← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 86

Sashe 46

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk lokacin da ya faɗi haka Juwairiya ringume shi take ta saka kuka iya ƙarfin ta shi kuma ya ɓuge ya yi ta aikin rararrashi.

A haka dai suke zaman su cikin kulawa da juna da girmama juna don in Juwairiya na mishi magana,gabaki ɗaya hankalin sa yake ba ta ko tari ba ya yi sai ta gama ya na matuƙar girmama lamarin ta,don ita ma ta na ba shi kulawa har ya na kawai ya ƙyale Zainab ta tafi duk in da yake so tun da ya na da wanda take kusam makwafin ta kawai Juwairiya ce baya jin ta a zuciyar ta amma komai na ta ya yi masa.

Ranar wata alhamis Juwairiya ta dage ta shirya ma A.m abincin da yafi so wanda duk sai da ta zauna ta tambaye shi,ta kuma saka su a cikin ranta don kullum sai ta tambaye shi abin da yafi ƙauna a cikin rayuwar sa,kuma duk ya gaya mata.

Ƙarar shigowar mota ta ji da sauri ta miƙe daga sallayar da take zaune bayan ta idar da salla,ta na karatun alkur'ani ta rage zaman jiran dhi don ta ƙagu ya dawo musamman da ya kirata ya ce mata a kwai labari mai daɗi.

A ranta tunani take ko zai zo ya faɗa mata ya na sonta shi ya sa ta ɗauko kur'ani ta na karantawa,saboda ta zaƙu matuƙa da ya shigo.

Ɗaga labulen ke da wuya ta leƙa kawai sai ta ga Zainab ta fito janye da akwati,wani irin tashin hankali ya ziyarce ta ta saki wata ƴar ƙara na rashin jin daɗin dawowar ta ta zauna jaɓar!

Sai kuma ta yi zubbur ta miƙe da ta kalli kanta a madubi sai da gabanta ya buga ta yi kyau matuƙa ga ƙarin haske da ta yi,da jikinta bai da haske amma yanzu wani irin ja ta yi sosai jikinta kamar ka losa jini ya fito.

Falo ta fito amma lokacin har Zainab ta shige ciki sai ta koma É—aki ta yi kiran A.m tare da yi mishi albishir da Zainab ta dawo.

Zubbur ya miƙe ya tattara komai ya taho gida don ya ganta saboda ya yi mising ɗinta sosai.

Ya na shigowa ɗakin ya same ta a zaune ta na ɗaki waya take yi ganin sa sai ta kashe wayar ta miƙe ta na zare ido,tare da dafe ƙuncinta a tunanin ta mari zai kai mata kamar na farko.

Amma sai ya ba ta mamaki sosai ya ganin ya harare ta ya saki tsaki ya nemi guri kusa da ita ya zauna.
Abin sai ya ba ta mamaki ta kalle shi ta ce." Habibi i miss you zuc.."

Wata uwar harar ya daka mata tare da taɓe bakin sa.
"Rufe min baki shashasha kawai ni za ki yaudara duk abin da kika ga dama ki je ki yi ta yi na zuba miki ido duniya ce,tunna Æ´an'uwan ki dabbobi ne ba su san a kwai Allah ba bare annabi ya faku."

Ya miƙe ya sauko ƙasa don ya ci abinci ita ma sai ta biyo shi dama wanka ta yi ta na son ta sauko ƙasa ta ci abinci,sai aka kira ta ganin kiran na kuɗi ne don wata Hajiya ce take son ta yi mata oder kayan ɗaki za ta aurar da yara biyu.

Biyo shi ta yi da sauri suka sauko ƙasa duk yadda take ta mishi hira bai tanka ba don ya so ace Juwairiya na gefen sa yake cin abincin ya yi ta mata sanni ,ita kuma ta yi ta murmushi dimple ɗinta ya na lotsawa shi kuma ya yi ta saka hannu a gurin don ya na burge shi,sai ya ciro wayar sa ya tura mata da tsaƙon godiyar abincin har da steaker na kis akai ma abinci.

Rungume wayar ta ta yi tare da sakin ma hoton sa da ta ɗauke shi ba tare da ya sani aba suna zaune a falo,saboda bai taɓa ce wa zai ɗauke ta hoto ba duk da in ta yi kwalliya ya yi ta yabawa shi ya sa ita ma ta ɗauke shi ba tare da ya sani ba.

Kuma ya yi kyau sosai kamar wani balarabe ta saka pasword a gurin hoton kafin ta buÉ—e sai ta rubuta sunan ta da full sunan shi.

Da sauri ta saka ƙaton hijabin ta har ƙasa saboda tsoron fita kiran da Zainab ta yi mata,sai da gabanta ya buga don gani take hijabin ƙara mata kyau kawai ya yi,amma dai ya rufe surar jikinta da A.m kullum sai ya yi ta yabon shi ya na zuzuta wa.

A hankali ta taku har zuwa in da suke duk da dukan da gabanta yake yi.

Zainab haka kawai ta tsinci gabanta ya faɗi ganin yadda Juwairiya ta canza har sai da ta miƙe, gabaki ɗaya ta zama kamar wata matar gidan yadda fuskar ta ya canza ta ƙara haske sai abin ya ba ta mamaki ƙwarai ta kalle ta tare da sakin ƙara ta ce.

TO MASU KARATU ABIN DA ZAINAB ZA TA CE YA TSORA TA NI NA MIƘE DA SAURI HAR BIRO NA YA FAƊI GASHI NA NEME SHI BAN GAN SHI BA KUCI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 22*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"Ke uban me kike yi haka ki ka canza ko kayan shafana kike amfani da shi in ba na nan? Duk da na kulle É—akina."

Zainab ta ce ta na kallonta cikin tsananin mamakin yadda ta ga Juwairiya ta koma lokaci guda.

Juwairiya hankalinta ya tashi ita kanta ta yi tunanin hakan dama dole ta yi maganar canzawarta,ko A.m da suke tare kullum sai ya yi maganar ta ƙara kyau bare Zainab da ta ɗan jima ba ta ganta ba,sai ta yi shiru ta na zare ido.

"Dear ba ka ga yadda yarinyar nan ta zanca ba kalli jikinta ka gani da key na na tafi,amma ina tunanin shafe-shafe take yi da siyan supplement irin yadda ƴan matan yanzu suƙa ɓace da siya don su yi kyau.

To in ma shi kike yi wallahi ina tausayin ki matuƙa don babu in da zai kai ki sai motar nadama,domin duk tashen kyau da kika yi daga ƙarshe cutar canser ita ce ajalin ki,kin ga kin kashe kan ki a banza saboda kwaɗayin duniya da son burge namiji,gara ki tsaya a haliitar da Allah ya yi miki,saboda namijin da kike yi don shi gudun zai yi,kin ga wa gari ya waya? "

A.m da ko kallon Juwairiya bai yi ba haka zalika bai kalli Zainab ba da take zuba nasiha,a ran sa ya na tunanin dama ta na da hankalin yi ma wani nasiha ta kasa yi wa kanta.Ya na cin abincin sa hankalin sa kwance,irin ba ruwana can ku ƙarata ba ta shafe ni ba.

A yatsine ya juya ya kalli Zainab sannan ya yi ma Juwairiya kallo ɗaya ya ɗauke kansa don ji ya yi ta burge shi sosai ya ije cokalin abincin sa ya na hararar da ta zame masa ƙa'ida tare da kallon Zainab."

"Ta ina zan gane hakan tun da ba kallon ta nake yi ba ke ma tsokana na kike bayan kin san idanuwana ba sa iya kallon wata mace sai ke,kuma in ta na shafe-shafe ina ruwan ki ba aure za ta yi ba.Kuma ni ba na tunanin haka wataƙila canjin abincin da ta samu ne ta canza kin san ko wace mace da kalar jikinta.Kuma ga shi ta iya girki sosai wallahi ina yabawa abincin ta a kwai saka natsuwa a zuci."

Zainab ta harare shi ta tsaki tsaƙi jin abin da ya ce." Oho Allah ya sa a duniya za ka ce ita ta ci gasar iya girki bai dame ni ba, ba wahala na zo yi a duniya ba bare na bautawa wani can,kuma da kake magana in dama ba ta iya abinci ba korar na zan yi tun da dalilin da ya saka aka ɗauko ta kenan."

Kamar ba zai ce komai ba ganin yadda ta ƙule amma ya na son ya ƙuntata mata, saboda ya fahimci in ya ce dukan ta zai din ga yi haka za su ci gaba saboda ba za ta taɓa canza halinta ba,shi kuma sam ba ya son ya mai da gidan sa gidan dabbe musamman da yanzu Juwairiya ta ɗauke shi kamar wani waliyi."

Spoon ya ɗauka ya taɓe bakin sa tare da ɓare ledar tuwon shinkafa da ta tuƙu sosai ya zuba miya,ya kalli Zainab da take huci kamar wata kububuwa don ya ya bi Juwairiya ya ce."Ai ita komai ta iya ta na da ƙoƙari matuƙa dubi gidan nan komai tsaf-tsaf sai tashin ƙamshi da yake saukar da nishaɗi a zuciya ga..."

A.m ya yi shuru da maganar da yake yi jin an yi jifa da kayan abincin da yake ji a ƙasa.
" Na ji ta iya koma mene ne ba ruwana kuma in ban da munafunci ce wa ka yi ba a gida kake kwana ba in na yi tafiya shi ne kake maganar iya abincin ta."

Miƙewa ya yi a gadare ya ba ta amsa da ce wa."An gaya miki kuɗin banza nake samu da zan din ga yawo hotel ina kwana?Da ma sau ɗaya da kika yi tafiya na kwana a can tun da na ga ba canza wa za ki yi ba, na na haƙura ina kwana a gida ai da babu gara ba daɗi ko banza a kwai wace za ta ba ni abinci."
Chapter 46 · 0% Book details