIRJINKI,ZAI DAWO MATUƘAR JIKINKI BAI MURJE BA,TO GASKIYA KUƊIN KI KAWAI ZA TA CI.

IN HAR KINA SON MAGANIN YA YI AIKI A JIKIN KI SAI KIN DAURE,KIN SHA SAFE DA YAMMA.SANNAN MUNA AIKAWA KO INA SIYAN NAGARI MAIDA KUÆŠI GIDA.

MAGANIN AKAN FARASHI MAI TSAUƘI IN KINA SO MAZA GARZAYO KI KIRA WANAN NUMBAR ( 07088268243) KO (08144072423)

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 36*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Shiru ya biyo tsakanin su babu mai magana kowa yana tsaƙe-tsaƙe a zuciyarsa,sai kukan Zainab da sheshsheƙa da yake tashi a hankali.

Ko da suka isa gidan da gudu ta fice daga cikin motar ba tare da ta kalle shi ba,ta haye sama kai tsaye bayi ta wuce,tare da sakar ma kanta shower tana wankan dole,don kawai kar ya kula ta.

A.m da ya gaji da zama tashi ya yi ya leƙa bayin don ya tabbata ta kammala wankan,ƙin fitowa ta yi,yana leƙawa ya gan ta a tsuguna tana kuka sosai.

Jikinsa ya yi sanyi sosai shi kan sa bai yi tunanin tana kishin sa haka,don gani ya yi abin ya wuce misali,saboda duk ta bi ta rame kamar ba Zainab ƴar ƙwalisa ba.

" Zainab don Allah ki fito daga bayin nan ki zo mu fahimci juna,karki saka wata cuta ta kama ki."Ya ce da ita cikin tsananin tausayin ta.

" Ka fita don Allah na dawo gidanka ne don ba zan iya rayuwa babu kai ba,amma hakan baya nufin na sake amincewa da kai."Iya abin da ta ce mi shi kenan ta ƙara sakin kuka,mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Da ya gaji da tsayuwar jira sai ya fita falo don ya duba lafiyarta,amma sai bai gan ta a falon ba,cikin sanɗa ya leƙa ɗakinta sai ya gan ta kwance tana bacci da sauri ya ja ƙofar ya fita,tare da sakin ajiyar zuciya mai nauyin gaske.

A.m dake tuƙi ya fita don ya siyo musu abin da za su ci,duk da cewar mai aikin da Momi ta kawo musu ta yi abinci,amma ya rasa ta in da zai fara lallashinta,shi kan sa bai yi tunanin haka take ba,saboda ya gaya mata dalilinsa amma sam ta ƙi ta manta komai.

Ko da ya dawo siyo musu abinci É—akin Juwairiya ya fara zuwa,amma har wannan lokacin tana bacci.

Jikinta ya taɓa sai ya ji ɗumi hankalinsa ya tashi jin zazzaɓi a tare da ita.Wayarsa ya ciro tare da kiran likita don ya duba ta,ya ije mata kayan ciye-ciyen ta ya fice daga ɗakin ba tare da ya tashe ta ba,saboda gudun rigimarta da yake tsoro.

ÆŠakin Zainab ya nufa amma sai ya ji ta kulle har da makulli.

Bai yi ko tari ba ya juya zuwa É—akin sa ya É—auko spare makulli ya buÉ—e.

Har yanzu tana zaune bayan ta yi sallar magariba hawaye yana bin ƙuncinta.

" Ya kamata don Allah ki manta komai Zainab kukan ki yana cutar da zuciyata,na yi miki bayani amma kin ƙi saurarata."Ya faɗa bayan ya tallabo ta jikinsa.

" Na fahimce ka kawai na kasa yadda da abin da ke faruwa a tsaƙaninmu n..."Ya katse ta da cewar.

" Wallahi ba ni da nufin na cutar da ke. Ita ma katsesa ta yi ta ce." Ya wuce sam bana son ka ko ambaci sunanta don Allah ka kyaleni kawai."

Ganin haka sai ya ja ta jikinsa yana shafa bayanta,kamar wata ƴar baby yayin da ita kuma ta lafe jikinsa,tana jin ƙaunarsa fiye da ta da.

Ya mantar da ita komai da kalar soyayyar da yake nuna mata, wanda take ji ba za ta iya rabuwa da shi ba,sannan za ta iya zama ajalin duk wata mace da ta yi gigin raɓarsa.

Da a kira salar isha i sai suka yi wanka sannan suka kwanta,a ran A.m na ta addu'a Allah ya sa kar wancan rigimammiyar ta tashe su,saboda sam Zainab ta ƙi yadda ya yi mata bayani.

Juwairiya bayan ta yi salla ta zauna tana cin kwaÉ—on zogala, wanda ta saka mai aiki ta yi mata tun yamma,saboda jikinta da babu daÉ—i ta kasa ci.Wanka ta shiga duk da ba ta son ta yi amma jin jikinta yake yi mata wani iri.

Likita da ya shigo ya kira wayarta da A.m ya tura mi shi da cewar in ya zo ya kira ta.

Duk yadda likitan ya so ya yi mata allura ta ƙi, don ita ba ta ga wani ciwon da zai saka A.m ya kira likita ba,ta lura mugu ne so yake kafin ta haihu duk ya tsire mata jiki da allura.

Cikin dare misalin biyu da kwanta kasa bacci duk da ba ta yi ninyar zuwa ɗakin su ba,kamar yadda Hamdiya ta yi ta zuga ta don har text ta yi mata,amma ita tsakani da Allah yunwa take ji matuƙar gaske,wanda take jin za ta iya shiga cikin wani hali kafin gobe.

" Inna lillahi A.m ɓarayi ne suka shigo cikin gidan nan!"Zainab ta faɗa da tashin hankali a fuskarta jin ana ƙwanƙwasa musu ƙofa.

A.m da bai samu ya rintsa ba har sai da lokacin da take tashin sa ya gota,sannan wani nauyaryar bacci ya É—auke shi.

Ƙara juyawa ya yi tare da rungumo ta amma sai ta ture shi cikin tashin hankali tare da girgiza shi da ƙarfi.

" Na shiga uku! Allah ya sa ba ƴan garkuwa da mutane ba ne suka zo."Ta faɗa a tsorace wanda ya saka A.m miƙewa da sauri cikin tashin hankali.

Ji ya yi kamar ya ɓoye saboda bai san ta in da zai fara ba.

Ƙofar ya nufa da tsoro a fuskarsa har zai murɗa ta riƙe shi ta ce. " Don Allah karka buɗe su cutar da kai."

" Mene ne".

Ya ce cikin wata irin murya da ya saka ta kalle shi da shakku a fuskarata.

" Tambaya kake mene ne A.m?Ka san waye a tsaye a ƙofar ɗakin ne?"Da tashin hankali ta faɗi tana masa wani irin kallo.

A.m da ya yi tsuru-tsuru kamar ɓarawo a hannun mata sai kawai ya buɗe ƙofar ta bayyana, da take tsaye da kayan bacci duguwar riga a jikinta da hijabi da ta ɗora ga ɗan titsin cikin da ya fara fitowa a jikin hijabi.

Zainab ta girgiza idanunta ta ƙara ta kuma kallonta da ta yi tsaye fuskarta cike da tsiwa,tana musu kallon kamar ta ga kashi har da wani ɗan girgiza take.

Ta ƙara girgiza idanunta ta kuma goge fuskarta a ranta tana tunanin anya Juwairiya ce ta canza kala ta dawo haka.

" Ka san lokacin cin abincina ya yi shi ne baka girka mini batun É—azu cikina ke ciwo."

Ta ce da shi ba tare da ko fargaba tana kallon su duka da tsuka tsaya ƙiƙam kamar wasu gumaka.

A.m ya yi wani iri da shi ya kalli Juwairiya sannan ya kalli Zainab da ta yi suman tsaye,har yanzu ta kasa yarda ita ce a gabanta.

Sai haushin kan sa ya kama shi gani yake kamar bai cancanci ya zamo mijin mata biyu ba,duba ga dukannin su tsoron su yake yi.

" Innalillahi!Momi na shiga uku da gaske wannan yar iskar yarinyar da ka ce tana gidanku ashe tana gidan nan?"

Ta faɗa tare da cakume shi tana kuka kawai sai ta ɗaga hannunta za ta mare shi da sauri ya riƙe ya ce." Zainab ki kula har yanzu da saurana don ban zama irin mazannan da mace za ta rinƙa duka ba.Na so na yi miki bayani amma ke kullum ba kya yi mini uzuri ki saurare ni.Abba ya tilasta mini na kawo ta gidana amma da zarar ta haihu zan sallame ta."
Chapter 82 · 0% Book details