Sashe 25
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Kinga ni ko zamu fara Allah babu wata matsiyaciyar mace da za ta shigo min gida,na kuma riga na gaya miki in ta yi wannan kuskuren to ta tabbata ni ce ajalin ta.Kuma hankalina kwance yake ya yi min alƙawari,wace mace za ta aure shi baya haihuwa ko ni haƙuri nake."
Faɗin likita ba Allah bane Zainab in Allah ya so sai ya haihu domin ubangiji yudabbirul amri ne ya na jujjuya lamaruran sa,don haka ban ji daɗin abin da kika faɗi haka kuma kinga ya na iyakan ƙoƙarin sa.
Zainab sai ta ji wani iri a ranta ta na fatan hakan don yanzu yadda A.m yake son ya haihu har yake zubar da hawaye ta na son ko É—aya ne ta haifa mishi ita fa ba ta son tara yara.
" Ina fatan haka Allah ya amshi addu'armu sannan da kike cewa na je na rarrashe shi Allah ya sauwaƙe haka kawai kema kin faɗa min don ki tsokane ni ne ko?A kan maganar fita waje ai dama ban miki dole ba.Ni na gaji da wayar nan don takaici kike ƙara min zan shigo gidan ki kawai mu tautauna ki gashe min da yara."
Ta maza ta datse wayar ta na baƙin cikin halin da ƙawarta ta ɗaukar ma kanta saboda ta yi aure sai ta hana ci gaba a rayuwar ta?Tsaki ta yi ta ɗauki wayarta ta ta shige ɗaki zuwa can ta fito ta ci ado kamar wacce za ta gasar kyau,ta ɗauki key ɗin motarta da wayarta ta fice ta na ba za ƙamshi mai sanyaya zuciyar duk wanda ya yi katarin shaƙar shi.
A.m riƙe da waya a hannunsa a cikin haɗaɗɗen ofishin sa sai ya duba numbar A.k da nufin ya kira sai kuma ya yi cilli da wayar a kan duguwar kujerar da ke cikin ofishin.
Ya yi haka yafi sau a ƙirga gabaki ɗaya abubuwa sun rikice mishi a kampanin wanda har Daddy ya fara ƙorafi,ya sani A k wani jigo ne a cikin kampanin amma ransa ya ɓace ya je ya gaya mishi maganganu mara sa daɗi ga shi tun ba'a je ko ina ba ya fara dana sani.
" An ya Juwairaah auren ki alkhairi ne?"Ya faÉ—a da tsigar tambayar kansa saboda ganin da ya yi kan maganar auren ta kawai ya bata da aminin na sa wanda suka zama kamar Æ´an'uwa.
Miƙewa ya yi ya tsaya a windon dake ofishinsa ya na kallon waje ganin Daddy ne da ƙaninsa yake tuƙa shi,ya yi maza ya fice daga ofishin tare da shigewa cikin wani ofis wanda ya san ba za su neme shi acan ba ya kulle kansa.
" Wayyo Allah na! Ya zan yi na san Daddy ya biyo ni ne ganin na ƙi ɗaukar wayarsa ga shi kwana biyu A.k bai zo ba abubuwa duk sun caɓe.
Sai ya yi shahadar kiran wayarsa duk da ya san ba dole ba ne ya É—auka saboda ya yi fushi tunna mai tsanani da shi.
ilai kuwa wayar ba ta shiga wanda ya tabbatar mishi da ya yi blocking É—in layin ne,É—aga wayar ya yi zai yi jifa da ita sai ya fasa ganin kira ya shigo a ransa ya na addu'ar Allah ya saka shi ne,duk da ya san abu ne mai wuya ya kira shi
Ganin kiran Daddy sai hankalinsa ya tashi ya kai hannu zai kashe bai san sadda hannunsa saboda ruÉ—ewa ya danna masa amsa kira ba har kuma ya saka a amsa kuwa.
"Son lafiyar ka kuwa wai me ke faruwa ne?Rejecting É—in wayana kake yi are you alright kuwa? Ina A.k wayarsa ba ta shiga lafiya yake mai ya faru tsakanin ku mutane suna ta kirana suna complaining tun shekaranjiya na É—auka ko bai jin daÉ—i.Gashi gobe ne tafiyar ku chaina.
Daddy ya fara magana ya na jero mishi tambayoyi cikin tsananin damuwa wanda ya ƙara ta da hankalinsa to mai zai cewa Daddy shi kam ya yi nadama sosai ya san ya na da saurin fushi amma nan da nan yake sauka.
"A.k ya yi fushi sosai dama haka yake da ɗaukar abu gaskiya na shiga ruɗani kawai na haƙura da auren bani da rabon haihuwa ne don ba zan iya karya alƙawarin da na yi ma Zainab ba,ba zan iya rabuwa da ita ba don ina son ta na tabbata duk ranar da na kawo wata mace Zainab za ta yi kisa in kuma ba ta yi ba za ta kashe kanta ko ta rabu da ni,ni kuma ina sonki bazan iya rabuwa dake ba."
Sai kawai ya rintse idanunsa ya na jin wani gululun baƙin ciki ya tokare shi a maƙogaron sa ya duka ƙasa don jin shi yake zai faɗi."Hello ka na ji na a kwai abin da kake ɓoyewa son ban yarda yadda yake girmamani,zai daina zuwa aiki ba maza ka shirya muje gidan sa duk in da kake ka dawo ina jiranka ga shi nazo ofis ɗin ka baka nan."
Muryar Daddy ya katse mishi tunanin sa ya firgita lokacin da ya faɗi haka dama ya san babu wanda zai yi gigin gaya masa sun samu saɓani ne in ba so suke su rasa aikin suba.
" Um um Daddy ba ni kusa na fita a mashin zan karɓo tsako bari na dawo sai muje."
" Ok duk ma in da kake yanzu ka yi maza ka dawo."
Daddy ya ba shi umurni tare da katse wayar sa ya bi wayar da kallo ya san dai a kwai abin da ya haɗa su,amma haka kawai A.k ba zai ƙi zuwa gurin aiki ba sanin sa mai ƙwazo da kiyaye halalin sa.
Kamar an ce ɗaga labule sai ya hangi A.m ya zura da gudu ya na sanɗa ya fice daga kampanin kamar wani ɓarawo,kamar yadda mutane suka tsaya suna mamakin haka tare da tunanin lafiyarsa kuwa Daddy sai abin ya ba shi dariya ya kira Mudassir ya nuna mishi shi,dai-dai lokacin da ya fice da gudu har ya na buge kai da get.
Dariya suka ƙara kwashewa da shi." Wai me ke damun son ne ya canza kwana biyu."Daddy yace ya na kallon Mudassir shiru ya yi kawai don ba za'a ji mutuwar Sarki bakin shi ba.
Yafi kusan rabin awa in yakai hannu zai ƙwaƙwasa gidan sai ya janye ya kai ma iska naushi ya na jin tsananin nadamar abin da ya yi masa.
" A'a yallaɓai kai ne a tsaye."
Megadin gidan da ya fito da ninyar ya siyo abu a shago ya gansa tsaye.Jikinsa ya hau rawa don shi bai ji ya ƙwanƙwasa kofar ba ya san zai sha faɗa." Don Allah ka yi haƙuri wallahi ban ji ja ba kuma ba bacci nake ba."
Ganin ya gigice sai ya buɗe baki a wahalce yace." Karka damu yanzu na zo."A taƙaice ya haɗa kalmomin don baya son magana.
" To shigo zan É—an siyo a bu a shago ne."
Yace ya na waigen in da yabar motarsa amma ganin bai gan ta ba ya wuce abin sa.
A hankali yake taku zuwa cikin gidan ya na isa kofar shiga falo ya ga an buɗe ƙoda tun kafin ya ƙwanƙwasa,matar A.k ne ta na dariya." Hangoka na yi na Zey."Tace masa da masa.
" Uhumh kawai yace ya ƙara sa ciki ya zauna."Ina mijin ki na yi mishi laifi don Allah ki ba shi haƙuri tun kafin ya fito duk da na san ba dole ba ne ya fito."Yace mata cikin damuwa.
" Oh wannan tsakanin ku ne ya dai kama ta ku din ga haƙuri kun girma fa shi ma tun da lamarin ya faru yake ta huci na ba shi haƙuri amma yaƙi."
Tace sannan ta miƙe ta nufi ɗakinsa ba ta jima ba ta dawo fuskarta babu walwala na ƙin zuwa da ya yi duk irin haɗa shi da Allah da ta yi kan ya gane kuran sa.Bayan fitar ta ne A.k ya rintse idanun sa ya na jin ɗacin abin da ya faru tsakaninsu shi da Allah yake son shi ba wai don kuɗin sa ba,amma haka A.m ya rufe idanunsa ya na gaya masa baƙaƙen maganganu kuma sab ba zai goya mishi baya akan abin da yake so ba.
A.m ya canza fuska tun da ta gaya mishi bai ce da ita komai ba idanunsa a rintse ya miƙe tamkar wanda ƙwai ya fashe mawa a ciki ya fice ba tare da yace komai ba,abin da ya sa ya zo tsoro yake kar A.k ya gaya ma Daddy abin da ke faruwa kawai ya haƙura,amma tun da yaƙi fitowa bari ya ɗauko Daddy koma me zai faru ya faru.
Da ya koma hankalin Daddy ya tashi ganin yadda ya É—an faÉ—a tsakanin kwana biyu,dafa kafaÉ—arsa ya yi." Ka na cikin damuwa lafiya wai me faruwa ne?Ina A.k É—in?"
Ya jera masa tarin tambayoyi a tare ya shaƙi numfashi ya fesar sai kawai ya kwanta akan kafaɗar Daddy cikin muryar kuka ya na hawaye yace." Daddy A.k ya yi fushi da ni mun ɗan sami saɓani ne saboda wata ƴar matsala kuma na je gidan sa na ba shi haƙuri,ni na janye wannan maganar amma yaƙi saurarata har ya ije aiki.Daddy shi ne ya ɓata min rai na kasa riƙe kaina na faɗa mishi baƙaƙen maganganu, amma na yi nadama sai dai ya datse layina layika na ba ya son magana da ni."
Sai ya sa kuka kawai hankalin Daddy ya ƙara tashi yau shagwabar ta tashi kenan.
Miƙewa ya yi." Oya tashi muje gidan na sa amma ba ka kyauta ba duk da tsaƙanin harshe da haƙori ana saɓawa,nan gaba ka kiyayye ba'a ɓata ma wanda yake kusanci da kai sosai in ma hakan ta faru ƙoƙari ake a riƙe fushi don dole zaku ne mi juna."
Daddy yace ya na shafa bayan sa." Gaskiya ne Daddy na ba shi haƙuri fa kuma na yi nadama.
A lokacin da suka isa gidan da matar shi ta shiga da nufin ta gaya masa,har ya ji muryar Daddy a falo da sauri ya zo ya durkusa ya na faÉ—in." Da kan ka Daddy ai da ka sanar min ni zan zo."