Sashe 55
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya ta yi jin abin da ya ce."Ni ba satar fita na yi ba layina aka rufe zan je na buÉ—e ne."Ta bashi amsa ta na kallon shi.
"Lafiya ba ki dawo ba gidan babu daɗi kwana biyu na yi missing ɗinki ga tubbina da ya yi rashin daddaɗar abincin.Gaskiya gangar jikina da tubbina sun yi rashin har na kasa haƙura ."
Zuba mishi ido ta yi jin abin da ya faÉ—a kamar da gaske.
"Ai ko ya kamata ka fara sabawa ko ka manta saura kwanaki mu rabu.Kuma meye abin damuwa bayan ka na da matar so a gida ban ga dalilin da zai saka ka damu da matar wucin gadi ba."
Ta faɗa cike da tsantsar kishin Zainab da ya bayyana ƙarara a fuskarta.
Kallonta ya yi tare da matsowa daf da ita ta yadda har suna jin numfashin juna ya kama hannunta ya ce.
"Kishi ko?"
Ya saki hannunta ya juya mata baya sannan ya ci gaba da magana.
"Bai kamata ki saka kishin matata a zuciyarki ba kin san cewa ita ce matar so.Kin sa dalilin aurenmu am sorry to say da Zainab ta na haihuwa babu abin da zai saka na aure ki.Kawai ni na san in muka rabu zan yi kewarki da kishin mijinki don ki na da baiwar da ba kowa ce mace take dashi ba."
Ta na son ta yi magana kuka ya ƙwace mata amma hakan na ta daure ta ce."Mai yasa ka shigo da ni cikin rayuwarka ka san ba gurbina a cikin zuciyarka?"
"Saboda ki haifi yaro na bawa Zainab saboda ina son na ga ƙwaina ya sa na aure ki."Ya faɗa muryar sa a ɗage.
"To mai ya sa kake gaya min maganganun da suke yaudarar zuciyata?Ka tsaya iya kan abin da kake buƙata a gareni."
Cikin kuka take mishi maganar sai ta juya za ta ruga da gudu da sauri ya janyo ta zai rungume ko mai ya tuna ya sake ta ta ruga da gudu ta na kuka.
Cikin motar shi ya faÉ—a ya na wani irin huci kamar mesa ya daÉ—e a gurin sannan ya figi motar a guje kamar zai tashi sama.
Lantana mai aikin Zainab da take laɓe a bayan kango ta na kallon A.m da ya yi shirin rungume Juwairiya ta fito cikin tsananin mamaki ta na kallon in da motar shi tabi.
Zaro idanunta ta yi cikin tashin hankali ta na mamakin da ma cin amanar ta suke shi da ita?Allah Sarki baiwar Allah ta na can ta damu da ita gashi wayarta ba ta shiga,ashe ita ta na can suna cin amanarta.Haba!Biri ya yi kama da mutum ai ko yau dole Zainab ta ji abin da suke yi ita ta na can sai tsabar son kuɗi ta ɗauko mace zuƙeƙiya ta ije ma mijinta.
TO FA WAYYO ALLAH BA RI NA YI NAN DON GASKIYA BAN SHIRYA GANIN WANNAN TASHIN HANKALI BA.
KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.
BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 25*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Hajiya Zainab tana zaune a ƙaton katafaren falonta ita da ƙawarta mai suna Nabila wacce suka taso tun yarinta,amma ita tana aure a Abuja ta zo ganin gidane da kuma ta ya Zainab murnar asibitin da ta buɗe.
Lantana ce ta shigo saboda tsabar gulma jikinta har kyarma yake yi.
Duk da ganin tana tare da baƙuwa amma sai ta kasa haƙuri har baƙuwar ta tafi, matsawa kusa da ita ta yi ta fara magana don tsabar gulma da yake cinta.
"Hajiya don Allah in ba za ki damu ba ina son na yi magana da ke kuma mai mahimmanci."
Zainab ta kalle ta sheƙeƙe tare da jan tsaki ta na tauna jingam a bakinta.
"Ni fa Lantana na fara gajiya da halinki yadda kika san ke kika kawo babu duniya,na san yau ma bai wuce ki ce na baki kuɗin aiki kafin wata ya ƙare ba,kuma na rantse ko me za ki ce ba zan bayar ba."
Ta faÉ—a hankalinta na kan waya ta na hira da matar da ta addabeta take ta tura mata da sallama kullum,ba ta daina ba har sai da ta yi nasara ta fara magana da ita suna gaisawa.
Lantana ta kalleta a ranta ta ce."Banza mara mutunci kawai ai wallahi don kawai iskanci suke yi da ita da na so ma ya aureta na ga ƙaryar iya shege."
Amma a fili sai ta ce." Ba wannan ya kawo ni ba idanuwana sun yi mummunan gani kuma in kika ji,wallahi hankalinki zai tashi matuƙa ba na son abin da zai cutar da ke ne kasancewar ki na taimaka min.
" Ke dakata karki dame ni da shegen surutunki."
Ta ce bayan ta ije wayarta sannan ta kalleta ta ci gaba da cewa." Za ki iya magana ba ni da matsala ƙawata ce tun na yarinta."
Lantana ba haka ta so ba amma tun da ta faɗi haka gashi gulma na iban ta sai ta kwashe abin da ta gani,harma da ƙara magi da gishiri don ya yi zaƙi cakwai ta fara gaya mata.
Ba ta kai ga ƙarshen labarin ba in da take tunanin zai fi ɗaga hankalinta.
Zainab ta miƙe kamar wata mahaukaciya ta kai mata raruma.
Wani irin shaƙa ta kai mata cikin ihu ta zare idanunta kamar mahaukaciya.
" Ke baki da hankali mijina kike maganar kin gan shi da wata in ma da wata kika gan shi,bai kamata ki haɗa shi da wata ƙazamiya kucaka yar matsiyata ba."
Sai kawai ta rufeta da duka da mari take kai mata.
Lantana ta hau ihu da ƙarfi ganin dukan da take mata ta ƙara sakin ƙara ganin ta wawuro wani gilas za ta maka mata.
" Don Allah ki taimake ni wallahi abin da na faɗa miki gaskiya ne,ba zan shirya irin wannan ƙaryar na gaya miki kawai don na ɓata miki."
Ta faɗa yayin da ta ruga ta ɓoye a bayan Nabila da ta miƙe cikin tashin hankali ganin za ta yi kisa.
" Zainab be patient kar fa kishi ya sa ki aikata dana sani,ya kamata ki yi ma maganarta kyakykyawar fahimta,ita ba ƙaramar yarinya ba ce da za ta yi miki gulma don son ranta."
" Ke Nabila dakata wallahi yanzu za ki fita da fashashshen kai mundin kika yadda da abin da take faɗi,mijina mai aji da kyau za ta haɗa shi da mai aikina.Na yadda da A.m ba zai taɓa kula wata ƴa mace ba,don ban taɓa ganin ya kula mata masu aji ba bare ita ƙazama mara gata da aji."
Ta ce da ita tare da ƙara rarumar abu ta yo kanta da shi.
Nabila ba ta damu da abin da ta ce ba ta tunkare ta tana ƙoƙarin ƙwace makamin da ta ɗauka.
Da ƙyar ta samu ta zauna tare da dafe kanta ta ce."Na yi baƙin cikin da ki na nan ta kawo min wannan baƙin labari,da bakya nan sai na nuna mata haukana."
Sai kuma ta kai mata shaƙa da ƙarfi saboda gani take kamar ta raina ta ne ta kawo mata wannnan labari.
Lantana idanunta suka kaɗa suka yi jajur ta na ƙaƙari saboda ta shaƙe ta sosai,sai zaro idanu take ta na dana sanin gaya mata gashi za ta baƙunci lahira ba ta shirya ba.
Lantana ta sadaƙar mutuwa za ta yi ta tabbata da ita kaɗai ne da Zainab a gidan, sai ta kasheta dama haka take da kishi akan mijinta take barin shi ya na garari.
Da ƙyar Nabila ta ƙwaci Lantana da take fitar da numfashi sama-sama.
Ta samu ta tura ta cikin É—aki tare da rufe ta a É—akin ta dawo gurin Lantana da take murza wuyanta.
" Kin tabbata abin da kika gani gaskiya ne?"
" Wallahi da gaske ne Hajiya da idona na gansu."Ta faÉ—a cikin kalar tausayi.
" Ok ga wannan ki riƙe na gode da kika gaya mana ki ci gaba da saka ido a kansu."
Lantana da ta ga an miƙa mata farare gal da su sai ta washe baki,ta karɓe ta soke sannan ta kalle ta ta ce.
" Hajiya na gode dama tuntuni nake lura da ita yadda take mishi kallo kamar mayya,zan ci gaba da bibiyar su amma fa sai dai ki bani numbar ki ba zan gaya ma Hajiya Zainab ba kashe ni za ta yi."
Bayan ta gama da Lantana ta buɗe ɗakin ta shiga ta na zaune akan gado,ko kaɗan ba ta nuna damuwarta akan maganar ba,saboda ta saka a ranta A.m ba zai taɓa dubi ga wata ƴa mace ba.
Nabila ta zauna a gefen ta suna fuskan tar juna.
Zainab na yi matuƙar mamakin irin yadda kika yadda da mijnki duk da ba ina zargin sa ba ne, amma Lantana ba za ta taɓa gaya miki ƙarya ba musamman in kika dube ta za ki ga alamun gaskiya a fuskarta,na tabbata a kwai ƙamshin gaskiya a maganarta ko da kuwa ba haka maganar take ba.
Duk da cewa A.m mutumin kirki ne wanda bai damu da irin wannan rayuwar ba,ni kai na ba na tunanin zan iya tarayya da mai aiki duba ga yadda ya tsani duk wani talaka,amma ki tsaya ki yi karatun ta natsu ki saka ido domin namiji ba shi da tabbas!"
Zainab ta kalli Nabila a wukaƙance tare da miƙewa ranta a ɓace ta ce.