← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 86

Sashe 8

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Zainab ta sauke hannunta a hankali jikinta ya yi sanyi matuƙa ganin matashin saurayin da ya kafa mata manyan idanunsa ya na kallonta,cikin zafin rai a yadda idanun sa suka nuna jira yake ta mare shi ƙila ball zai yi da ita yadda ya haɗe fuska.
Ta shiga in ina ta na ƙoƙarin matsawa daga gurin ya tureta ya na faɗin."Matsalar ƴan matan bahaushe kenan daga sunga sun fita waje su dinga nuna isa.Da kin mare ni wallahi sai na yanke duk yatsun ki na kai ma karan gidan mu nan gaba sai na ga da wane hannun zaki yi mari."Ya ja tsaki tare da zama ya maƙala earpis a kunninsa tare da harɗe hannun sa duka a ƙirji,zuwa can ya cire earpis ɗin ya lumshe idanunsa.

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na huɗu dan har yanzu shinfiɗa ne har ba'a fara ba.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA HUÆŠU*

Jiki a sanyaye ta koma kujera ta zauna ta na jin wani shauki ya na ratsa bargon jikinta,hannu ta sa ta share zufan goshin ta tare da jingina kan ta da bayan kujera ta na kallon sa cikin wani irin yanayi.Ganin halin da ta shiga Imsal ya matso dai-dai kunninta tace."Gaskiya gayen ya na da kyau sosai."
Zainab ta ƙara lumshe idanunta ta na kallon shi ba tare da tace mata komai ba,amma ta na jin wani girmar lamari a tare da shi,zuciyar ta ta na bugawa da sauri-sauri haka bugun ƙirjinta.
A lokacin da jirgin ya fara tafiya Zainab ji take kamar ta je gurin sa ta yi mishi magana,ji take komai na ta ya sukurkuce,amma ganin yadda ya É—aure fuska idanunsa na rufe ya sa taji karayar zuciya.
Wayarta ta ciro ba tare da ya sani ba ta dinga ɗaukar sa hoto,ta na turawa ma ƙawayen ta da ta yi saurayi.Ko da suka iso Nigeria bai kalli in da take ba,ya na janye da troley ɗin sa hankalin sa na kan A.k da yazo ɗaukar sa.
Da sauri ta ƙarasa gurin sa tare da shan gabansa saura kaɗan ta faɗi,amma ba ta kula ba ta tsaya ta na mishi murmushi mai ɗaukar hankali.
A.m ya juya bayan sa ya na kallo a tunanin sa wani take ma murmushi a bayan sa,don shi sam ba yarinyar ba ta yi mishi ba,saboda tsiwarta sannan shi a wannan lokacin babu so a tsarinsa,bai shirya aure ba duk da burin iyayen sa kenan.
Kallo ya bita da shi tun daga saman ta har ƙasa ta na da kyau shi ma ya san haka,amma hakan bai wani dame shi ba kasancewar ya sha haɗuwa da mata kala-kala.
Wani ƙarin murmushi ta ƙara saka mishi tare da bin sa da sauri ganin ya fara tafiya."Don Allah ka tsaya ina son magana da kai,in ba damuwa ina son mu ƙulla abota."Ta faɗa tare da miƙa masa hannunta .
Wani ban zan kallo ya yi mata mai kama da ya ga kashi yaci gaba da tafiyar sa ba tare da yace mata uffan ba.Jikinta ya yi sanyi ta na tsaye ta na kallon shi har ya shige cikin motarsa,wanda A.k ya tuƙo don ya ɗauke sa.Da idanunta da suka canza kamar za ta zubda ƙwalla ta kalli bayan motar.
TURAKI FAMILY
Abin da taga an rubuta keman a bayan motar wani irin farin ciki ta ji ganin A.m ko ɗan waye,sai murna ya kama ta sosai tasha jin mahaifin ta na waya da wani daga cikin family ɗin.Ba ta son wulakanci sannan ta sha wulaƙanta maneman ta,amma wannan karan ta na ji ranta sa samu kalan mijin da take so.
Ko da ta isa gida tunanin wannan kyakykyawan saurayin ya tsaya mata a zuci,da ta rufe idanunta kyakykyawar fuskarsa take hangowa.Tun kafin Abban ta ya dawo ta kira tare da bashi labarin saurayin da ta haÉ—u da shi,kuma ya tafi da imanin ta.
Dariya ya yi sosai kin yadda ta ruɗe akan shi ta na mishi shagwaba da ƙyar ya samu ya lallasheta,ta kashe wayar ta bayan ya yi mata alƙawarin gane ko waye daga cikin family Turaki saboda ya san Alhaji Sama'ila abokin cinikayyar sa ne.
Ko da ya dawo gida haka ta sa shi a gaba ta na ta yi mi shi magiya,har ya gaji da ƙorafin ta ya kira Alhaji Sama'ila.
Bayan ya gaya mi shi dalilin kiran sa dariya sosai tare da farin ciki ya yi,a ransa ya na roƙon Allah ya sa A.m ya so Zainab ko ba komai ya yi dacen mace,sannan zumuncin kasueancin su zai ƙara ƙarfi.
Duk yadda Abba ya yi da ita kan ta haƙura da numbar A.m da ta kafe sai an turo mata,amma taki daga ƙarshe kan dole ya ƙara kiran Alhaji Sama'ila ya turo mi mi shi da numbar.
Da gudu ta ruga cikin ɗakin ta da wayar ta a hannunta bayan ta kwashe numbar a wayarta.Kan gadon ta ta faɗa ta na ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske ,tare da ƙanƙame filo a ƙirjinta.
Ran ta ya fara ɓaci ganin ta yi kira ya kai sau biyar ba'a ɗaga wayar ba,da ga ƙarshe sai ta ji an kashe wayar jifa ta yi da wayar ta ta zauna akan gadon ranta a jagule.
Ko da Alhaji Sama'ila ya tare shi da zancen yarinyar da suka haÉ—u a jirgi,nuna ya yi bai gane ba in ma ya haÉ—u da ita ya manta.Ganin kauce-kaucen da yake mi shi sai ya yi masa umurni da yaje ya ganta ya na son ya nemi aurem ta.
Babu yadda A.m zai yi ba tare da ya so ba ya amince duk da a wannan lokacin ya fara tunanin lokaci ya yi, da zai yi aure ya huta da damun da iyayen sa suke mi shi a kan ya yi aure sannan ya na buƙaƙar ya ga yaransa ga ƙaninsa ya na da biyu.
Da wannan tunanin A.m ya amince ya je gidan su Zainab tamkar za ta yi hauka haka take ji a ranta,da ta gan shi ruÉ—ewa don Allah ya saka mata son shi a birnin zuciyar ta.
Tun ya na share ta har ya bada kai bori ya hau.Zainab ba ta a cikin matan da namiji zai wulaƙanta ita kanta ta na alfahari da hakan.Haka suke shan soyayyar su kullum suna maƙale da waya ana ga ya ma juna kalamai so.
A hankali A.m ya fara jin tsanar wasu daga cikin halayan Zainab,musamman yanayin shigar ta da tsabon son jikinta,sannan shi namiji ne mai son mace wacce ta iya girki amma tunkafin su yi aure ta gaya mi shi ita ko ƙafar kicin ba ta shiga.
Dariya ya yi kawai don ya yi tunanin tsokanar shi take yi ganin ta wayayya mai aji,ya san babu yadda za'a ta bari Æ´ar aiki na yi mi shi girki,ko a gidan su Amminsa take mi shi abinci.
Haka dai aka dinga cin soyayya har Allah ya kai si ga aure.Bayan an gama shagali amarya ta tare a É—akin mijinta.Shi kaÉ—ai ya shigo bai nemi rakiyar kowa ba,ko A.k daga kofar gida ya tafi ya na ta mishi dariya.
Da gudu ta taso ta rungumshi ya janye ta jikinsa,kasancewa wannan ne karon farko da mace ta rungume shi,idanunsa ya kafa mata duk rashin kunyar ta sai ta ji ta kasa haÉ—a ido da shi ta sunkuyar da kanta.
Bayan sun yi sallah sun ci kayan daɗi da ya siyo musu,suka tsunduma kogin soyayya.Wani irin tarairayan juna suke yi ma junansu A.m bai san ya kamu da soyayar Zainab ba sai da ya aure ta yake jinta a zuciyar sa.Koda yaushe suna maƙale da juna in ba shi a gida suna kan waya.Ya na matuƙar ji da ita ba ya son ɓacin ranta.
Abu ɗaya da ya fara kawo musu cikas yadda Zainab take son jiki komai suka yi amfani da shi,a nan za ta barshi sai in shi ya ɗauke da fari abin bai dame shi ba,amma daga bisani sai ya ji ya na taɓa zuciyar sa.
Kusan shi yake ɗan wasu aikace-aikace na gidan.Sati biyu da auren su mahaifiyarta ta kawo mata masu aiki mata guda biyu.Da fari A.m yaƙi amincewa amma daga kan dole ya haƙura,saboda yadda shaƙar numfashin gidan yake son ya fi ƙarfin sa.Hankalinta kwance ta ci tasha ta tafi gurin aiki.Hakan bai wani dame shi ba saboda ya na matuƙar sonta.
Kamar yadda Zainab ta tsara ba tare da ya tsani ba take shan maganin ha na ɗaukar ciki a ɓoye,ba ta damu da mai zai faru ba duk da ta san illar sa musamman da take likita,amma yadda A.m yake yaba halintar ta ya sa take shan maganin don ba ta son canjin jikinta.Kuma mafiyawancin family ɗin su suna da ƙiba.
Tsaye yake a gaban madubi ransa a jagule ya na kallon kansa a madubi,zuciyar sa babu daɗi.Matuƙar yunwa yake damun shi amma ba ya son cin abincin masu aiki,saboda daɗin shi bai kai na amminsa ba ya na jin kunyar zuwa ƙarɓo musu abinci,wanda ita Ammin da kanta tace ya kama ta su fara girki saboda ta gama kawo musu na amarci,in bai manta ba rabonsa da abinci tun daren jiya da ya ci a gidan A.k.
Ya ɗauki kum cikin ɓacin rai ya na tunanin bayan ya na matuƙar kiahin Zainab,sannan ita ba ta da kiahin kanta don ko masu aikinta mata yadda take fito musu kamar tsirara ya na bashi haushi amma ita ko a jikinta.Da namiji zai ɗauko kuku ya dinga mishi girki.
A hankali ya ji an turo ƙofa an shigo wani ɗan murmushi dole ya yi mata ya na jiran ta ƙaraso,amma sai ya ji an yi shuru kamar ba'a shigo ba idanunsa ya ɗaga da nufin ya kalleta yau yangar ce ta motsa.
Sai ya ga mai aikin su wacce bai ma san sunan ta ba tsaye ta na kallon ƙirjinsa ta na lashe baki,idanunsa ya kai kan jikinsa tare da jin kunya don daga shi sai ɗan tawul iya gwiwarsa."Ke!Uban me kike kallo ƙazama kawai?"Yace da ita ran shi a ɓace ganin yadda take kallonsa kamar wata mayya.
Da sauri ta matsa cikin tsoro muryar ta na rawa tace."Madam ce ta bani umurnin na shigo na share É—akin."Ta ba shi amsa tana jin wani lamari dangane da shi.
"Tunna kin ga da mutum ba sai ki fita ba,banza mayya kawai."Yace da ita bayan ya ƙara daka mata wani tsawan,da sauri ta fice har ta na buge kanta da ƙofa.
Ya zama dole na ɗauki mataki ba zan lamun ce da waɗannan ƙazaman arna suna shigo mim ɗaki ba,gajerun wandunan sa ya kwashe ya saka a sif ɗin sa ya na takaici don ya san masu aiki suka wanke.
Chapter 8 · 0% Book details