← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 86

Sashe 50

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta faÉ—a tare da juya mata baya sai dai ta ji a jikinta kamar babu kowa a É—akin ko da ta juyo wayam ba Binta ta fice daga É—akin.

Duk yadda ta so ta yi magana amma Binta taƙi tanka mata sai in ta ga za ta takura mata ta saka mata kuka,hankalinta ya tashi matuƙa ta yi zuru ta na kallonta.

Binta ta saka a ranta ba za ta ƙara mata magana ba balle ta tanka a kan cin amanar da suke yi ita da shi,Allah Allah ta ke gobe ya yi Zainab ta dawo ta saka mata kukan ta kaita gida.

A.m bai shigo gidan ba sai misalin bakwai bayan ya dawo daga masallaci kamar yadda bai neme ta ba,haka ita ma domin ko kiranta ba ta son ya yi saboda hankalinta ya tashi jin ya faɗi za a yi mata dashen ƙwan haihuwa.

Sai ta fara nadama matuƙa ta na ji kamar ta gudu daga gidan don ta san mundin ta faɗa mishi to ita ma yanka ta zai yi ko ya kasheta,saboda ya gaya mata duk abin da ke tsakanin su ba da wata manufa yake yi ba burin sa ya samu baby shi ya sa yake mata haka don haka ta saka a ranta abin da ya fi na Binta zai yi mata.

Kwanciya ta yi ba wani karsashi a tare da ita saboda duk yadda ta so ta zo su kwanta amma taƙi sai ta samu guri a ɗakin da Baba take zama ta kwanta.

A.m da ya gama shirin baccin sa shiru ba ta zo ba dama bai saka ran za ta zo ba kuma shima ransa babu daɗi don sun yi ɗan tanka-tanka da A.k akan nemar shawarar sa da ya yi na dashen da yake so ayi mata,amama sai ya nuna rashin amincewar sa akan ya ƙara haƙuri har Allah ya kawo.

A.m ya ji ba daÉ—i don ya gaji da jiran gawon shanu don haka ya nuna ma A.k rashin amincewar shi in da har ya ji zafi ya gaya masa magana,yayin da ya saka a ranshi kawai za su tafi ai shi ba uban shi ba ne da duk a bin da zai yi sai ya nemi shawarar sa.

ÆŠakin da take kwance ya nufa tare da saka cocilar wayarsa ya haska fuskarta,ba bacci take ba amma ta yi maza ta rufe idanunta jin shigowarsa.

Ta yi mamakin da bai tashe ta ba ya juya ya fita.

Hankalin shi ya É—an tashi ya shiga tunannin ko ta gudu ne don bai ganta ba,sai kuma ya duba É—akin da ya san Baba ta na zama ilai kuwa ta na É—akin ta takure a guri taya ta na baccin wahala, don ko numfashi ba ta saukar wa ta daÉ—i ganin yadda ta takure kanta.

Sai dai ya yi mamaki ƙwarai ko da ya matsa kusa da ita sai ya ga ta miƙe zubbur ta na salati,wanda ya saka a ranshi mafarkin shi take yi.

"Inna lillahi na bani don Allah karka cutar da ni mahaifiyata ba ta da rai."

Ta faɗa da muryar kuka ta na roƙonsa amma bai kula ta ba sai ya saka hannu a aljihun wandon sa ya zaro bindiga ya ɗora mata a goshinta.

Ta buÉ—e baki za ta yi ihu amma sai ya saita daidai bakinta ya ce da murya mai sanyi."In kika yi ihu sai na kashe ki.".
Ya faɗa da wata irin murya da ta ƙara tsorata ta wanda ya sa ta yi sauri ta rufe baki ta tare da mai da kukan.

Ganin ta yi shuru ta na kallon sa har fitsari ta yi a wando.

A.m ya kalleta tare da watsa mata harara ya fara magana da ce wa."Gobe Zainab za ta dawo Allah ya sa ki faÉ—i wani abu a tsakanina da Juwairiya kashe ki zan yi."

Wani irin kartawa cikinta ya yi ta ƙara toshe bakinta ta na tunanin yau Allah ya kawo ta gurin jidali gashi mai gida na son ya kasheta.
"Wallahi ba zan ce komai ba babu ruwana ka taimake ni karka kashe ni."

Ganin ta tsorata ya sauke bindigar ya na shafawa ya ce."Good in kunni ya ji gangar jiki ya tsira ina fatan kin gane."
Da da sauri ta É—aga masa kai sannan ya fara taku zai fita wanda Binta ta fara addu'a Allah ya raba ta da shi lafiya.

Ganin ya kuma jiyo sai hankalinta ya ƙunduma ya tashi ta ƙara firgicewa ta na tunanin mai ya saka ya dawo."
"In Zainab ta dawo ina son ki yi ƙaryar aljanu a mai dake in da ka ɗauko ki in kuma ba haka ba wannan zan saka na kashe ki."

Ya faÉ—a ya na nuna ta da bakin bindiga sannan ya juya ya fice daga É—akin.
A ranar kasa bacci ta yi ta na ta kuka daga ƙarshe dole ta koma ɗakin da suke kwana don gani take kamar zai dawo ya kasheta.

Washegari gidan ya kacame sai gyara ake yi kasancewa da misalin sha É—aya Zainab za ta iso shi kan shi gogan bai je ko ina ba ya na zaune a falo ta iso.

Tun da suka shiga ɗaki ba'a ƙara jin ɗuriyar suba sai da aka kira sallar azahar sannan A.m ya yi wanka ya fito yayin da Zainab take biye a bayan sa don ta fito ta ba ma cikinta haƙƙin sa.

Binta da take jiran fito ba ta jima da jin fitowarta ba lokacin ta na waya ta fito da gudu ta ruga zuwa waje sai ta dawo ta kalli Zainab ta ƙara rugawa waje,tun Zainab ba ta damu ba sai ta ɗan firgita tare da daka mata tsawa amma ba ta dai na ba ƙarshe fashewa da kuka ta yi ta kama suratai.

Zainab da ta matsa ne sa da ita ta na faÉ—in."Na shiga uku ke Juwairiya fito ki ga abin da take yi dama Anty Fati ta san ba ta da hankali ta kawo min ita?"

Ko da ta fito ta ga halin da take ciki sai hankalinta ya tashi matuƙa yayin da tsoro ya shigeta gani take kamar ta yi hakan ne don ta tona asirin su.

"Gida za ni amai da ni gida a kwai dokin da nake hawa ni Sarkin ljanu a can in kuma yau ba hau ba duk saina yi maganin ku."

Ta faÉ—a da tsamin murya ta na girgiza jikinta kamar ta na da aljanun da gaske.
" Na shiga uku kin ji mai take ce wa?"
Ta ce da Juwairiya da ta tsaya ta na mamakinta yayin da tausayinta ya cika ranta don ta san ta yi hakan ne don ta koma gida ita ba ta san A.m ya tsoratar da ita bayan wannan.

Kama ta yi ganin ta na jijjiga sai hawaye ya wanke mata fuska.

Zainab da ba ta taɓa ganin wai mai aljanu ba sai ta tsorata ainun take ta kira Anty Fati jikinta na ɓari ta sanar mata halin da Binta take ciki nan take ta ce bari ta turo direba da mai aikinta su taho da ita don sam iyayen ta ba su yi mata bayani ba.

Zainab ta tsorata sosai a ranta Allah Allah take direban Anty fati ya iso,abincin da take ci kasa ci ta yi ta tsaya ta na kallon ikon Allah yayin da jikinta ke ɓari.

Suna cikin wannan halin ya shigo da sauri ta ƙarasa gun shi ta yi masa bayani.

Ya kalli Binta da take kaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa ta na zare ido,sai hakan ya so ya bashi dariya amma ya cije.

Wata uwar tsawa ya daka mata ganin ta gan shi sai ta razana kamar za ta gudu don Allah ya saka mata matuƙar tsoron shi.
ÆŠan natsuwa ta yi amma ba ta daina zare ido ba ita a dole ga mai aljanu.

A.m ya kalleta sai ya kauda kansa tare da taɓe baki ya ce da Zainab da ta yi tsuru-tsuru ta na kallon Binta.

" Maganin ki kenan da shegen kwashe-kwashen ki ta yi maza ya bar gidan nan ai ga yi nan kin je kin jawo ma kan ki mai almatsutsai."

Ya yi maza ya haye sama ya na dariyar yadda Binta take yi sai ka ce wata ƙadangaruwa,saboda in ya tsaya dariya zai kubce masa.

Direba na zuwa Zainab ta saka aka kwashe kayanta tare da yi mata ihisani aka wuce da ita.

Ta na shiga É—aki kuka ta fashe da shi na tausayin Binta haka kawai ya yi mata sanadin rabuwa da aikin ta bayan ya san ita marainiyace an ya ya kyauta kuwa.

Ta na kallon shi akan mutum wanda ya fiye son kan sa bai damu ba in dai zai faranta ma kansa da masoyiyar sa bai damu don ya cutar da kowa ba.

Don haka ko wayar da yake yi da ita in ya fita duk lokacin da Zainab take nan ta ƙi daga ƙarshe kashe wayar ta yi saboda haushin sa da take ji matuƙar gaske,don ya faye son kan sa akan komai.

Zainab ba ta haƙura da neman mai aiki ba don har ta yi maganar a kawo mata wata.

Makarantar da ta fara sai hakan ya yi maata daɗi sosai ikon Allah kenan duk da ta cire rai sai gashi Allah ya saka ta na da rabon yi.Abin da iyayen gidan ta suka zaɓa mata ya sa ta ƙara yadda da cewar nufin su rayuwarta ba ta da wani amfani sai dai don ta yi musu hidima saboda girki suka zaɓa mata,ita ta na ganin wani kalar girki ne ba ta iya ba,amma kuma da ta fara karatu sai ta raina kanta don gani ta yi kamar da can ba ta iya komai ba.

Ganin hakan sai ya dage damtse burinta ta iya girki ta yadda za ta siye zuciyar A.m,da take jin kamar ana mata wahayin son shi.

Duk da cewa makarantar sau uku take fita a sati amma ta na jin daÉ—in karatun,sosai fiye da komai ba kamar da da ita kaÉ—ai take rayuwarta in dai matar gidan ta na nan.

Juwairiya ta yi ƙawa ɗaya a makaranta wacce suka shaƙu sosai duk da ba su daɗe ba,sai dai ita matar aure ce har da yaranta biyu.
Chapter 50 · 0% Book details