← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 86

Sashe 11

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk maganganun da take yi ba ta ce mata komai ba,aranta ta na tunanin karta amince a za a sami matsala da Baba Sani duk da shi ma ya na da laifi,in da ace ya na taimaka musu da ba za ta yi aiki ba.
'Ki na ji Mama da ban so na gaya miki wani sirrina ba,amma nuna amincewar ki ya zama dole na sanar miki domin ki taimakeni ki ceci aurena.Mai aikina mijina ya kama ta da yarana tana basu kirjinta suna tsotsa ita kuma ta na saka musu hannu a gabansu.Hankalinsa ya tashi ƙwarai ba yan ya miƙa ta ga hukuma ya kawo su asibitin da nake aiki,hankalina ya tashi ƙwarai na yi kuka kuma mun yi rikici da shi daga ba ya yace dole na bar aiki ko mu rabu.Ina son aikina saboda da shi nake taimaka iyayena,sannan ina son aurena na yi-na yi a dai na saka ni aikin kwana amma ba zai yiwu ba.

Mijina ya bani zaɓin na bar aiki na kula mishi da yaransa ko ya rabu da ni,domin yaƙi barin na ƙara ɗaukar me aiki.Mun yi rikici da shi sosai daga baya ya haƙura na samu mai aiki amma daga wannan ya kama ta da wani matsala zai rabu da ni."Tace cikin hawaye ta ja numfashi sannan ta ɗora da cewa.

"Mariya ita ta ja ra'ayina akan Juwairiya saboda ta gaya min ta na da hankali,da ƙyar na amince da na ganta na yadda da maganar Mariya ki taimake ni Mama in har kika amince zan zama tamkar ƴarki,zan taimaka ma rayuwar ku."

Jikin Mama ya yi sanyi sosai har ba ta san sanda ta amince ba jin aure na shirin mutuwa,duk da watarana ita ma aure za ta yi."Na amince Allah ya kyuata amma ƴar nan ya kamata ku din ga kiyaye wa,ni ma matsalar ba daga gareni ba ne a kwai ƙanin mahaifinta ba lai-lai ba ne ya amince amma ta fara mu gani."

Sosai ta ji daɗi ta buɗe jakarta ta ciro dubu ishirin da biyar tace."Ga kuɗin ta na wata biyu dubu ishirin sai ki fara koda sana'a ne,sannan dubu biyar na baki kyauta kuma gobe in Allah ya sa tazo za ta taho da tsaƙo."

Mama ta ji daɗin kuɗin da ta bata ta na ta murna da saka mata albarka har ta yi mata sallama,ta kama hannun Juwairiya tace."Sis sai kin zo gobe ko?Don Allah ki zo da wuri ƙanninki suna ta maganarki."Tace tare da shafa kanta.
"Gaskiya ta na da kirki sosai."Mama tace ta na juya kuɗin da ta bata,sai kuma ta aje kuɗin ta kalleta tace "Kin san me ba zan taɓa kuɗin nan ba sai mun ji me Baban ku Sani zai ce."Da sauri ta miƙe kawai ta na faɗin."Ki ba ni naje na yo miki sare-sare ki fara sana'a ni fa ko me zai yi sana yi aikin nan,tunna shi ba taimakon mu yake yi ba don haka ba shi hurumin da zai hana mu."

Ta yi maza ta fice daga É—akin kafin Mama tace komai sam ba ta jin tsoron abin da zai ce in dai ba kasheta zai yi ba ta rantse sai ta yi aikin.

Kamar yadda ta gaya mata mijinta ba mazauni bane haka kuwa ta gani,don tun da ta fara aiki ba ta gan shi ba sai tanƙamemen hoton su da yake manne a falon wanda tun da taje ranar da Mariya ta kaita ta gan shi a hoto,wannan dalilin ya sa hankalin ta ya kwanta ko da ta ga Baba me aiki aikin ta take yi ta tafi ba ta kwana.

Ta na aikin ta cikin kwanciyar hankali ga abinci da take ci kullum taci mai kyau ta sha mai kyau,don Anty Naja ba ta da rowa ko nama taci sai ta rage mata saboda yadda Juwairiya take kula da yaranta ga ta da tsafta ko ina na gidanta tsaf ya na tashin ƙamshi.

Kusan sati biyu ta na aiki cikin jin daÉ—i kuma har zuwa wannan lokacin Baba Sani be dawo ba,kullum in dai za ta dawo Anty Naja na sawa a yi girki da su ta saka mata a kula kuma da yawa,don haka ba sa matsalar abinci ga É—anye da take badawa a kai ma Mama in dai za ta yi aikin kwana.

Ranar Juma'a da safe bayan ta gama aikin ta ta shirya musu abincin karyawa ta ibi nasu kamar yadda ta yi mata umurni,kasancewar ta gama aikin kwana za ta yi hutu har ta bawa Juwairiya hutun kwana biyu.

A hanya Juwariya ta na tafe ta na ta yi mata addu'a don tsakanin su Allah ne kawai zai biya ta,saboda irin kyautata mata da take yi fara aikin ta ta bata kaya masu kyau sosai da abin alheri ko hijabi kala biyar ta bata,sannan ko baƙi ta yi bata ce mata me aiki sai dai tace ƴar'uwanta ta na da matuƙar kirki sam bata nuna wani abu ko rashin mutunci.

A dai-dai ƙofar gidan su ta tsaya cikin firgici ganin Baba Sani ya ɗare kan motar sa ya na riƙe da ƙatuwar bulala,sai juya ta yake ya na zare ido ransa a ɓace da ga ganin yadda ya ɗaure fuska alamun ba mutunci.

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na bakwai.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE)

Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA BAKWAI*

Tsananin mamaki ya kama shi ganin yadda Juwairiya ta gan shi amma sai ta yi tsaye ta na kallon shi, ba tare da nuna wani tashin hankali a fuskar ta ba ko tsoro.

Ya ɗan ƙare mata kallo cikin mugun nufin sa amma sai ya ga duk da ramar da ta yi,ta ƙara mishi kyau ɗan tafiyar da ya yi.

Juwairiya da tsaya ko zai ce wani abu amma ganin ya yi shiru,ya sa ta nufi hanyar shiga ƙofar gida za ta shige.Da dauri ya sha gaban ta a ransa ya na mamakin dai na tsoron shi da ta yi,tun ranar da ya nemi haɗa jiki da ita.
"Da ga gidan uban wa kike?"
Ya tambayeta da fuskar shanu y na zare mata idanunsa da suka kaÉ—a suka yi ja,saboda tsabar fitina da ya saka ma kansa.Ta É—an ja ta tsaya tare da matsawa nesa da shi ganin yadda ya matso daf da ita.

"Ba na hanaki yawon maula ba,shi ne don kin ga ba na nan kika mai da shi sana'ar ki?"Ya tambayeta tamkar zai kai mata bugu.

"Ni ba maula naje yi ba,aikatau na samu nake yi domin na ciyar da kammu."Ta faÉ—a mishi ba tare da jin tsoro ko shakku a ranta ba.

Wani irin azababben mari ya wanka mata wanda ya sa ta yi taga-taga za ta faÉ—i,amma ta dake duk da azabar da ta ji kamar za tai fitsari a tsaye sai ba ta nuna mishi ba,don a shirye take ta shirya tsaf!Ko kasheta zai yi.

Matuƙar mamaki ya kama shi wai yaushe ya yi sake har ta raina shi haka,amma sai ya ƙara ɗaure fuska yace."Na ga kwana biyu kin raina ni Juwairiya saboda na nuna miki manufa ta a kanki,to wallahi har yanzu ina kan baka na saina cika muradina gara ma ki amince ki sami maslaha a rayuwarki."
A wannan lokacin ta ji wasu tagwayen hawaye sun cika mata fuska,zuciyarta ta amince da lai-lai shi ba mutum bane don ta yi tunanin rasuwar mahaifinta zai saka ya haƙura da ƙudirin sa.

"Ka sani ko mutuwa zan yi ba zan lamunce ka biya buƙatar ka a kaina ba!Ina matuƙar kaico a rayuwata da ka fito a matsayin ƙanin mahaifina.Ko mutuwa zan yi sai dai na mutu."Tace mishi ta na ƙoƙarin shigewa gida.

Sororo ya yi lai-lai ya yi sake tunna har taga wallar shi ta na faÉ—a mishi mugayen kalamai,masu tsauri a cikin idanunsa ba tare da shakku ko shakkar sa ba.

"Tun da kika ce haka mu zuba ni dake,bari na tuna miki akan ki zan iya komai tun da kika girma na É—ora kwaÉ—ayina akanki Ki kuka da kanki zan iya komai don na cimma manufata."

Ta buɗe baki za ta yi magana wani irin takaici ya toƙare mata maƙogaro,sai hawaye da suka fara turereniya a fuskarta da ta tuna ƙanin mahaifinta yake mata wannnan halin,sai ta ruga a guje ta shige cikin gida ta na kuka.

Mama dake ƙoƙarin hura wuta a murhun gawayi idanunta duk sun yi ja, suna zubar hawaye saboda wutar taƙi kamawa sai saka leda take yi.Sai ganin ta ta yi ta shigo da kuka ta shige cikin ɗaki ta buɗe baki da nufin ta yi magana,duk da cewa ta san dalilin kukan saboda ta ji dirin motar sa sanda ya dawo sai kuma ga shi ya shigo.

"Saboda ba na nan shi yasa kika saka ta ta na yawon maula ta samo muku abinci ko?Na rasa wani hali kike so ki koya mata shi yasa na tsaneki saboda mugun halinki."
Ta yi shiru ba tace komai ba dama É—abi'ar ta kenan duk sanda zai yi mata rashin mutunci ba za ta tanka ba,haka ma yanzu mutuwar Yayan sa bai saka ta canza ba.
Har ya gama bambamin sa ya fice bata ce ƙala ba,amma ta na jin gara su haƙura kawai da tashin hankalin da zai jawo musu.Bayan ta gama kukan ta ta share kamar kullum don Mama ba za ta taɓa lallashinta ba.

"Juwairiya ina ganin a haƙura da aikin nan kawai."Tace cikin ƙunar zuciya ta na kallon ta."Gaskiya Mama sai dai kiyi haƙuri,amma ba zan haƙura tunna shi ba taimaka ma na yake ba."
Chapter 11 · 0% Book details